"Mommy shine bakizo ba se yau" da wata hausarsa da tukunna bata k'arisa nuna ba, da alama ya jima be iya magana ba...hankalinta ya dawo mata jikinta ta waigo ta kallesa setaji wani tausayinsa ya mamayeta lokaci d'aya takai masa runguma itama

"Kayi hakuri my Hidar nashiga wata hidimar ne ta daban kaji"  lafewa yae ajikinta ta soma shafa sumar kansa a hankali tana lumshe idonta

"Mom dad d'ina yace wai kin karya alk'awari ba kyau" d'ago dashi tai suka kalli juna ta furta"

"Kayi hakuri my Hidar, dalilin dayasa banzoba babba ne, kuma da ace ina lamban wayan daddynka aidana kirasa a waya kaga base kunyita jirana ba" jinjina kanshi yae

"Ina Ameena?" D'an tabare fuska yae

"Adda meenal batada lafiya fa, tanacen asibiti naga an d'aure ta" Da sauri ta mik'ar dashi zaune

"Menene ya samu Meenal d'in?  Waye kuma ya kaita asibitin, yanzu ina daddyn ku yake?"

"Motane ya kad'eta damukazo nemanki anan, tana nan tanata nemanki tafita wajen gate shine mota ya kad'e ta, daddyna yace laifin kine ai" cikeda rud'u ta mik'e tsaye

"Yanzu to ina daddyn ka?" Da hannu ya nuna mata shi, yayi tsaye ya zura hannayensa duka biyu a aljihunsa yana kallon su, fuskar nan babu annuri ko kad'an, jikinta amace taja hannun Haidar zuwa wurin sa.....acikkn farin gilashin dake idansa take hango manya manyan idansa ....ya kad'a yayi jajir da alama yana cikin damuwa sosai, lokaci d'aya wani shakkar sa ya mata dirar mikiya, a raunane ta furta

"Sannu Daddyn Meenal ina wuni?" Yafi dak'ik'u talatin be bata amsa ba har seda ta sare ta kuma shak'a sosai sannan yace

"Lapia" acikin wata murya da bata tab'a jin namiji da irin taba" seda ta tattaro courage d'inta sannan tace

"Dama Hidar yake gayamun wai mota ya kad'e Addansa, shine nakeso dan Allah ko zamuje na dubata?" Zare gilashin idan sa yai

"Ke dawa?" Ya wurgo mata wannan tambayar acikin muryarsa me kamada muryan wani sarki

"Dama ina nufin ko zaka kaini gunta ne dan Allah?"  Juyawa kurun yae ya soma tafiya batare daya bata ansa ba, har yayi nisa yakuma tsaya ya waigo

"Ya dai? Ba gun Meenal kikace na kaiki ba?" Murmushin yak'e ta k'ak'alo sannan tabi bayansa zuwa wurin parking lot d'in, sauri ta k'ara taje ta bud'e motanta ta tarkato wayoyinta biyu data bari da kuma jakarta sannan ta dawo bayansu....fadawane sunkai susu goma sha biyu ga wasu Excort kuma sanye da bak'ak'en suit susu hud'u, gani tai ana ta zubewa ana aika masa gaisuwa amma ko gezau beba bare su saka ran ze amsa, tsaye tai kaman wata statue tana kallon ikon Allah wannan kuma wanene....hankalinta ne ya kaita gun masu gayarda Hidar

"An gaisheda prince Hidar d'an sarki jikan sarki, gaban salama bayanka salama" Yana tsaye shima yayi biris tamkar yanda mahaifin sa yae....cikeda isa da k'asaita ya furta

"Zan koma" haka suka wage murfin motar yashige a gidan baya shida Hidar, kasa koda motsi Meenal tae harseda yawa wani bafade magana akan tashigo sannan ta tako zuwa d'ayan b'arin ta shige ta zauna aka mayar da murfin motar aka rufe d'an satar kallonsa tai tana mamakin inda shegen kaud'inta ya kawota, yasha mur tamkar be tab'a dariya ko bema santa ba

"Daddyna Mom tace wai nayi hakuri hidima ne ya mata yawa kuma batada Number wayaka datace a gayamun, ka dena yiwa fuskar ka haka 😡😡, ya nuna da fuskar sa, kanawa mom fushi kaji" murmushi zancen yaron ya sanya shiyi ita kuma seta d'auke kanta d'ayan b'arin ta basar

"To Haidar na dena shikenan?" Murmushi yaron yae shima amma be kuma magana ba, har suka isa National hospital dake abuja....suka fito daga cikin motar sesukayi cirko cirko kasancewar uban gayyar be fito ba har wannan lokacin, sunyi mintuna kanya zuro k'afarsa d'aya itama ta jira 20 seconds kan 'yar uwarta ta fito, yayinda fitowar gangar jikinsa gaba d'aya suka d'auki wasu seconds ashirin lafiyayyu, tsayuwar sama bayan yayi seda tafiyarsa tajira ayita na wasu daqiqu ashirin, wani irin takaici ne ya tarnak'e Meenal, da badan sanadin tane 'yar sa ta shiga halin datake cikiba daba abinda ze hanata juyawa ta nemi adaidaita zuwa inda dare mata ba, haka suka d'unguma itama dake mace tafishi cira k'afar ta.

