Acikin akwatin bankina na b'oyayyen acc d'ina dana bud'a  na adane  kud'ad'e masu yawan gaske fiye da rabin dukiyata ne wanda ni muhammad na mallaka miki su acikin sirri, akwai komai nawa  awurin Aminina sharif kuma nagaya masa da lauyana zakuje ki cire, acikin dukiyar dana mallaka miki ba acikin gado naba ina roqon alfarma ki gidanmun rijiya da masallaci ladan yake zuwamun ko bayan bana nan idan Allah ya baki iko ga number sharif nan koda yake ko baki nemeshiba shize nemeki ***********.

Banida rayuwata a hannuna kuma bansan gaibuba amma dai ina barmiki wannan wasiyyar ne sabida banida tabbacin zankai safiya! Ki taimaka ki cikasamun alqawarina na auren yusuf dan Allah my meenal..... Ko daure ki gidan rijiyar nan da masalallaci.

Abu na k'arshe kuma adu'a ina rok'on alfarmar acikin lokutan dasuka rage miki na rayuwa karki manta ni, ki sakani acikin adu'oin ki don nemamun rahamar Allah kinga fa my meenal banida magaji, banida d'a banida jika babu me tunawa dani dagake se mahaifana da 'yan uwana....ki rik'e koyarwar musulunci meenal banason yanayin shigarki ina jiyemiki lahirarki a sassautawa duniya ayi sirki da neman lahira....

*Ina sanki Ameena!! Ina miki son so fiye da tunaninki, aduk fad'in duniyar nan banda iyayena babu wanda nakeso sama dake...inajin tsoron mutuwa, idan na kutu ki sani na tagine dan amsa kiran mahaliccina amma ina cike dason k'arin lokaci don bauta masa in kuma rayu dake....hakance tsarin rayuwata amma ina tsananin san rayuwa ta ki riqa mun adu'a....

*Ki auri yusuf my meenal, amma idan hakan yana daga cikin tsarin Allah.....karkiyi jayyya da zab'in Allah idan har kikaga babu alkhairi aciki... Ki hakura..karki d'auki wasiyya matsayin dole zab'in Allah shine daidai.

Ma assalam ina miki fata Alheri"

😭😭😭😭😭 koda ta gama karanta wannan dakardar tayi kuka mara iyaka ranar a zaune ta kwana, tana kallon yanda rubutun yake kana gani kasan yana cikin azaba sanda yake rubutun.....

*****************
   *Bayan meenal ta gama takaba*

Tattarewa tai ta koma gidansu, amma abun nacinta nason tawa yusuf maganar amma ba fuska, mahaifinta ta sama ta gaya mai komai gameda wasiyyar da muhammad ya bari nason ta auri yusuf!!! Mahaifinta kuma besha mamaki ba ya nemi mahaifin marigayin kai tsaye suka tari yusuf da zancen yayi musu kam!!! Yasha musu amma mahaifinsa yaja layin tsinuwa akan baze bari abinda d'an uwansa ya buk'ata d'aya ba a ce baza'a masa dole ya hakura

Abubuwa biyune suka tashi hankalin yusuf yace bayason auren meenal, na farko dai  yagama shirin aurensa da budurwarsa maryam sun gama d'inkewa....yana kuma masifan santa, na biyu kuma ya tsani meenal, yanajiyo sanda take cewa idan akan tace batasan yayansa yake cewa ze mutu ta janye, dama kenan cewa take batasan shi kanta tsaye, da wannan ya k'udiri niyyan wulaqanta mata rayuwa dama ga yusuf da shegen zafi ba kad'an ba.

   Kallon kallo suke da ita tunda yazo, sosai tsoron yaa yusuf ya d'arsu a ranta tunba yauba shi dama baya wasa da yara, kuma sam shi baya zuwa koda gidan sune, tsaki yaja yana wurga mata mugun kallo yace

"Mayya wai meye haka? Kallon na meye?  Kin cinye mun yayana ni kuma yanzu zaki cinyeni ne, wlhy nafi k'arfin ki kurwata kur" Nisawa tae

"Yaa yusuf to kuma duk me ya janyo wannan maganar?" Ta tambaya tana langwab'e kai

"Wlhy na tsaneki, banza wazakiwa karuwanci anan? Kin gama kashemun d'an uwana ni kuma kike cewa zaki aureni, wlhy sekinsha  azaba a hannu na, inada budurwata kin kawo zancen wasiyya jahila kawai" kallon mamaki take binsa dashi meya kawo zancen kisa, ta k'udirta a ranta kome zeyi seta cikawa muhammad burinsa, tunawa tae da wata magana da muhammad ya tab'a yi mata

