"Baka isa kazo kaci mutincin sarauniya agaban dubban jama'a ba sanar dani abinda kalmominka ke nufi?" Murmushi yae yace

"Aunty amsa kikeso na baki?" Kallonsa kurun take batace masa komai ba, zaro disc biyu yayi

"Sekije ki nutsu ki kalla ki kuma saurara wataqil zaki samu damar baiwa kanki ansa da kanki" kaman  bazata karb'a ba sekuma ta sanya hannu ta karb'a kurun ta zura a jakar hannunta ta bishi da ido, rufe motar yae tare da sanya hannu yae pressing abin d'aga glass zuwa zama, yana shan k'amshin sa yau sarautar yakeji yakuma rasa dalilin daya sanya sam ya kasa yadda waiba sanya hannu sarki ra'uf a wasu al'amuran nasa shidaahaifin sa kurin ya kama ya adane sunan sane shida gimbiyar rusau amma tas seya gano bakin zaren dankuwa baze ragawa mugu ko d'aya ba acikin masarautar, a d'aya b'angaren yana cike dajin zafin meenalyn sa inama ze iya fushi me tsawo da ita dasetayi sati bataga k'eyarsa ba amma ko yanzu zuciyar sa cike take fam da zumud'in son ganin matar tasa, bekai k'arshen tunanin saba k'arar shigowar sak'o a wayarsa ya katsesa, zaro wayar yae daga aljihun sa ya duba sak'on, meenaly ce

"Bansan jin kowa, bansan cin komai, bansan ganin kowa da komai bansan menayiwa idona ba suke hanani bacci ma, ban saniba banida tabbas watak'il senayi kwalli da idanka anawa zan runtsa, ban saniba kose ka ciyar dani zanci abinci, bansani ba kose najika akusa dani jina ze dawo ba, ina ganin kamar yanda dukkanin gab'ob'ina ke ambatar sunanka kaine maganin matsala ta, bansan laifinaba mijina ka yafeni kaji kana raina, bana buk'atar komai illa kazo gareni idan bazaka zoba nikamun izinin na ziyar ceka Takawa na" Wani irin murmushi yae wanda shikanshi besan sanda yayi shiba, ya shagala sosai da karatun sak'on ya karanta yafi so goma kafin su isa gida, kai tsaye part d'inta ya nufa  a sukwane, da sallamar sa ya shiga d'akin nata batare daya jira isoba kaman yanda ya saba, kuyangi da bayi se zubewa suke suna mik'o gaisuwa amma hannu kurun yake d'aga musu abokin tafiya ma mamaki yake yanda akayi yau oga keta zuba murmushi be matsawa kansa ba yayi ta kanshi kawai zuwa part d'inshi

Mik'ewa tae daga zaman datake bakin gadon tana cike da damuwar rashin replying message nata dabe yiba, a hankali ta taka inda yake shi kuwa ya tsaya ya zura hannayensa a aljihunsa yana kallonta fuskar sa d'auke da murmurshi, asaman k'irjinsa tayiwa kantaasauki ta lullub'e bayansa da hannayenta lokaci d'aya ta sauke sassanyar ajiyar zuciya, hannayensabya zarendaga aljihunsa shima ya zagayeta babu wanda yace komai har tsawon mintuna biyu, dan kanta tace

"Ina fatan ba wani laifin namaka ba, tun barinmu adibiti ka canjamun yanzu kuma tun safe ban k'ara ganin kaba, nashiga damuwa sosai Takawa" Saketa yae ya zameta ajikinsa hannunsa ya zura a nata yajata izuwa bakin gadon, kusa da juna sosai suka zauna har suna gugar jikin juna cikin murya me d'aci ya furta

"Meenaly ni fushi na miki fa, ke yanzu bakya mun kishin kanki fisabilillah seki saki jikinki agaban wannan maza, sukuwa su rasa jikin matar dazasuyi practical akanta seke meenaly, a d'azun idan na nace zan miki magana watak'il seta kaiga na mareki tsabar b'acin ran dakika sakani aciki" kwantar da kanta tayi asaman kafad'arsa ta marairace fuska

"Kayi hak'uri mijina, tunanin komai be kawomun ba  hakan bazata k'ara faruwa ba kaji" kawar da kansa yae gefe tunawan da yae da abinda ya faru, zuciyar sa tana masa zafi yace

"Kinma den zuwa asibitin daga yanzu" ya fad'a a k'ufule, hannunta ta d'aura asaman girjinsa har lokacin kanta yana saman kafad'ar sa tace cikin sanyin murya

"Bani wani zab'in dayake sama da naka mijina, banida umarnin da zuciya koni karan kaina zan baiwa kaina se naka umarnin, banaji akwai abinda nakeso sena tabbatar kana son abi  nan, banida buri, wannan buri banidashi wlhy Allah sena son faranta maka, dukkanin hukuncin daka yanke akaina shine abinda ze zauna daram idan hakan shine fatan ka kake kuma ganin daidai ne sena hak'ura da asibiti har abada fatana dai ka hak'ura kaji" besan mezece ba, besan meyakeji ba game da meenal, besan sirrin dake cikin kalamanta ba dake wargaza duniyar tunanin sa kwata kwata, besan wane kalmomibtake amfani dasuba wurin ganin ta sanyashi farin ciki har kullum yana mamakin yanda kalamanta ke sanyashi farin ciki har k'walla yake  idan dad'in ya masa yawa, tallafota yae cikin muryan dabata tab'aji yayi magana da itaba ya furta a hankali

"Banda mahaifiyata da mahaifina meenly aduniya banajin akwai wata halittar danake so sama dake, tun ina k'aryata zuciyata akan hakan harna gano tabbas kece farin cikina, kece abar sona kece nake k'aunar zama dake a kullum, kece mace ta farko dake sanya murmushi bayyana a fuskata idan na tuna ki kawai koda kuwa bama tare, ban saniba ko kinajin abinda nakeji game dake amma ni nasan idan wannan abin danakeji game dake baso bane k'aunace tsintsar ta meenaly, ki tallafi bawan Allah nan ki gujewa b'acin raina, a d'azun dana biyewa zuciyata sena halllaka wannan yaran masu koyon aiki da har wawiyar likita  datayi gigin fallasa mun jikinki awurin k'artin banza, ke kanki sena zaneki" Rungumarsa sosai tayi

"Ina tunanin a tsakanin so dakuma k'auna akwai wani babban abu da har yanzu masana ilimin so basu sanshiba bare su bashi suna, iyakar abinda na sani zuciyata da ruhina da gangar jikina kai kawai suke kira akoda yaushe watak'il wannan baya rasa nasaba da had'uwar ruhi wuri d'aya inaga da zaran an tsaga jinina naka za'a gani sabida tsabar had'uwar jinina dakai daya harhad'a alak'a tsakanin so da k'auna, shauk'i dakuma begenka, banaji wannan k'aramar zuciyar tawa zata iya d'aukar wannan nannauyar k'aunar data tattara abubuwa da dama, idan da zaka bani aron taka danaji dad'i se muyi musayar zuciyoyin mu danmu samu sassauci matsayinka na namiji watak'il zaka iya da nauyin dake rataye a tawa zuciyar nikuma zn d'auki taka matsayina na mace tunda yake na tabbatar tawa zuciyar tafi taka d'aukar nauyi, kodan duba da yanayin danake shiga aduk lokacin da nisan kilometre d'aya jal yashiga tsakanina dakai" Murmushi yae  me sanyi

"Ina sonki meenal" shine abinda ya iya furtawa kafin ya tsoma bakinsa ruf acikin nata....

Mom Nu'aiym.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now