  Da gudunta tayi kan yarinyar dukda kasancewar ta tarar da d'akin a cike danqam, kana ganin mutanen dake zaune a wurin zaka tabbatar wa kanka jinine na sarauta kodan yanayin shigar su

"Nashiga uku na, Ameena meya sameki haka?" Hankalinta yakai k'ololuwa wurin tashi ganin hannun yarinyar a ninke ga bandage har a kanta, bata fatan kyakyawar fuskar Ameena ta sauya ta dalilinta.....kuka wiwiw ta saka yayinda ilahirin d'akin yae tsit ita kad'ai ake saurare Meenal kamma baccinta takeyi abinta dukda yake kallo d'aya zaka mata ka gano tanajikin rad'ad'in ciwo, Hidar ne yazo ya rik'e hannunta

"Mom plss ki dena kuka, Adda Amal fa taji sauqi, kuma granny tace muriqa yi mata adu'a" Share hawayenta tae ta rik'o Hidar d'in amma bata dena zubar hawaye ba, seda tai kusan minti biyar sannan ta baiwa kanta hak'uri, Koda ta d'ago kanta ilahirin mutanen dake d'akin sun zubo mata ido ciki kuwa hadda Daddyn Hidar....ganin wani babban  mutum sanye da uban rawani yasha nad'i ga kayan nan na sarauta, ga kuma babbar mace a gefensa zaune itama cike da shiga ta alfarma ya bata daman zubewa a k'asa  ta gaidasu cikin girmamawa, Hannu kawai me rawanin ya d'aga mata yayinda macen dattijuwa tace

"Sannu 'yarnan, dama kece Momyn su Hidar?" Murmushi ta k'ak'alo tana share hawayenta ta gyad'a mata kai alamar E itace, murmushi tae

"Ki dena kuka kiwa Meenal adu'a, inshaa Allah zataji sauqi, karayane a hannu kanta kuma ata bayane ya fashe kuma anyi nasaran yin d'inki ma, abinda ake shirin warewa zuwa gobe ma, hannun ma ana ganin sauqi Alhamdulillah ki dena damuwa kinji 'yata" jinjina kanta kurun tai batai magana ba, gyaran murya wannan dattijon yai yace

"Adena damuwa, ayi hakuri ana kuma adu'a inshaa Allah matar ciki zata samu sauk'i da yardar Allah"  Wani irin kunyan tsohon ne ya mamaye ta, ta sadda kanta k'asa kafin kuma ta k'ara komawa ta k'urawa Meenal ido, adu'a samun lafiya sosai ta mata sannan ta durk'usa tamusu sallama akan se washe gari zata dawo in Allah yaso..... Bazata juri wulak'ancin  wannan man d'in ba dan yana jinin sarauta seyaketa wulak'an ci? Akarin me,,,,, adaidaita taje ta hau tayi tafiyarta batare data tsaya neman saba ma.

***************
     Se yau zulfa takira Ameena, tasha mita kuwa, acikin wayar take gaya mata komai, atare sukasha kukansu

"Amma meenal ke a haka zaki auri usif d'in? Bakya gudun abinda zeje yazo, damuwa bazata miki yawa ba kuwa, tunda ke kinyi niyyan cika wasiyan sa kuma jininsa yak'i baseki hak'ura meenal?" Nisawa tayi

"Tunda nake da Yaa muhammad ban tab'a aikata abinda yake so ba, last wish nashi kam sena cika, a k'auyuka uku yanzu haka an gina rijiyoyi guda uku, kuma masallatai uku zan yi yanda ze samu lada me tarin yawa, kuma duk a k'auyuka zan yisu, auren yusuf kuwa koda ze kasheni se idan na mutu kan auren amma sena aure shi, wlhy ina tsananin kewar muhammad zulpha, ki k'aramun k'warin gwiwa kawai" nisawa ta qarayi

"Allah yasa hakanne mafi alheri"

Godiya ta mata sukayi sallama.

**********
    Wayarta data manta yake jujjuyawa, yazo yayi dogon bincike akan yarinya amma shiga hurumine farawa takan wayanta, ina ze ganta to? Wane irin saunancine mantuwa da waya a mota haka kawai? Tunda tace zata dawo gobe ze bayar a bata......

Mom Nu'aiym

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt