"Ki nutsu mana Meenal, zaki tashi hankalin ki ne kawai ki tashi na iyayenki, rashin sanin inda kike aiba shi bane horo me kyau dazaki masa, horon dazamu masa aiba yanzu bama se nan gaba" B'ata fuska tayi

"Anty na rok'eki da Allah ki adana ni anan se bayan kwana biyu, kinga dai dukkanin abinda kikace inyi bana miki musu ko, to dan Allah ki taimaka mun da wannan bayan kwana biyu naje gidan" Jinjina kanta tae

"Toh shi kenan idan yayanki yazo kinsan dai halin fad'anshi, sekiyita hak'uri da abinda zece mun nidake, sannan zancen cikin nan karna k'arajin kina maganar zubar wa wlhy kinji na rantse ko a zuci karna k'araji" hawayen idanta ta d'auke da d'an yatsan ta

"Bazan k'ara ba Anty,har maganar sakin ma bazan k'araba, amma wlhy sena rama wannan wulakancin guda biyu, na farko wannan latsani dayake yana barina da ciwon ciki kuma wlhy senaci uban jakadiyar sa me mammatsa k'afa yana lumshe ido dan samun wuri" Dariya taso k'wacewa maman humaira tabbas kuruciya tana yawo akan wannan baiwar Allah, ga kishi amma batamasan meye ba, bazata iya cewa ga inda ke mata ciwo ba....

"Gaskia semun rama, har wata jakadiya ce dashi me masa tausa, lallai dani zataci gidan su, yanzu dai ki tashi kiyi wanka ki sauya kaya ki saka nawa kizo kici abinci se bacci ko?" Murmushi tayi tamike, haka tazo tana cin abincin tana toshe hanci batason warin shi anty tayi dariya lallai yau manya ne da ciki kenan🤣🤣🤣.

*************
    Beko waiwayi hotel d'inba se wuraren 5 na yamma likis, gashi ya gaji ba abinda yake buk'ata irin yaci ya kwanta tinda ya fita yake tsaye akan wasu harkokin sa, matar daya baiwa key tagama duty harta tashi ta barwa wanda ya karbi duty key nasu, beko tambaya ba yasan meenal na d'akin koda yaje ya tura a rufe, beyi mamakin komai ba ya soma knocking kusan 10 mns yana tsaye agun, ganin kamar kota k'ara fitane ya sanyashi juyawa zuwa reception d'in, karb'an key yae ya koma yana tunanin tafita ne bayan ta dawo amma mesa take yawo ne irin haka? Bata tsoron wani ya ganta mesa ne yanzu meenl bataji wai? Tsaki yaja yashige wanka, yanayin d'akin ya nuna masa bata dawo ba sam, har dusbing ya duba bega shirgin kayan takeaway na breakfast datayi ba kurn dai yaga na jiya da dare kenan cleaners ma basu zoba, to ina meenaly ta shiga ne? Ya tambayi kansa, dama rigar suit ce ajikinsa ita kawai ya cire ya juya zuwa reception da hanzarin sa, yayi tambaya akan meenal amma sunce basu ganta ba, yafa shiga rud'u lokaci d'aya ya tashi hankalin hotel d'in, ganin ze musu bori ya sanya manager yasa aka lalubo cctv, tu  wuraren 8 am data fita bata dawo ba sam babu ita acikin masu shigowa, idan ma wani abin ne to kuwa da k'afarta tafita kuma ba'a wurn su ya same taba. Abokin Tafiya yakira yazo shi kuma ya sameshi har d'akin sa, hannayensa ya zuba duka a aljihunsa beko cire madubin idan sa ba dake fari k'al ya k'urawa Abokin Tafiya ido ya kasa furta komai se kallonsa yake shikuma yana zaune asaman kujera k'waya d'aya jal dake d'akin shima kallon Takawa yake yana nazarin sa, ba abokin sa bane ba yaron sane amma tun suna yara yake masa hidima suke tare, yasan koda ya tambayeshi bawai amsa ze bashi ba dan bega dama ba, dan haka ya k'ura masa ido kurin yana nazarin yanayin sa har kusan mintun goma sha uku, harya cire tsammanin ze masa magana sekuma yaji yace

"Bangan taba fa, cctv ya nuna tun 8:am tafita daga nan" hannayen sarkin mota dake kan saman kujerar ya tattaro gu d'aya

"Wacece Ranka ya dad'e?"  Sajensa yakaiwa cafka zuwa gemunsa yaja gashin gemun da k'arfi kaman ze cirge shi kan yace

"Ameena mana sarauniya Ameena bansan ina taje ba wlhy" Cikin takaici yace

"Takawa kai d'inne nima idan abubuwan ka suka motsa seka rik'a tsoratani dajin ikon kan nan, nifa naga fitarta na dinga kiranka awaya kak'i d'aga wa, nazo nabita har tasha dataje batasan ina binta ba, naga tahau kotar abuja, tunkan motar ya tashi naci gaba da kiranka baka d'aga ba, haka na barta ta wuce abunta, bayan kafito ko maganar msd col bakamun ba banji kana neman taba, shine nayi tunanin kasan da fitar tata na kame bakina" Bangon dake kusa dashi yakaiwa mugun duka cikin k'araji

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Où les histoires vivent. Découvrez maintenant