Farkawa yae amma dukta k'amk'ameshi, murmushi yakeyi daya rasa dalilinshi ya zame jikinshi wanda yae sanadiyar farkawarta, janye jikinta tayi tana k'ok'arin wazgewa, murmushi ya k'arayi kanya fita daga d'akin zuwa parlor itama tana d'ingishi tabi bayanshi, dawata iriyar yunwa ta tashi, shisa zataje kitchen neman wani abu tasa acikinta, tun ranar data soma ciwo yauce rana ta farko dataji tanason cin abinci

Karo yae da Nusy tana zagaye yae turus

"Talented Nusy lafiya dai?" Waigowa tae shima kanshi yayi noticing razanar da tayi

"Yallab'ai nazone mu gaisa da sawun takawa, ban santa tab'a gaisawa da itaba" Jinjina kanshi yae kurun ya nemi wuri ya zauna kannan zare madubin idanshi ya d'aura saman side table dake gefen kujerar dake kusada shi, ya zaro hanky ya soma goge idanshi yace

"Nusy ki zauna mana, ga wuri nan" kujerar da side table ya rabasu ta zauna, sannan ta zube k'asa bayan d'aura wayarta kusa da madubin nashi tace

"Barka da war haka takawa" Hannu ya d'aga mata yace

"Barin shiga daga ciki" ya wuce zuwa cikin gidan, a coridor ya had'u da Meenal yake sanar mata, sad'af  sad'af ta tako tana lab'ewa, tana kallon sanda ta cafki madubin takawa ta zaro wani abu a jaka ta lik'a asaman madubin ta gefen dake kusa da kunnen sa, ta ajiye da sauri jin motsin tahowar wani abinda ya janyo fad'uwar madubin adaidai isowar Meenal, wani mayaudarin murmushi meenal ta sake mata sannn taje ta zauna kusa da ita suka gaisa cikin karmci a gaggauce ta mata sallama ta wuce, agogon ta cafka itama ta, soma binciken abinda ta saka, Tana dubawa taga ashe tracker ne, tana k'ok'arin cirewa y k'araso a wurin, karb'e mudubin yae ya kalli inda yaga tana kallo, d'an k'aramin abune manne a wurin, bak'i yasan ba komai ajikin madubinsa koda yae bacci ma dashi ya kwanta kuma dashi ya tashi, wani mugun kallo yawa Meenal, cikin rud'u tace

"Abu Haidar waccen cef data fita ta saka" Tsaki yaja kurun ya fita kai tsaye wurin Nusy yaje a hanya ma suka had'u, mik'a mata abin hannunshi yae, K'irjintane yae mummunar dokawa

"Waccen yarinyar ta rainani meye wannan ajikin madubina na kamata tana sakawa?" Murmushi tayi ganin cewar koda ya kama abun be kawo ita bace, duddubawa tayi

"Tracker kuma Takawa, ai kaga abinda naketa jiye maka, kaddai wani abu take shirin aikata maka, shekranjiya ma danaje gidan naji tana waya akan wai zata kammala komai zuwa jibi, ashe aikin kenan datakeyi" Nisawa yae yace

"Ba komai kije kawai, zan miki waya akan maganar" Harta juya ya kira sunanta

"Nusaiba" waigowa tae tana masa murmushi

"Baki ciremunba ko kem kina son zaman tracker d'in a wurin ne?" Murmushi tae

"Haba yallab'ai me hakan ze amfanar dani, hankali nane yaje wurin tunanin dalilinta na bibiyar rayuwar ka" karb'a tayi kawai ta cire sannan ta mayar masa da mudubin. Juyawa yae batare da yayi magana ba yana ayyan yanda zeci ubansu idan ya tabbatar.

Be koma part d'in ba har aka kwana uku hakan ya bata mamaki ta tabbatar cewar wani zargi yake akanta game da hakan, musamman da aka gaya mata sun jima tsaye tare da talented ranar da abun ya faru, ganin ta samu sauk'i ya sanya ta sanya aka shiryata sosai ta fito daga b'angarenta tare ta Kuyangi su goma seda suka d'auki hanya sannan tace

"Bangaren sarauniyar Hankaka" Da sauri sukayi layi itace a tsakiya suka d'auki hanyar wurin, a zaune suka taddata tanata faman jin mulki, ana mata tausa tana cin Apple har k'asa ta zube tana rero gaisuwa da kirari, hakan yayiwa sarauniya hassy dad'i se wani blushing takeyi

"Amun afuwa Ran sarauniyar Masautar Hankaka ya dad'e, banzo na kawo gaisuwa ba kwana biyunnan duk banji dad'i bane" Zabura tae ta wurgar da Apple dake hannunta, sekace wacce aka aikowa da labarin ranar mutuwar ta, lokaci d'aya ta mik'e tanata zare ido

"Yaya Takawa ze karya dokar masarauta? Yaya ze taki takalminsa tunkafin wankan masarauta ya tabbata a kanta? Lallai yayi kuskure kuma yau zan had'u dashine" sadda kai k'asa Meenal tayi

"Ki gafarceni sarauniya, hakan be kasance ba, Hasalima Takawa bashida labarin takalminsa sabone har yanzu, ciwone daga Allah" har zuk'a ta k'arayi

"Kwananki nawa aduniya? Yaushe ma aka gama ginaki, ni zaki gayawa ked'in sabuwa ce? Bari Takawan yazo seya gaya mun idan, ya gagara hakuri ai tunda kika Fara laulayi bayyana zatayi" K'afafuwanta ta kaiwa cafka

"Kimasa Uzuri Yake wannan sarauniya me adalci, idan har hakan ta kasance na b'oye Allah ya haneni leqa aljannar sa" Ajiyar zuciya ta sauke

"Na yarda dake 'yata, tashi kije gobe za'a masa shirinki hakanne ze kwantar da hankali na" godiya sosai tayi sannan tabar b'angaren fuskar nan d'auke da k'ayataccen murmushin samun nasarar manna mana voice recoder a Mundu'war gwal dake a wutsiyar k'afarta da zoben k'afar, ga samun nasarar Dasa guntuwar camera a gefen window parkor sanda zata fito, tana matuk'ar jin dad'in yin komai batare data aika kowa ba, amfanin d'aurawa a zoben qafa da munduwar qafa sabida ta rik'a jiwo kowace hira da Sarauniya hassy zatanayi da mutane, tana fatan tana zareshi idan zatayi wanka sabida ruwa yana tab'awa akwai damuwa...

Kai tsaye B'angaren Gimbiyar Rusau ta nufa tana sanya k'ayataccen murmushi a fuskarta, se wani mulki takeji yana fizgarta da sarauta sekace jinin sarautar ce...

Kome zatajeyi cen Allah masni.

Kumun uzuri yau nayi kad'an banci kaza ba......

Mom Nu'aiym.

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz