"Acikin biyu wanne ka zab'a, kawa Takawa rashin kunya ka hanata hanya kokuma kabarta ta shige ta kareka akan ita ta matsa" kalon juna sukayi shida d'an uwans suka janye wasu dogwayen takubba na mayak'an da dasuk gitta ta shige seda tad'an taka sannan ta waigo tace da kuyanginta

"Kuje ko wacce ta kaiwa waninta ziyara adawo k'arfe sha biyu na rana"  godiya sukayi sannan suka juya kowacce dama tana jiran irin wannan  damar tayi abinda take ganin shize fitar da ita....

  Kai tsaye inda take tsammnin nanne bed room d'insa ta nufa, da sallamar ta ta shiga sedai ta tarar ya rage hasken fitilar d'akin se deem light kurun alkyabbar jikinta ta zare ta rage kayan nauyi tukunna ta shige ban d'akin sa, Ba laifi akwai wadatacciyar tsafta k'ara gyarawa tayi sannan ta wanke wasu tsirarrun boxers da singlet data gani da wasu handkerchiefs ta shanya awurin dataga an tanada donsu, fitowa tayi tashige duka sauran d'akunan ta gyare ko ina sannan ta shiga kitchen tasha dariyar ganin yanda yake a harkitse tasha wahalar gyaranshi sosai seda taga komai k'alk'al sannan ta juya gefen kayan abinci duk wani abu daya lalace t cireshi a fridge dasu albasan dasuka rub'e ta jefar  a wani buhun semo ta zuba komai ta bud'e k'ofa ta baiwa wasu Fadawansa su zuba, lokacin sha d'aya tayi ta shige kitchen d'in ta masa lafiyayyan girki sabida komai akwai a part d'in abu d'ayane ya takura gidan shine rashin mace aciki, ga alama ko girkin namijine keyi da kansa,seda ta jere komai a dining sannan ta koma d'akin wanka tayi har lokacin bacci yakeyi kayan data cire ta mayar sannan ta koma b'angarenta lokacin k'arfe d'aya na rana tayi ma.

    Koda ya farka seyaji k'amshin dayasn ba nasa bane amma yakanji jiyo k'amshin jikin wani makusan cinsa kodai mafarki yakeyi?, mik'ewa yae zuwa ban d'akin nanma yasha mamakin ganinsa k'alk'al  ko ina yayi fesfes ga k'amshi me ratsa zuciyar me shak'ar sa ya kwantar masa da hankali...yaga kayansa asaman hanger a shanye yasan yace kar wanda ya shigo masa zazzab'in mura yake fama dashi, magani yasha mesa bacci shisa yaketa bacci tamkar gawa, ya gayawa Amoh ta dena turo masa komai daya shafi kuyangin nan kar suyi poisoning nashi, ya iya  girkinsa daidai gwargwado ze iya d'an gyaran gidan sabida tsaro.....wanka yae sannan ya fito daga d'akin yasha mamakin ganin komai qalqal idanshi na kaishi dining ya gano k'amshin abincine yakeji, k'ofa ya bud'e  kira wani daga cikin bayinsa

"Waya shigo nan part d'in? Ya buk'aci sani

"Sawun takawo ce ta kawo ziyara kuma bamu isa mun hanata shiga ba" Jinjina kanshi yae yana murmushi, aranshi yace wato tanan ta b'ullo abincin ya bayar duka sannan yasha tea daya had'a da kansa, yabar gidan...

********* wuraren k'arfe biyar aka aiko tafiya da sawun takawa b'angaren sarauniya hassy, yana kallon sanda suke wucewa yae murmushi danshi bega amfanin wannan ba, Acen kuwa wanka akai mata da ruwan turaruka masu tashin hankali, bayan nan aka cika wani tsohon baho da ruwa aka sakata, yasha flowers masu alasin k'amshi da dad'i, tayi awa d'aya aciki harta k'osa a fitar da ita, hankalinta sosai yake a tashe jin abinda tajiyo datake sauraren recordings na duk maganar da akeyi a inda takai abin recording d'inta, acikin ruwa take amma gumi sosai take had'awa sabida tsoro, ta tabbatar masarautr nan akwai munak'isa acikinta, wanda kakewa kallon masoyinka ma bakasan meyake maka tanadi ba, tabbas makashinka na gindinka.

An shirya sosai Nakai amarya d'akin mijinta, an gama shirya komai shima kuma yasha shiri sosai zuciyar sa ba dad'i se baya take kaishi yana tunano angwancinsa da Salma abar sonsa ko guntun murmushi babu  fuskar sa....

************
   "Na gama shirya komai, daga zaran an kaita ka aika message d'in kakuma dinga kiranta kamar ba gobe, tuni anyi saving number wayarta As Maryam acikin wayarta, yanda ze k'ara yadda b'oye lambar tata takeyi" Wata dariya wanda ake gayawa maganar yae

"Bakida matsala hajiya wannan duk me sauk'i ne zanma k'ara da maganganu masu rikitarwa sabida tada hankalin 'yan mazan, tun yaushe muke jiran wannan chance aikoda wasa bazanyi wasa da wannan damar ba" Murmushi sukayi du kansu kansu ajiye wayoyinsu.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now