*TARKON ƘAUNA,*
*DAƊIN KOWA,*
*KWANA CHASA'IN,*
*JAMAI RAJA,*
*SAPNE SUHANE,*
*GIDAN BADAMASI,*
*RUƊIN ZUCIYA,*
*BAGHYA LAKSHMI,*
*AKUSHI DA RUFI,*
*AUDIO NOVEL,*
*HAUSA NOVELS.*

Kada kimanta da ranan zaɓe in kin shiga group ɗin ki zaɓi *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* tananne za ku iya nuna mana irin son da kukema ƙungiyarmu da littattafanmu.

Karku manta fa masoyanmu idan kun zaɓi labarinmu za kuyi comments ne, wannan shi ne zai nuna mana cikakkiyar ƙaunar da kuke mana, *Mun gode, Mun gode.*

Allah yabar Ƙauna da zumunci.

*DEDICATED TO: DAN ISKAN NAMIJI REALLY FANS*


*10-15*

Maryam! "Mommy na asibiti rai a hannun Allah, Daddy kuma ya yanke jiki ya fadi," ya kara rungumeta ya fashe da kuka.

Tsananin tausayin sa ya ƙara kamata, bata san sanda ta rugume shi ba, tana share masa hawayensa.

"Kayi sauri mu wuce kawai" tashi yayi da sauri jikinsa ba kwari haka ya miƙe yana share ƙwallar idonsa ya nufi ɗakinsa, gas ɗin ta kashe kawai tasa abaya har ya fito suka wuce asibitin.

Mama ta kira cikin kuka, take sheda mata cewa Mommy da Daddy suna asibiti ba lafiya, sun wuce can kawai, su kansu hankalinsu ya ƙara tashi sosai, a lokacin Abba da Umma sunzo.

Abba ne ya kira Arfan ya tambaye shi asibitin da suke, ya sanar masa yace gasu nan zuwa shi da Umma, ya kashe hankalin Mama da Nafeesat ya tashi, musamman Nafeesat tana mugun son iyayen mijin nata.

Suna zuwa suka tarar Mommy tama farka, dan tana zaune tana ta rusgar kuka, suna shiga suka tarar da ita a zaune tana ta kuka kamar ranta ze fita.

Da hanzari suka ƙarasa kusa da ita, Arfan ya rungumeta yana rarrashinta, "Mommy wai lafiya meya faru? kun gama samu a duhu naɗauka wani mummunan lamari ne ya faru daku."

ɗago kan da za tai taga Maryam a gefe tana hawaye, wani kukan kura tai ta kamo Maryam tana jibgarta kamar jaka, tana ihu "gwara na kashe ki da naga wannan baƙin cikin da kike shirin ƙunsa mun."

Arfan ne yai kanta ya fisgeta, "gwara ki kashe ni da ki taɓa mun Maryam! itace rayuwata Mommy, me tai miki ?idan na rasata tabbas kun rasani."

Ihu Mommy ta kwarara, "wallahi kinyi ƙaɗan annamimiya ki haɗa ɗa da uba sanki, wallahi ba wanda zaki samu a cikinsu muguwa munafuka."

Banda kuka ba abunda Maryam keyi, saboda batasan me taiwa Mommy ba take mata wannan dukan, gashi taji tana wasu mugayen furuci masu barazanar tarwatsa mata kwanya.

"Mommm.....myyyy ban.. gane...me kike faɗa ba" ƙinƙinar dole ce ta kama Arfan, saboda ji yake kamar saukar aradu saukar maganar a kunnensa, ganin ya sake ta ta ƙara rufe Maryam da duka.

"Wallahi sai kin rasa rayuwarki, mijin yarki da babansa kika yaudara kika sasu a tarkon ki, to wallahi barin irinku a duniya masifa ce, gwara ace babu ke inyaso nima a kashe ni azzaluma."

Ya isa haka Mom! ko meye tsakaninki da Daddy be damen ba, saboda haka ki rabu da Maryam, kar nai abunda zaki fushi dani akan Maryam, bana gane kaina a kanta, ita ɗin rayuwata ce, ita kaɗai nakeso a duniya."

Kuka Mommy ta fashe da shi, "lallai Arfan akan mace kake gayan haka? macen da ta haramta a gareka, kasan cewa yayar ta kake aure amma kake gayan haka? to ka kyauta, amma inaso kasani babanka ma ita yake so shi ne sanadiyyar zuwan mu nan.

Ihu Maryam ta kurma ta zube a wajen, yayin da Arfan ya faɗi jagwab, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, "Mommy what!" ya faɗa da ƙarfi.

"Tabbas wannan babbar masiface da ta shigo rayuwar mu Mommy, amma Maryam bata da lefi, mune muka shiga rayuwarta, nine mutuɓ na farko da Maryam ta fara so, na tabbata bazato Daddy ba ni zata so, saboda haka karki nunawa Daddy nasan maganar zan."

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now