*ZUHRA*
(The flower)
©️2019 Novel
{{Reposting}}
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 1
"Zuhra! Zuhraaa!!"
Wata matsakaiciyar mace da ke zaune bisa kujeran tsuguno gabanta ƙwarya ce rufe da faifai, samanshi robobin talla ne irin na fulani a zaune yake a kan gammo, daga ganin fuskar matar na baƙaƙen Fulani za ka fahimci bata da cikakken fara'a kuma bata da sauƙi sam.
Daga cikin wani fallen ɗaki wata murya ta shiga amsawa
"Nayu Inna, waɗu munyel dami miɗo wara"
(Na'am Inna kiyi hakuri gani nan zuwa).
Ko numfashi bata bari Muryar ta sauƙe ba ta shiga balbala masifarta da bata rabo dashi
"Shegiyar yarinya kin bar min Nono a gantale so kike yamma yayi ki ja min asara ko? Toh wallahi kika bari na isko ki ɗakin nan sai na lahira ya fi ki jin daaɗi Zuhraa in kuma kina ganin wasa nake ki ƙara minti ɗaya ki gani..."
Duk cikin harshen fulatanci suke maganan, kaman kuwa kiftawa labulen ɗakin ya yaye.
Wata kyakyawan yarinya ce wacce ba zata haura shekara 12 - 13 ba ta fito sanye da kayan fulani irin na saƙi riga iya cibiya tare da zani kanta ba dankwali anyi mata irin kitson fulani wasu sun zubo ta gaba wasu ta baya masha Allah tana da dara daran idanu tare da hanci me tsaho da ɗan ƙaramin baki, bata da kiba kwata kwata fara ce sol tana da ɗan tsawo dan ba za a ƙira ta guntuwa ba idan ka haɗa ta da tsararrakinta a shekaru.
Gwiwarta ta kai ƙasa dab matar da ta ƙira da innar cikin tarin ladabin da take da shi da kuma tsoron matar da take ji tamkar rai ta shiga cewa "daaa mi inna" (ga ni).
Innar ta sa ƙafa ta hambare ta a bazata saboda rashin zaton hakan ya sa tayi baya-baya ta faɗi ƙasa.
A masifance tace
"Ai na ganki mara kunyar yarinya, ki ɗauki nonon nan maza ki kai min tallah saura in ga kin dawo da ko ƙwara ɗaya ne ki ga abin da zan miki. Na Naira ɗari biyu ne da furar hamsin, ɗari biyu da hamsin kenan ko Naira ɗaya yayi ciwon kai baki da abincin dare a gidan nan. Kin daina kallona kin ɗauka kin wuce ko sai na hau kanki da duka? shegiya me kama da Mayu".
Zuhra ta tsugunna ta ɗauki ƙwaryar nonon ta ɗaura a kanta ta nufi zauren fita tana hawaye, tana fita makwabtansu ta shiga da sallama.
Wata mata ce ta amsa mata ta duƙa har ƙasa ta furta
"Jam bandu na chubado?" (ina kwana chubado).
Matar ta amsa fuskarta ɗauke da fara'ar ganin zuhran
"Jam Zuhra un vurti kadi?"(lafiya Zuhra har kun fito kenan?).
Zuhra ta shiga amsawa
"Eh, Shatu taski na chubaɗo?" (Eh, Shatu ta shirya ne chubaɗo?)
Kan ta rufe baki wata yarinya ta fito daga zagayayyen toilet da ke daga chan kusurwan gidan tana cewa
"Wai har kin fito? Useni Waɗu munyel haaa mi ɓorna kare njotta ɗo mi wara 'yan dilla." (Don Allah kiyi hkr bari in sa kaya yanzun nan in zo mu tafi).
Zuhra tace
"Toh shatu Yawu useni fu." (kiyi sauri) ta ƙarasa tana jan kujera ta zauna su na ɗan taɓa hira da chubaɗo mahaifiyar shatu, ba'a fi mintuna biyar ba Shatu ta fito daga ɗaki da irin kayan jikin zuhra amma nata baƙin saka ne itama ba laifi kyakyawa ce ta ce wa mamanta
"Chubaɗo ina nonon?"
Chubado tace
"Yana madafi je ki ɗauko na 200 ne."
Tayi chan da sauri bayan ta ɗauko ta dubi mamanta da idanunta ke kan Zuhra da ta miƙe tana ɗora ƙwaryarta a kai ta ce
"Toh Chubaɗo seto 'yan warti"(Sai mun dawo) ta bi su da Adu'a suka kama hanya suka fita suna tafiya suna hira har suka isa kasuwa inda suka saba zama suka nufa bayan sun ajiye kayan tallansu suka samu duwatsu suka zauna akai suna hirar su na ƙawaye.
