Page 1

1.4K 84 8
                                    

💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼


*BY HAERMEEBRAERH*

*Ina farawa d sunan Allah,mai rahama mai jin qan bayin shi, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad sallahu alaihi wa sallam, bayan lokaci mai tsaho yau inshaa Allah zan kawo maku sabon labari, wanda nake fatan ya sauya rayuwar mutane da dama, ta fuska kala2, labari ne mai qunshe da darrusa mabayyana, ina fatan zaku bude zuqatan ku masu albarka, kamar yanda kuka saba, domin fahimta da daukan darussan dake ciki.*

*Kamar koda yaushe ina roqon makaranta novels dina,ku na adanawa koda bakuyi sha'awar bi ba a yanxu, kar sai gaba ku zo kuna nema lokacin an wuce kuuu, wannan rubutun ina son nayi d sauri fiye da da, saboda kunsan na koma makaranta, ina roqon addu'ar ku akan samun nasara akan wannan karatun nawa, na gode maku*

Page 1:

Aeeshaa ke zaune a kan kujerar zaman mutum daya, dauke da wuqa da kwano, tare da kubewa tana yankawa, tana yi tana kallon lokaci, aiki take kamar wata inji, ba hutu, abinda ke tsaida ita wannan aiki, sallah.

Cikin sauri ta tashi ta koma kitchen ta dau turmi da tabarya, ta saba wannan kubewar da ta yanka, tana gamawa ta je ta zuba a tukunyar miyar data ji nama da kifi, ta kada ta rufe kadan, sannan ta koma kan tuwon semo da ta tuqa tin minti biyar da ya wuce, tuqawa tayi taga yayi,maza ta dakko leda da mazubi ta fara zubawa tana murde ledar tana sawa a inda ya dace, da sauri ta juya kan miyar dataji ta fara alamar zubewa, ta kashe gas din, ta qarasa rufe tukunyar, sannan ta qarasa kwashe tuwon ta.

Tana kammalawa ta diba fridge taga zobon data hada ya dau sanyi, murmushi ne ya kwace mata, da sauri ta koma ta wanke dik abinda ya dace, ta fara jera abincin akan dinning, sai da ta kammala komai, ta juya da sauri dan wucewa dakin ta tai wanka ta shirya islamiyya, kar ta makara kamar yanda tai da safe, zuwa makarantar boko, taji kiran Umman su, zuciyar ta ce ta buga da qarfi.

"Na'am Umma gani nan zuwa"

Cikin azama ta nufi dakin Umman nasu, inda ta tsaya a bakin qofa, tai sallama tare da qwanqwasa qofar, shiru kafin daga bisani ta amsa mata cikin tsawa,

"Dan ubanki sai yaushe zaki riqe akan ki inna kira ki kina shigowa? Sai ki tsaya dan gulma kina wani jira sai na baki izinin shiga,kina abu sai kace wata uwar mata, da ban son ganin ki zan kira ki ne?"

Shiga Aeeshaa tayi, ta samu gefe ta tsaya tace,

"Umma kiyi hakuri,gani,"

"Yauwa nace kin gama abincin ne?"

"Eh na gama,na hada komai kan dinning, yanzu shirin islamiyya zan, kar na makara kinsan yau banje boko ba saboda makara da nai, na kammala komai har dare nai abincin ma tinda naga tiwo ne"

"Waya saka ki yi har dare? Ni nace ki dafa har dare ko iyayi? Ko kin fini sanin me ya fi dacewa da ayi ne?"

"Umma dan Allah kiyi hakuri bana son ranki na baci, bari inna dawo islamiyya kome kk so zan dafa, dan Allah ko zan fashin boko bana son nai fashin islamiyya,"

"Alhuda huda kenan sarkin karatu, wuce ki tafi,kina dawowa kizo akwai wankin da zaki hada dana qannen ki kimin, kinga sai kisa uniform dinki ma dika ki wanke ko?"

"Eh hakan ma yayi Umma na tafi sai na dawo,"

"To"

Aeeshaa da sauri ta shirya ta fito, dan ko wankan bata samu yi ba gudun makara, in ta dawo tayi.

"Aunty Aeeshaa muma mun shirya,"

"To Ameena maza muje kar mu amshi bulalan latti ko? Ina Abdul hakeem?"

"Gani meye?"

"Kai dai Allah ya shirye ka baka da kunya ko kadan har yanzu,girma kk amma kana shiga daji,"

KUN MAKAROWhere stories live. Discover now