"Ki dena furtamun kalmar tsana kanki tsaye my meenal, ba kyau ranar dukda wani ya gaya miki bazakiji dad'i ba zakuma ki gane abinda nake nufi, koda mak'iyinka bakaso yace ya tsaneka bare kuma abinda kakeso" Runtse idanta tai ta bud'esu a hankali, ta gane nufinsa taji zafin kalaman yusuf fiyeda tunanin sa, koda ze kasheta kuwa seta cikawa muhammad burinsa na auren yusuf din

"Kai hakuri yaa yusuf" mik'ewa yae yana banbami

"Wlhy senaci qaniyar ki idan kika k'ara gigin kiran wayana yanda kikai d'azu, bana buk'atar hakan shashasha kawai"  sororo tai tana kallonsa harya b'acewa ganinta, takula yanzu ta fara ganin abubuwa indai wannan yusuf d'inne to akwai matsala, kumafa kome ze mata se dole  ta aure san.....figar motarta tai zuwa Island park tana cikin tsananin damuwa, Ba kad'an ba take k'aunar muhammad d'inta yanzu kam, shikam be tab'a zaginta ba baya son b'acin ranta ko kad'an, betaba yi mata koda tsawaba, kome zata ce masa baya damuwa, yau itace ake zagi, zagin ma na wulaqanci amma ta gagara yin komai, gefe d'aya ta samu inda babu hayaniya ta zauna tanata rizgar uban kuka me tsuma zuciya.......kaman daga sama tajiyo muryan yarinya ga kuma hannunta a kan nata tana jijjigata

"Mommy meyasa kike kaman daddy na ne ehm? Kullum shima seyazo nan ya dinga kuka kuma idan na rarrashesa baya denawa, dan Allah ku dena kuka kunji, kinga Hidar ma sabida kuna keda daddyna se kuka yake" D'agowa tai ta kalli yarinyar bazata wuce shekaru bakwai ba se yaron dake binta iyakacin sa hud'u yanata kuka, ita d'inma yarinyar k'walla ya taru a idonta k'arfin hali kurin takeyi kamo hannayensu tai dukansu  tace

"Mesa daddy yake kuka, ni kinga cikina ne yake mun ciwo, Haidar meya same ka" jan hannunta ya somayi

"Kizo muje kice daddyn mu yae hakuri ya dena kuka, mommyn mu mukazo nema kuma bamu ganta ba, shine yake kuka, kozaki nemamun ita ne" bata gane kalaman yaron na, amma bata mik'e ba, sema rumgumesu da tai dama hakan take buk'ata ta dinga rizgar uban kuka, suma yaran kuka suka saka sunfi 5mns sunayi sedaga bayane sukayi shiru dukkansu,ta kalli babbar tace

"Yaya sunanki?"

"Sunana Ameena" yarinyar ta bata amsa kai tsaye.... Jinjina kanta tai

"Mesa daddy yake kuka ne?" Ta tambaye ta

"Mommy ce ta b'ata tun kwanan baya fa, shine bama ganin ta, kuma haidar seyace azonan a duba masa ita tunda nanne muke yawan zuwa, idan ya matsa se daddy ya kawomu idan munzo bamu ganta ba sekuma daddy da haidar su dinga kuka" bata gane komai ba akan bayaninsu amma a hakan seta basu hakuri akan zasu ganta  ne wataran.....

Mahaifinsu kuwa tsaye yake k'ik'am yana kallom su a tare da ita, har sukai sallama yana kallon su, Hidar harya juya ta rik'oshi ta rungumesa a durk'ushen datake sannan ta manna masa sumba a kuncinsa......wani memory ya flashing wa daddynsu Ameena wanda seda ya runtse idansa na mintuna kannan ya bud'esu.... Wayam babu ita ba labarinta sesu hidar dake d'aga hannu alamar bye bye da alama ta b'ullee....gun yaransa yazo be damu da sanin wacece sukaje gunta ba, damuwar dake zuciyar sa ma ta ishesa.....

*Masu karatu yanzu muka fara wasan fa😍😍😍😍✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 anya meenal zata k'ara samun farin ciki kuwa?*

Mom Nu'aiym

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...Where stories live. Discover now