7 & 8

2.6K 62 4
                                    

_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_



             _IN BETWEEN THE LOVE_
            ❤ _Lies another love_❤


            _✍🏿M Shakur_

                        7️⃣ & 8️⃣

_how to pay your subscription fee_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*you can also send MTN card ta WhatsApp number na 07012181461 in baki da banki, sainai adding naki a group din danake posting*_



_Free Page_

Dan kallon ko ina yayi a anguwan ganin ba mutane yasa yaji dadi lemme just kill two birds with one stone, taku daya yayi ya fizgo hijabin Aneesa hakan yasa Rauda tai mugun faduwa sabida kayansu data kulle atare, bugawa kirjin Aneesa yashiga yi hakan yasa ta shiga kiran sunayen Allah a ranta, cikin karfin hali ta take kafarshi cikeda tsiwa tace "kasakeni" girgiza mata kai yayi yana kallon kwayan idanunta yace "saikinyi daga daga dani as you said Hajiya, thank God babu kowa a layin amfanin unguwan masu kudi kenan, oya fara" ya mika mata jikinshi jiran tadake shi, ganin hankalinshi baya kanta yasa Rauda data zube akasa ta mika hannu ahankali taja wayar Aneesa touch light phone dayadan zamo daga jakanta dake kwance akasan wajen, hannu tamika taja wayan tsabagen yanda tarude batasan lokacin data shiga saka number Ya Aliyu na Nigeria ba tana addu'a Allah yasa yasaka layin tai dialing, kaman ance yadaga kai yaga Rauda rikeda waya, ganin waya a hanunta yasa Khamis yawani irin ture Aneesa da karfi hartana buge gate yay kan Raudan cikeda bacin rai, fizgo bayan riganshi Aneesa tayi tace "kin kira, yi sauri an dauka?" komawa baya Rauda tayi tana sake dailing number Ya Aliyu daya gama ringing bai dauka ba tana kuka sosai tana kallon Khamis dake kokarin fizge riganshi daga rikon da Aneesa tamai....


Uban gudu yake shararawa kan titi ya kunna waka dake tashi kadan kadan, shi kadai a motar da kamshin ciki yahadu da kamshin jikinshi sai abin ya gauraye yabada wani d'adadden kamshi mai melting zuciya, sai murmushi yake rabonshi daya fita alone, sanan rabonshi daya rike starring mota yay tukoi harya manta wlh, yauma bakaramin rigima sukai da Dad ba kafin ya yarda yafito shi kadaiba dan saidama yace yafasa zuwa gidan Momma, ganin bakuwar number yasake kiranshi yasa yay dan tsaki tareda yatsine fuska yadau wayar yakara kunne batare dayace komiba. "Y...Ya Aliyu I...is me, me, me ne, Rauda, ka...g..kaga Ya Kham...Khamis is trying to ra...p..pe me" yanda Rauda tai maganan tana kuka sosai muryanta na breaking baima gane kan zancenta ba sai kalmar karshen rape dayaji yasa yaji kirjinshi yabuga sosai, gangarawa gefen titi yayi yaci brake cikin tsawa yakira sunanta. "Rauda, calm down, tell me who is Khamis and where are you? Keda waye ne, where are you?" arude ta kalli layin tace "Suleja bansan inane anguwan ba" da sauri Aneesa data rike bayan rigan Khamis da duka karfin ta ta bude murya tace "layin yan gayu a Suleja" baki Rauda tabude zatai magana danta fadamai sunan layin yasa kafa cikeda fushi ya bugi hanunta da kunenta data kara wayan hakan yasa wayar tai tsalle tawani irin tarwatse a gefe, yanda takalmin shi yadaki gefen kunenta saida idanun ta suka juya tai baya kaman wacce ke shirin sumewa kunenta yay wani irin dummmm bamataji jinta yadauke duka. "dan uwarki sabida tuntuni banso na dakeki angayamiki kin gagareni ne" arude Aneesa data rike bayan riganshi ta sakeshi ta rarrafo da sauri tana kallonta tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, kai mugu ne wlh Allah ya saka mata, kunenta" tamika hannu zata taro Raudan datai baya zata zube akasa, wani irin fizgo Aneesan yay da hannu daya zatai magana yasa hannu ya dauketa da lafiyayyen mari mai kyau yace "you had your chance kitafi amma kika tsaya" bude Gate din gidan yayi ya wani irin tura Aneesan ciki da duka karfinshi tafadi akasa da sauri ta mike zata fito ya finciko Rauda datai kasa ya shigo da ita hakan yasa Aneesa tace "kabarmu mutafi Malam ga gidan nan babu kowa ciki, dama nafada tun dazu karya kake, kallo daya za'amaka agane kai irin yan iskan mazan nanne masu lalata yaran al'umma,














ATSAKANIN SOYAYYA (In Between the Love) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant