Yau ta kama juma'at yau za'a daura auren Lawan da doctor Saudat auren da ba wanda ya sani ko matansa basu sani ba

An daura auren Lawan da saudat auren sirri sukai ba wanda yasan da wannan auren saboda saudat tace bata bukatar zama gidansa hakan ba karamin dadi yai masa ba

Momy kawar Saudat ce tazo tayata murna saboda ita kadai ta yarda tasan tayi aure sai kawarta data rakata gun malamin data kai ta ita ki bama ta kasar gaba daya

Yanzu Saudat kina ganin auren da kikai na sirri ze kai ki tudun muntsira kuwa wace irin rayuwace wannan kika daukarwa kanki

Dakata Momy bansan shishshigi saboda naga baki da surutu kinada amana na bari kika san maganar aurena

Aurena nayi shi ne da zuciya biyu na farko inasan nadau fansar wani cin mutunci da Lawan yai mun a asibiti na biyu kuma inasansa

Saboda haka dole Lawan  yabi abunda nakeso saboda dorewar auren mu dashi wallahi sai na gasawa Lawan gyada a hannunsa badai shi Dan iskan namiji ba zan nuna masa shu'uman cin mu na yaya mata

Hmmm baki da wayo wannan ba hanyar daukar fansa bace kibar mutum kawai da halinsa musamman Lawan din nan da kinfi kowa sanin ainihin iskancin sa

Mtsww mubar wannan maganar kinsan har dinki nai masa yau ze fara zuwa yanzu ma me kunshi zata zo da kitso tai min kinsan amarya nake ayau

Bakin ciki kamar ze kashe Momy saboda haushin yadda Saudat tai auren sirri tana ganin abun ze bata matsala a gaba amma ita sam bata tunanin hakan


     **************

Buduri ake a gidan Alhaji Ghali na tashin hankali idan kaga yadda maza ke turuwar abun ze baka mamaki musamman yadda ya kasance manyan mutane ne wayanda ake mugun ganin girmansu a garin nan

Nauwara ce ta fito daga bandaki taga mutum a cikin dakinta fuskarsa a rufe ba abunda kake iya gani sai idonsa hannunsa wata sharbebiyar wuka ce

Ihu ta saka ta razana ta juya da gudu zata koma yasa kafa ya hardota jikake dam ta fadi a kan tiles ba karamar faduwa tai ba dan hakoran ta guda biyu sai da suka fita

Jini ya fara ambaliya ta hancin ta ta baki habu na labe sakon wadrobe ya rasa abunda ze dauka ya temaka mata dashi daga gefe ya hango butar jona ruwa dai dai kafarsa

A hankali yadauka shiko ya bita kasan ya haye kanta ya shaketa yana neman hallakata ya daga wukar ze daba mata habu yai kukan kura ya doka masa kettle a kansa

Tuni ya fadi warwas a kasa nan da nan jini ya fara ambaliya ta kunnensa amma saboda karfin hali ya daga wukar da niyyar sokawa Nauwara  habu ya kara buga masa kettle akansa shike nan ya mutu a wajen

Nauwara tayi plat a kasa hakora biyu a waje kuka take me sauti tana nadamar auren me kudi datai da talaka ne da tuni tana rayuwarta hankali kwance

Hankalin Habu yai masifar tashi ganin yadda wannan me mask din baya numfashi yana daga mask din abun ya firgita shi saboda babban yaron Baby Chakwai ne yana mugun ji dashi

Duk wani ta'addanci shi yake sawa ha aikata kuma tabbas kashe shin da yai ba karamin barazana bane ga rayuwarsa

Zama yai dabas zaman Yan bori shima ya fashe da kuka saboda tsananin tausayawa rayuwarsa da yake yasan yanzu shi dai sai ta Allah ba abunda ze hana baby Chakwai besa an kashe shi b akan wannan tantirin

Shi kuka Nauwara a hankali ta mike zaune bakin ta na zubar da jini ta kalleshi waye kai meyasa ka temake ni daka bari ya kashe ni na huta

Tayaya zan bari ya kashe ki Nauwara bayan Allah ya jarabceni da kaunar ki tun kallon farko danai miku naji ina masifar kaunar ki ya matso kusa da ita

Yanzu yazami da gawarsa Nauwara meye shawarar ki akan gawar nan kigaya min dan Allah

Ajiyar zuciya ta sauke banda wata shawara banda ita taunani na ya tsaya ta fashe da kuka

Baby Chakwai shagali kawai ake sha burinsa ya cika ze rayu shi kadai da Alhaji Ghali dama burinsu duniya tasan yayi aure tunda har an sheda yayi auren komai ya kare meye amfanin zaman yarinyar a gidan

Yasha giyarsa yayi tatul ya kalli Alhaji Ghali ya sheke da dariya my sweetheart kaje ka fito da waccen jakar ta gyara ragowar dakunan munada bakin kwana tunda munada wadatar waje base sunje ko ina ba

Jikinsa na rawa ya mike ya shiga gidan Dan cika umarnin Babyn sa saboda bayasan abunda ze bata ran baby Chakwai musamman yadda suke kara samun kyautuka daga kasashen duniya na kungiyarsu

Dole ya rike baby Chakwai yarinya Yar yayi wadda kowa keso shi yayi dace duk da ya fara tausayawa kwadayayyiyar yarinyar data nane masa

Alhaji Ghali ne ya shiga babban parlour din a hankali ya karasa bakin dakin nata saboda jin tashin kuka da magana kasa kasa

Ya kasa kunne yaji Habu na fadin yazama dole na kashe idan ban kashe shi ba tabbas keze kashe kiyi hakuri mu nemo mafita kawai

Kofar ya shiga bugawa iya karfinsa fitsari ne ya subucewa Nauwara jikin ta yanata rawa kamar mazari

Ki bude duk abunda kuke fada naji ku bude kashe ni kike son yi ko to wallahi ta Allah ba taki ba kaf danginku dan ubanki yau zaki san nizaki kashe

Tayaya wani ya shigo mun gida wallahi sai na kashe ku dukanku gaba daya Nauwara ta gama firgita ta fice hayyacinta

Ganin haka Habu yai shahada ya mike ya bude kofar shidewa tai ganin ze bude ga gawa yashe a kasa yana zuwa ya murza key daya biyu

Gam kake ji Alhaji ya turo kofar ya damki wuyan Habu shaka bata wasa ba abunda ya gani ne ya sashi sakin Habu ya fadi yaraf shima ya zube wajen



*Kuyi manage da wannan wallahi banida lafiya ne sosai gaskiya bakwa comment rashin comment dinku shine ze hana ni yin dogon typing*

DAN ISKAN NAMIJIWhere stories live. Discover now