LIKITAN ZUCIYA

395 17 0
                                    

LIKITAN ZUCIYA....

1

Me yake damuna?
Anya kuwa inada imani irin wanda mutanen kwarai suke dashi?

Wayannan sune tambayoyin da suke kai kawo a cikin zuciyata. A wasu lokutan idan na roki Allah ina jin nauyi, domin ina tsananin neman tallafinsa, alhalin ni kuma bana sadar da abubuwan daya umarceni da in sadar, hakanan bana nesantar da dama daga cikin abubuwan da yace in nesanta........... Kunyar da nake ji tana karuwa idan Allah ya biya min bukatuna, duk da cewar ni bana aikata abubuwa da dama da yake so kuma ya yarda dasu......

Gashi inayin iyakar kokarina domin kaucewa abinda Allah mai girma da daukaka ya haramta, amma wani lokacin sai son zuciya yayi rinjaye a kaina..... tabbas malamai sunyi gaskiya da sukace _wanda yafi karfin zuciyarsa, yafi wanda yake iya rusa birni shi kadai jarumta...._

Wai menene yake damun zuciyata?
Tabbas akwai wata cuta wadda tana bukatar likitan da zai yaye min ita. Likitan da zai bani maganin da zaisa zuciyar tayi laushi ta kuma dace da abinda Allah yake so kuma ya yarda dashi. Zuciyar da zata kyamaci zunubai kamar yadda take kyamatar wuta.... zuciyar da hutunta zai zama saboda ambaton Allah ne......

Wanene wannan likita?
Tambayar dana fara bijirar da ita kenan zuwa ga wani dan'uwa, wanda shi kuma ya turani wajen wani hamshakin malami.... a wani gari nesa da mu kadan.

"Tabbas kana bukatar likitan zuciya."
A cewar malamin bayan ya saurari dukkanin bayanin da nayi masa. Sannan yaci gaba da cewa "Naji dadi, domin kuwa wannan shi yake nuna Allah yana sonka da rahamarsa. Domin wasu sukan tsinci kansu a irin halin da kake ciki amma su a nasu shirmen suna kudurce cewa ai Allah mai gafara ne don haka basu da damuwa don suna afkawa zunubansa, sun manta cewa Allah wannan mai rahamar shine dai Allah wannan daya tanadi wuta, shine wanda yakewa mutane talala kuma shine mai azabtar da bawa tun daga rayuwar duniya har zuwa ta lahira........."

Nayi shiru ina sauraronsa, yayinda nake kara tuno wasu laifukan da nayi wayanda ni kadai nasan da su, sai kuma Allah wanda ya halicce ni. Hankalina ya kuma tashi lokacin dana tuno gudummuwata a bangaren hirar mutane, gulma, karya da sauransu.

"Kana ji na?" Babban malamin ya ambata.
Na gyada kai alamar inajinsa.
Sannan yaci gaba da cewa, zan turaka wajen likitan zuciya, saidai baya kusa, yana can bahagon daji......"
"Bahagon daji?" na tambaya cike da mamaki.
"Kwarai kuwa bahagon daji.... Dajin tafiyar kwana uku ce daga nan zuwa can.... saidai dajin yanada mutukar hatsari da abubuwa masu tsoratarwa... abinda nake so dakai shine ka sani zaka tafi neman ilmi ne, don haka ko mutuwa kayi a hanya ka mutu ne a hanyar neman ilmi. Sannan a hanyarka banda karya banda cin amana. Duk lokacin da wani abu ya shige maka duhu ka roki Allah...."

Malamin yaja bakinsa yayi shiru.

"Mallam saina koma gida nayi shiri kenan?" Na tambaya
"Daga nan ga hanyar dajin can." Ya fada yana nuna min wata hanya mikakkiya.
"Tohm, bari naje gida na debo kayan tafiyar...."
"Idan har ka sanar a gida baka bukatar komai, Allah zai ciyar da kai zai kuma shayar da kai."

Jin haka nace masa "Eh na sanar musu cewa zanzo daukar karatu."
Harna mike zan fara tafiya, saiya kira sunana, na waigo ina kallonsa, fuskarsa cike da farin gemu, fuska mai annuri... "Gwargwadon karyar da zakai gwargwadon wahalar da zakasha...." ba tare daya jira nace komai ba ya mai da kansa kan littafin hannunsa yaci gaba da karantawa.

2

Na tsaya kikam na kasa gaba na kasa baya.

"Akwai abinda kake bukata ne?"
Malamin ya tambaye ni.

"a'a" na fada cikin rawar murya.

"Aikuwa akwai muhimmin abinda ka manta" mallam ya fada amma a wannan karon murmushi ne yake kaikawo akan lebbansa. Yayi shiru kamar yana nazarin wani abu a fuskata, wanda hakan ya tilasta min sunkuyar da kaina kasa. Kamar daga sama sai naji sautinsa yana cewa "Baka tambayeni a ainihin inda zaka iske wannan malamin ba, amma duk da baka tambaya ba zan maka bayani dalla-dalla, domin tafiyarka bata da ma'ana idan baka san wajenwa zakaje ba, idan kuma kasanshi amma baka san inda zaka sameshi ba to namma tafiyar tana zama wahala kawai babu biyan bukata....."

LIKITAN ZUCIYAWhere stories live. Discover now