Haka Haris yae taku ya shafawa waziri abinda ze dawo dashi hayyacinsa shi kuma yae saurin lafewa koda waziri ya farka ya ganshi amota shida haris seya kid'ime ya kwashe shi zuwa masaukin su dama kowa da nashi abokin kwanan, tunda yake sarki yana tare da sarauniya shi kuma yana tare da haris koda haris a parlor yake shi yana kurya se mahaifiyar sarki da kuyangarta itama. Haris ya seda ya nak'alci anyi fin awa sannan ya motsa da waziri ya fara cin karo yanata faman had'a gumi ya mik'e cikeda tsoro

"Ranka ya dad'e wazirin wazirai, ya akayi muka dawo d'akin? Mun fasa tafiyar ne?" Girgiza kai waziri yae

"Baccine ya kwasheka sena hak'ura kawai,ganin baze yiyu muje kana baccin ba,ka manta dana tasheka mukazo d'akin,ai kana shiga motar se bacci shine na tasheka mukazo d'aki" Jinjina kanshi yae yana me zubewa a k'asa

"Ka gafarceni Shugabana ban kyauta ba wataqil faruwar hakan baya rasa nasaba da tsantsar gajiyar dake jikina ina neman afuwa" Murmushin yak'e yar

"Ba komai haris ka kwanta abunka ai kanama k'ok'ari" godiya yae yaci gaba da kwanciyar sa, ya gano waziri so yake ya adana wannan sirrin sabida yasan sarki Abdura'uf besan da zancen b'oye d'an uwan saba sam!

************
   Meenal se zagayen gidanta takeyi tana neman abinda zataci kafirar yunwa takeji, Malmo ta gani a  kitchen

"Malmo me kikeyi ne?" Kallonta tae sekuma ta zube ta sani yanada wahala ka ganta a kitchen d'in

"Ranki ya dad'e Sawun Takawa, Takawa ne ya buk'aci in Masa farfesun naman kai  kafin ya dawo, tona idar shine kuma nake kwashewa" Washe baki tae

"Zubomun me yawa a bowl ki had'o da fresh milk a fridge" juyawa tae batare data jira amsawar malmo be, zuciyarta ke tashi warin abincin ne duk taji bataso amma tana kwad'ayin abincin. Haka taje bed room ta baje a k'asa tana jiran akawo mata hadda ajiye tissue da tsinken sakace, da sallama malmo ta shigo ta dire  mata farantin agaban ta komai yana kai da sauri ta toshe hancinta

"Malmo dandai inajin wata uwar yinwa ne dabazanci abincin nan ba, kinsaka masa wannan spice d'in na indiyawa dayake nacewa ni bason warinsu nake ba wlhy" cikin girmamawa tace

"Babu abinda na saka daya dangancesu se kayan mu na gargajiya" Nisawa tae tana toshe da hancinta ta d'auki d'aya ta soma ci haka ta dinga cn abincin hancinta a toshe malmo ta tasata a gaba se mufmushi takeyi dankuwa ta soma hasaso wani abu daga wurin uwargijiyar ta in haka ne tana murna matuk'a

Takawa ne ya shigo d'akin da sallamar sa fuskar nan a matuk'ar d'aure yau sarautar yakeji bako k'arya, kallo d'aya malmo ta masa ya wurga mata mugun kallo

"So nawa zanyi hani akan kallo na? E ban gaya muku ba karna kuma ganin idan ku a nawa ba?" Ban Hakuri tashiga yi amma ko k'ala be sake ce mata ba seda Meenal ta sauke d'ankwalin dake hancinta tace

"Ke tashi kije" sumsum tabar d'akin k'irjin ta yana dokawa rabon dataga uban gidansu a irin wannan yanayin harta manta sam! Halin ya motsa kenan, zama yae kusa da ita amma akan gado ya d'aura k'afar sa d'aya akan d'aya yana wani k'ara had'e fuska k'ala bece mata ba itama kuma ko kallon inda yake batayi na, seda ta cinye naman kan tatas sannan ta k'wallawa malmo kira, tazo ta tattre kayan

"Ki tabbatar kin sanya turarukan wuta masu k'amshi agidan nan banason warin wannan farfesun dakikayi" Kanta a k'asa ta amsa da

"An gama Sawun Takawa" ta juya ta fice toilet taje ta wanke hannunta da Abin wanke hannu ta wanke bakinta ta fesheshi da mouth freshner ta dawo d'akin, k'amshin farfesun ya daki hancinta da sauri ta toshe da hannunta sannan ta kai hannunta kan mirro tashiga feshe d'akin da freshner har kala kusan 5 ta saka sannan ta sauke hannunta har yanzu akwai alamun k'anshin, tsaki taja tana mamakin wannan abin, idan ba barin d'akin tae ba tabbas seta amaye 'ya'yayen hanjinta, Anan ta barshi zaune zuwa d'ayan d'akin dayake mallakin sa ta shige abinta... Haushinta dukya isheshi wato bazata iya gayar dashiba kenan? Yayi saken da Meenal ta gama rainashi mik'ewa yae ya nufi d'akin yana tunanin cen ta tafi, kwance ya taradda da ita da remote control guda biyu, na farko dai AC ne tana rage k'arfinsa sabida yana mata yawa na biyu kuma na reviever ne tana k'ok'arin tsayar da channel d'aya na india ta kalla, zama yae ya k'ara hard'e k'afafuwan sa wuri d'aya yana kallonta amma ko gezau yima tae tamkar bata tab'a ganin saba

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Onde histórias criam vida. Descubra agora