"Am so sorry my Meenaly, kidena kukan haka kanki zeyi ciwo kinji, Baccine ya saceni nasha maganin mura" Tabare fuskar nan tayi cikeda shagwaba ga jikinta se rawa yakeyi

"Bakai bane kake barina nini kad'ai kullum, yaa muhammad na baya mun haka, nice ma nake gudunsa, ni Allah gobe gun mommy zani tsoro nakeji" Tana maganar ne cikeda tsoro jikinta se rawa yakeyi, k'ara matseta yae jikinsa yace

"Bazan k'araba Meenaly, kullum zanna rik'a kwanciya wuri d'aya dake, bazan k'ara baiwa kowa damar cutar dake ba, kuma zan hukunta wanda suka nemi hallkar dake" Sautin kukanta ta k'arawa yawa

"Wanan mugun fa cewa yake zeyi raping d'ina, wlhy bazan zauna anan gidan ba, so yakeyi ya tonamun asiri, idan kuma ya dawo gobe fa" Jijjigata ya shigayi

"Meenly aishi aka Harbe a bayanin danaji, so baze dawo ba kinji" Itadai batada nutsuwa da alama sambatu ma takeyi

"Cewa sukeyi zasu yanke faratana duka gom na hannu harda harshe na, Takawa dafa Allah be kawo kuba da tuni nasan na zama tarihi kasheni sukeso suyi" Besan da wane bakin ze soma rarrashin taba wannan ya sanya ya shiga bubbuga bayanta kurun, se uban kuka datake rusa masa har kusan asuba batayi bacci ba kuka kurun takeyi,  zuwa wannan lokacin jikinta ya d'auki zafi sosai, se rawar sanyi takeyi, duk inda ze juya tare yake juyawa da ita tana jikinsa, tausayin ta ya hanashi koda raba jikinsa da nata, tunanin mafita yakeyi, Baya tsammanin mutanen masarautar hankalinsu har yakai akan Meenal tunda yake bata dad'e a masarautar ba, incident na food poison daya faru ya d'aukeshi akan cewar  shi aka so yiwa amma wannan abun daya faru ya sani sarai ita ake hari, zancen a datse 'yan yatsu dakuma  harshe wannan abune dayake nuni kai tsaye  cewar tasan wani babban sirrin su dabasa so aji, idan hakane meta sani?, kuma acikin masarautar su waye?, anya beyi sakaci ba kuwa? Daya kasance be sanya idanshi akan 'yar mutane daya kawo acikin fitiniba, sodayawa yake ganinta tana zagaye acikin mabanbantan sassan dake cikin masarautar be hanata bane sabida ya kula da k'warewar ta wurin furta kalamai a baud'e, yaga kuma yanda take zubewa take qasqantar da kanta agabansu...

    Shiya taimaka mata tae salla, sannan tayi wanka da kanta fuskar nan kam se a hankali ta canja matuk'a dan yau hadda wani bak'i tayi inda mari da naushi ya sauka sanda sukeso su riqata tasaha naushi, sannan banqarar ma dasuka mata duk jikinta ciwo yake mata, tashiga yanayi me ciwo....
   Yanzukam Takawan Bashida yarda da kowa dake b'angaren nata se kanshi, dan haka da kanshi ya soya mata k'wai da tea ya had'a ya kawo mata, da kanshi kuma ya bata, tana gama shansu se amai, zazzab'i sosai takeyi harta soma ganin jiri, Dr. Ayub ya kira aka mata allura sannan yae shirin gagggawa na barin fadar da ita batare da sanin kowa ba, haka zalika kuyanginta ma da fadawa masu tsaron kofar waje be tafi da kowa ba, koda yafita da excort kan hnya aka ajiyesu, iya wayoyinsu da system data buk'ata ya bari aka d'akko mata, shima ana ajiyesu kan hanya ya karb'a da kanshi ya rik'e wasu, batasan dalilin fitowar suba kurin dai tasan jiri takeji, wani hotel sukaje sukawa kansu masauki, suna zuwa ya kama d'aki babba, yaje ya kama d'akuna gudana 4 dukda sunan sa, seya zab'a d:aya yaje ya suka baje, da kanshi ko yanzu ya mata wanka sannan ya ordering abinci, k'inci tayi ta soma kuka, shikuwa ya hau aikin rarrashi

"Haba Meenaly, kukan nan baze k'are ba wai? Ehn? Kanki ze k'ara ciwo ne my baby ki dena kuka kinji, inshaa Allahu babu wani abinda ze k'ara samunki, yaranki ma da Ummi na sunacen na bada tsaro sosai a kansu" kallonshi tae da jajayen rinannun idanuwan ta tace

"Abul khair bazan iya ciba, banida appetite kuma kaga hak'orina ma ciwo yakemun tunda wannan ya makamun mari" Tallafota jikinsa yae

"Babyna sannu, idan bazaki iya tauna abincin ba nizan tauna sena baki ki had'iye" Kallonsa take ido cikin ido, Meenal tasan meye aure, tasan meye jima'i amma baka rabo sabon shiga da tsorata maganar shi ma ta bata mamaki, kawar da kanta tae gefe d'aya

"Abul khair, nizan iya ci da kaina, wannan ne bana so, ni dan Allah ka kaini gun mommy" Dafe kanshi yae da hannu d'aya

"Meenaly, kin cika Rigimafa, tayaya zan kaiki gun iyayenki a haka? Dan Allah ki nutsu me kikeso yanzu?" D'an turo Baki tayi

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now