Sai wuraren la'asar Shatu ta dubi Zuhra ta ce
"Yanzu Zuhra ya za ki yi? gashi nonon bai ƙare ba kuma yanxu ya kamata mu koma gida sbd zamuje islamiya nasan kuma kika koma da saura sai inna ta miki duka."
Zuhraa ta share hawayen da suka zuba mata muryarta a sanyaye ta ce
"hmmm! Shatu ban san ya zanyi ba inna kamar ba mahaifiyata ba yanzu ki duba ki ga jainabu(zainab) tana gida tana kwance bata zuwa tallah ba'a tura ta kiwo sai dai taci kwalliya ta fita yawo amma ni bani da ko lokacin kaina gara hussaini yana tausayamin kinga wani lokaci ma idan inna ta hana ni abinci nashi yake ɗauka ya bani ban da hassan da jainabu sai dai suyi ta mini dariya baffa kuma ba ya cewa komai nikam na gaji da irin wannan rayuwar"
Shatu ta ce
"kiyi haƙuri ƙawata watarana sai labari komai mai wucewa ne".
(Duk cikin harshen fulatanci suke maganan)
Sun jira sun jira har suna shirin makara a makaranta su je a zane su Nonon zuhra bai ƙare ba haka dole suka kama hanyar komawa gida duk cikin fargaba zuhra take, suna isa kofar gidansu shatu sai ga Yayanta gidado ya fito da sauri zuhra ta wuce tana murmushi saboda kunyarshi shima murmushi yayi ya san in ba da dare bane ba za ta iya tsayawa hira dashi ba sam.
Tana shiga gida ta samu kuwa inna na zaune a gaban murhu tana tuƙa tuwon dawa da sallamar dake bayyana fargabar da ke cikin muryarta ta shiga, ko sallamarta inna bata amsa ba ta ɗago ta kalleta tana cewa
"Ina fara kin sayar duka?"
Zuhra tace
"A'a Inna timmai! Lutti ɗiɗi.." (A'a inna bai ƙare ba, saura biyu)
Bata kai ga rufe bakin ba Inna tayi kanta da muciyan da take tuƙin tuwon ta fara jibgar ta kaman ta samu sa'ar ta tun zuhra na ihun neman taimako har tayi shiru saboda babu mai shigowa karɓarta kowa tsoron masifar inna hanse yake.
Baffa ne ya yi sallama ya shigo a daidai lokacin da inna ta ɗauko bakin wuta ta manna mata hannu har sai da zuhra tayi wani irin ihun azaba da sauri baffa ya karɓeta a hannun inna ya fara faɗa
"Haba hansai! Haba me kike yi haka? wannan ai salon mugunta ne sai ka ce ba ke kika haifeta ba? ki dinga azabtar da ita haka? yanzu idan jainabu ake yiwa haka za ki ji daaɗi? Me tayi da zafi da za ki yi mata azaba da wuta don girman Allah?"
Da sauri inna ta tari numfashinshi
"A'a malam ni dai ka daina yi wa 'yata mugun fata ehe, in da ta min abinda nake so zan kula ko iskar da ya dibo ta ne? Uban me take yi tun hantsi har yanzu bata sayar da ɗan nonon nan ba gantali ba?"
Sababi take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba jikinta na girgiza tsabar masifa irin nata.
Shiru yayi saboda shi ba mutum bane mai hayaniya ko tashin hankali yana da tsantar haƙuri shiyasa innar ke taka shi yadda ta ga dama ya kama hannun zuhra dake durkushe a ƙasa tana kuka ya shiga da ita ɗakinshi ya ɗauko magani yana shafa mata, yana gama shafa wa ya ɗauko kwanon tuwonshi ya bata da sauri tasa hannu tana ci hannu baka hannu ƙwarya don ko kalace ba'a bata ba a gidan. Tausayinta ne ya kama baffa yana tunani a zuciyar shi yaushe zuhra za ta samu farin ciki a rayuwarta? sai yaushe ne za ta yi dariya kaman kowa?
Yana cikin tunani ya ji ta ce
"Baffa mi timmini usuko mi yetti ha mi yaha mi ɓorna kare mi ɗo dilla jangirde" (baffa na gama na gode, bari na je na saka kaya zan tafi islamiya).
Baffan ya ce
"Toh daada am sai to a warti jangu boɗɗum". (toh mamana sai kin dawo a yi karatu da kyau).
Ta amsa tana fita daga ɗakin baffa ta shiga ɗakinsu ta saka kayan islamiyanta milk color shirt and ƙimar da brown trouser ta fito ta wuce inna na aika mata da sakon harara..
🖤Gureenjoh🖤
