**********
   Jiya Ameena bata samu damar komawa gun meenal ba, sabida hidimar dayasha kanta, se yaune tun safe ta shirya komai na abincin data mata alqawari, sannan ta zuba a basket babba ta kuma sanyasu a boot na motar Muhammad tsadaddiyar benz fara k'al data zama mallakinta yanzu....kai tsaye school tanufa seda tagama lecture d'inta na 8 to 10 sannan ta juya zuwa asibitin....yau sanye take da atamfa fara k'al me zanen pink da blue ajiki, tayi mata d'inkin riga da skirt ba k'aramin kyau tayi ba, se tashin k'amshin turarenta takeyi na arab al oud da kuma big gurl is hia d'inta da suka gauraya suka bada launin na daban, jiyan kuma mom tamusu turaren kayan sawa a cikin wardrob nasu wanda aka kwana biyu ba'a samu turaren ba se yanzu....Ameena batada jiki sam, sedai tanata tarin dukiyar fulani da shape madaidaici, bazamuce tanata heeps na wuce wuri ba kokuma mazaunan ta sunada girman shahara ba, sedai komai na jikinta daidai ne da jikin nata d'an d'agwas, fara ce sol tana kuma da yalwar gashin kai harma dana gira da kuma na ido, idanuwanta sam basuda girma sekace wacce ta had'a zuri'a da 'yan china, cat eyes ne da ita masu tsawo dakuma wani lank'wasa ata k'arshen su, sedai kam sunada kyau daidai gwargwado, idan hanci yanawa mutum yawa toko tabbas yaso yawa Ameenan yawan sabida tsinin sa harya sakko ya zarce kusurwowin hancinta, bakinta d'an mitssli ne sedai yana  d'auke ne da kauraran lips dasuke zagaye dashi masu duhu kad'an, kaurinsu bewa fuskar muniba sabida tanada fad'i da kuma tsawo, hab'arta me tsawo sekace gidansu d'aya da abida muhammad....tanada tsayi sosai dakuma fara'a. Kai tsaye d'akin ta nufa d'auke da baske d'inta a hannu tana tafiyar ta sekace wacce k'wai yafashewa aciki tamkar batason yin tafiyar ma, da sallamar ta ta shiga cikin d'akin inda ta tadda wata baiwa  da kuma TAKAWa sunata fama da Meenal amma tak'i taci abinci wai ita sena mom, ran takawa a b'ace yake kasancewar tun jiya yarinyar ke kukan mom d'inta kuma tak'i taci wani abin, ido ya k'ura mata cikeda takaici hartazo ta durk'usa ta gaidashi,hannayensa duka biyu suna cikin aljihunsa sanda yace cikeda k'asaita

"Bakida Alk'awari ko kad'an, idan da kinsan bazaki kawo mata abincin ba mesa kikace zaki kawo, kin jawo yarinyana ta wuni ta kuma kwana da yunwa, gashinan yanzu harta soma ganin jiri wannan wane irin haline na k'ananun mutane, dama talakawa haka suke ne?" D'agowa tayi ta kallesa cikin jin zafin kalaman sa amma bata nuna masa ba se cewa tayi

"Bansan da cewar za'ayi rabon gadon tsohon mijina  daya rasu ba, jiyan na shirya inzo aka kirani, kuma se zaman yaja lokaci, kuma da muka dawo se nayi bak'i, daninada number wayanka dana kiraka na sanar maka ina me neman afuwa" shiru yae jin cewar mijinta mutuwa yae, ya gagara furta wata kalma

"Ayyah sannu Allah yajik'ansa ya masa gafara" Sadda kanta tai a k'asa tace

"Ameen ya rabbul Alameen" bece komai ba tayi kan Meenal

"Small meenal mesa zaki baiwa kanki azaba akan momy batazo ba? Ehn kiyi hakuri wlhy kina raina, badason raina nayi haka ba, kinji" Zama tayi ta zuzzuba mata ta tasheta a zaune ta bata abincin ta dad'e tana cin abincin har sanda ta kammala kuwa yana nan tsaye hannayensa a aljihun sa, kallon Baiwar yae yace da muryar sa da batada maraba data mata yace

"Kici abincin nan yanzun nan, dukansu kiyi testing komai" zubewa tayi dukda dama a zaune take

"Angama ranka ya dad'e TAKAWA" nan take ta soma bubbud'ewa tana ci, seda taci komai sannan yaja yaci gaba da tsayuwar sa, mamaki ya kama Ameenan, wanda itama seta nemi plate ta zuzzuba komai ta zauna taci sosai tasha komai data kawo sannan ta matsa ta kwanta a gadon tare da Meenal ta furta

"My meenal tunda mun k'oshi semuyi bacci ko?" Murmushi yarinyar tayi tace

"Mom please karki gudu idan ina bacci kinji" murmushi tayi

"Ban isa naje ko inaba my meenal sweery, yau ina nan anan zan wuni" murmushi tai

"Anna anan zaki kwana ko mom?" Rik'o hannunta me lafiyan tae

"My meenal nikaina daddyna zemun fad'a idan na kwana a waje, baza'a barni ba, amma kullum da safe zanna rik'a zuwar miki kinji" shiru yarinyar tai kawai batace komai ba, haka bacci ya suresu susu biyu abinda ya baiwa TAKAWA damar barin d'akin, tun jiya Talented ke kiransa amma  baya d'agawa yanaso ya kirata yaji game da wannan yarinyar.

**********

    Tana nan wurin Meenal har me martaba yazo shida wata mata da mutane sunkai biyar dabatasan kosu waye ba, sune ma suka tashe ta a baccin, sun gaisa sosai inda suke tambayar yaya jikin meenal akace da sauk'i anan taga wasu mata biyu masu tsananin kamanni dasu Meenal, tamkar an tsaga kara kuma TAKAWAN ma banbancin sa dasu d'aya ne shine zamtowarsu mata yana namiji, suna fita suka nufi masaukin su....waninenya d'aga waya yakira wani

"Garke akwai wata yarinyar dake bibiyar rayuwar su Meenal ba babansu, idan an samo bayanai akanta wanda ba'a yarda dashiba, me nuni da shirinta na b'ata mana aiki ku kasheta, kai kuma kashetan kafin gobe" yana gama fad'ar hakan yayi bayani akan inda yake saka ran abarta ya kashe wayar, ya kalli macen dake kusa dashi yace

"Bazamuyi sakacin da za'a lalata mana aiki ba, nace a kashe banza, bazamu bari wata mace ta rab'i wannan family d'in ba, Hidar kuma an sanar mana shishi kad'ai ake bari agida se fadawan sa, lallai na sanar wa Garke karya wuce gobe" murmushi macen tayi

"Aikinka yana kyau Me gamau, kana burgeni" haka suka gama tattaunawa sosai kansu shiga wata sabgar.

*********
    Sosai TAKAWA ya zuciya da bayanan da Talented nusy ta kawo masa gameda wannan yarinyar, kenan  zarginsa gaskia ne, lallai zata shiga uku kuwa a hannun sa, seta banbance tsakanin aya da kuma tsakuwa!!!

Mom Nu'aiym

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now