*************
      Lokacin duba system ne awurin meenal, bata buk'atar ranar walimar ta samu matsala koda k'waya d'aya ce kuwa, Zaman dirshan tayi akan gadon dukda tana fama da ciwon mara kwanakin nan aganinta period ne zezo mata dan haka bata wasu 'yan damu ba, dama kuma tanaso taje asibiti sabida ta wuce lokacin period d'inta da kusan sati biyu hakan kuma ba sabon ta bane ba sam, duk yandabtae 21 day's da gamawa to dawuya time d'in ya wuce batare data yi wani ba. Kamar kullum yauma b'angaren sarauniya hassy take lek'awa sabida tsaro, tana cikin rud'u ganin batasan me suka tattauna da kuyangar taba a wancen lokacin, tasha mugun takaici kam sabida bawai tagama yarda da hassy bane ba, mamakin ta be k'aruba seda taga sarauniya Daurama a gidan hassy suna tattaunawa

"Yanzu ke hassy da sauran jininki a jiki zaki yarda ki zama koma baya? Kinsani dai ba sabona bane ba zuwa gunki amma wannan abun tabbas ya tayarmun da hankali wanda naga dole inyi ruwa inyi tsaki akan shi" Kallon Nazari hassy ke mata secen ta nisa tace

"Matarshi ce babbar 'yar iska ai Ranki ya dad'e, bansan dalilin dayasa ta mayar dani wawiya ba, setazo guna da mugun dad'in bakinta ta gama yaudarana ta gudu, dayake ma tanada wani boka daya iya aiki shisa ban mammaka mata rashin mutunci ba har yanzu, yanzu tazo tace dani ranar walima a kasheshi ta hanyar poison amma wlhy se ranar tazo kiga ta canja komai ta kub'utar dashi, yanzu kuwa na sauya takuna akansu kwata kwata, ta hanyar dabata zata ba zan kashesu dukkansu har ita" Da gefen ido Daurana ta kalleta

"Karfa b'acin rai ya sanya ki aikata abinda zakizo kina masa dana sani nan gaba kad'an, bakya ganin kamar ranar walimar yayi sauri ki bada time mana, yanda bazama a zargeku ba amma hakan ai garaje ne" Murmushin dabe wuce labb'an taba tae mata

"Bazama a ce mu bane, gardawa ne nayi hayar su daga waje zasuzo su sacemun sarkin da kaf ahalin sa, se an shekara ana nemansu zan saka a hallakar dasu gaba d'ayansu ai idan sunsan wata basu san wata ba, wlhy sena ciyar dashi kashi tunda tak'amar sa jin kai, Hidar da Meenal kuma tun dama cen na shirya basu wani maganin baccin daze saka baza'a tafi dasu walimar dan kuwa bazan cutar da 'ya'yan 'yata ba, hatta gidan da zasu zauna na gama shirin komai na gidan tsaf, kuma har Amo tunda bata sona nima bawai sonta nake ba, ita kuma matar tasa agabansa zansa aimun raping d'inta" Murmushi irin na manya Daurama tayi

"Lallai kinada basira, Allah ya shige mana gaba to, idan kikai hakan kinyi daidai kuwa"  murnushi tayi ta waiga kad'an ta kalli gefen ta ba kowa sannan ta matso kusa da ita sosai ta rad'a mata wata maganar...Meenal bazata iya jiyo me aka ce ba amma tabbas taga yanda tshin hankali ya bayyana k'arara a fuskar Daurama! Murmushi Meenal tae sabida kanta ma ya dena gane komai zuwa yanzu, duk yanda take tunanin masarautar da munafurcinta abun yaci tura, abubuwa biyu ke damunta, na frko dai rashin sanin menene sarauniya hassy ta gayawa Asha da kuma wanda ta gayawa Daurama.

**********
   Tanaso tae magana da Sarki amma taga alamun abun dakamar wuya wai gurguwa da auren nesa, koda wane lokaci abubun fada kan tauye mata saduwa dashi, tasoma shiga damuwar rashin k'amshin sa, batasan taka maimai meyake sanya takeson k'amshin na jikin saba, Nusy tawa waya akan tana nemanta befi 30 mns ba nusyn ta karaso, muhimman abubuwa suka tattauna kan daga bisani ta mata sallama ta wuce, fitar dole zatayi dole ma taje gun mom d'inta, anzo gab'ar datake neman taimakon mom d'in da shawarwarin ta, zaman shiri tayi bayan ta fito wanka amma abun takaici duk kayan data d'akko ta sanya seya matseta yanda bazata wali acikiba, zama tae ta soma k'wallan takaici gata ba gwanar yin zani ba, bakuma zata iya fita a yanayin suturun masarauta ba sabida nauyin su, yanayin gaisuwar dataji na tashine ya tabbatar mata cewar Takawa ne yazo gunta watak'il labarin zuwa b'angarenshi a lokuta ma banbantane ya riskeshi datayi baya nan, Ko motsi ba taiba harya iso wurin datake, da idanta dake zubar da k'walla ta kalleshi

"Barka da zuwa" shine kad'ai abinda tace dashi ta kawar da kanta gefe, zama yae kusa da ya rik'o kafad'unta

"Sarauniyar Hankaka gaba d'aya ke kuka kuma? Ana zaune qalau lafiya kuwa?" Turo bakin nan tae

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now