"Ke karki d'auka cewar zaki mun wayau, tunkan uwarki ta wurgoki duniya nake a wannan masarautar nakuma san makircin mata" duqar da kanta tayi

"Bazanji hushiba danida nina jawa kaina rashin yarda awurinki, amma ki yarda dani in miki dukkanin aikin dakikeso na miki akan Takawa kiga aiki da cikawa" Tsaki taja

"Danla tashi ki barmun b'angarena, kokinsan inada ikon dazan sanya amiki wulakanci a wannan masarautar" Murya na rawa ta furta

"Ki rufa asirina, na miki alqawarin bazan tab'a bari sarki ko hajiyar Rusau suji cewar Yarima Fu'ad ba jinin me martaba bane jinin waziri da matarsa kurin ke yawo ajikin sa" Zabura tayi jin wannan maganar, tasan masarauta akwai kunnaye da idanuwa masu yawan gaske, waige waige ta somayi, seda ta tabbatar ba kowa sannan taja hannunta zuwa d'akinta na lungu, seda suka isa ciki ta wurgar da ita seda ta fad'i, d'agawa tae ta k'ara duk'awa cikin girmamawa
"gayamun inda kikaji wanan?" Kallon ta tae kanta k'arayin k'asa da kai

"Ranki ya dad'e Wurin boka me magana d'aya naji komai, shine kuma mutumin da yakewa Sarauniya daurama aiki tuni, kin kuma san ya da ta k'ware a makirci" Jinjina kai tae

"Zaki had'ani dashi?" Duk'ar dakai tayi

"Mezai hana kuwa, kokuma ki aika baiwarki, tabbas bazaki iya bi hanyar dake sadaka da gidan saba, sabida kashine layi d'aya ake takawa kuma d'anyan kashi kan a isa, nima kaina k'anwar mahaifiyata ladi nke aikawa da saqona" Sauke ajiyar zuciya tae ta soma aminta da yarinyar

"To yanzu kozan iya sani sauran sirrikan dake b'oye wanda ban saniba, murmushin mugunta Meenal tae sannan ta zauna, tace

"Ai baki isaniba, ita wacce me muku zaman banza a masarauta fa da sanya hannunta a kisan Salma, amma banso ki d'aga hankalinki, sabida kinga dai abin nan bamuda shaida, dole mu lafe semun nemo shaidu tukunna ko"

"Ban gane wa kike nufi ba?" Seda ta d'an waiga sannan tace

"Amoh mana uwar mu'az, aikinsan cewa fa tai kume kuka kashe tsohon sarki, sabida haka seta k'arar da zuri'arki kema, babu wanda yasan wannan maganar se baiwarta Kande, zama ki iya tutsiye kande ki nunata da wuk'a idan bata fad'a ba kice zaki kasheta, tausayi kika bani ai shisa nace dole in fallasa maqiyanki wlhy" share k'wallah Hassy tae

"Meenal da gaske wannan maganar, Amoh fa 'yar uwatace" Nisawa tae

"To ke kuma dai Sarauniya me adalci, keda kuma kika hanata haihuwa fa? Mu'az m ai rabone" kallon tae aranta tace yarinyar nan bokanta yanaci, sabida haka dole ta damk'e ta hannu bibbiyu

"To amma ni ai ba kisa nayi ba ko Meenal, salma tana sonta tana mata biyayya meze saka ta kashe ta?" Murmushi Meenal tae

"D'aukar fansa takeso tayi ai kekuwa akan mijinta, acewarya fa bazata bari Salma take haife haife da yaronta ba, yoke abinda na lura dashi ke bakya b'oye fad'anki ita kuwa kirsa, nifa bari kiji Sarauniya wlhy neman dukiya ya kawoni gidannan, akan mu'az ma hayata akayo, tunda gake mijina ya mutu sena amince da buqatar su ko iyayena basu sani ba, so akeyi na kasheshi" kallon mamaki ta k'ara yi mata tace

"Waya yo hayar taki akan kisan takawa" murmushi tae

"Baki gama yarda dani ba tukunna, nima bazan kwashe duka cikina in sanar dake ba" Murmushi sarauniya tayi

"Yanzu me kika shirya yi da takawa, banason binda ya tab'a lafiyar jikokina gaskia" Murmushi Meenal tayi

"Zan masa dad'in baki ki k'wace su daga hannunsa, idan kina basu Extra care babu me zuwa wurin su anan yace ze cutar dasu kome kikace, school ma naga ba zuwa suke ba" Nisawa tae

"Baze iya kaisu skul anan ba, a london sukeyi kuma tunda ya d'auki hutun nan me tsayi be mayar dasu ba dama baki sani ba?" Murmushin takaici tayi

"Yoni bafa wani saba nayi dashi ba koda akai auren, bokana kurun na saka ya curawa yaran soyayya ta, ta hakan na mamaye shi shegen se girman kan tsiya" murmushi Sarauniya tae ta k'ara yadda da meenal dan tasamu labarin hakan akan da yaranshi ta mamayeshi.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now