sakamako 10

448 26 0
                                    

     
  10
jarabawarsu husna ta kammala makaranta tagabato saura sati daya agama registration, gashi ba kudi kuma tasan bama zatafarama lado maganarba Don ubanta zeci takarasa yadda zatayi,tayanke shawarar zata karbo kudinta Inda take wankau did da lokacin karbar beyiba.

Ranar husna nagidan su farida takecema farida,

Farida kinyi reg din waec
Aa banyi ba Amma yaya Abdul zayimin insha Allah gobe
To Allah y baki saa, nide nafidda rai,
To sabodame
Kinde San babana baze biyaminba, bakuma Dan bedasuba,
Kai gaskiya banji dadiba naso ace tare zamuyi.....

Ashe duk maganar da sukeyi Abdul najinsu, yana balain tausayama husna gata mace, bakuma Dan babanta beda shiba.

Sai yamma lis sannan takoma gida

Washegari farida da ya Abdul suka tafi reg din exams din, kome yayiwa farida saida yayi ma husna,sungama suka koma gida

Da yamma yayi ma husna sallama tafito,

Au ya Abdul dama Kaine ke nemana

Nine husna ya gidan tace lpia klau ya Abdul, takardun ya mika mata yace gashi next week shirya kufara zuwa exams keda farida

Budewa tayi Dan ita bata fahimci Abinda Yake cewaba, laaaa yaya farida ce tagyama bazanyi exams bako

Aa baitabace

To ya akai kasanai, nagode sosai yaya Allah y saka alkhairi, Amin bakomai husna.

Ki gaisheda umma, to zataji

Tana shiga tanunama umma, har gida umma taje tayi godia.

Sati na zagayowa suka fara rubutu exams, Kullum tare suke zuwa suke dawowa.

Wata guda sukayi cirsuna rubuta exams din ranar karshe geography suka rubuta, sunfito suna tafi suna fira,

Farida tace Ana fara jamb zanyi incike BUK

Husna tace aurefa

To zanyi in Allah ya kawo miji Amma ni sai nayi jamia fa

To nigani baga makarantarba bakuma ga auren ba Dan ko saurayi bandashi,

Lalle kigyama Karamin yaro, duk wannan kyan zakice bakida saurayi

To inma Ana sona kowa tsoro yakeji kinde San halin babana ai

Haka suka dinga fira har suka kaigida kowa yawuce gidan su

Tana shiga taga mamanta na wanke wanke takarba tagama  sannan tashiga ciki,

Tace umma mungama jarabawa fa, to angama barka Allah y bada saa ya kuma taimaka Amin umma .

Kullum suna gida wata rana tare suke zuwa gidan da take aiki,tana  tayata sunyi tare.

Watarana daddare harsun kwanta saiga lado ya bankado kofa yashigo dakin, mikewa indo tayi da sauri,

Ke Ina abincina,
Yanafa kitchen naajema
Hutattacen abincin kikeso naci eh
Haba lado wallahi nagaji da wannan cin kashi da kake min, kamaida ni kamar wata baiwa nifa ba baiwa bace,
Batai auneba taji ya sauke mata Mari mai shegen zafi,nikikefadama wannan maganganun, zanga ubanda ze tsaya miki,
Lado ubana na kabari karka sake zaginshi,
Fixgota yayi daga kan gadon ya kaimata naushi a ciki yayi kwallo data, sai jibgarta yake ba kakkautawa, dafe ciki tayi tana wani irin kuka
Lado bai bar jibgarta taba saida yaga tadena motsi,sannan ya fice ya yayi gaba
Husna ta sakko atsorace ta jijjiga mamanta Amma shiru ko motsibatayi,kuka tafara tana jijjigata amma bata tashiba, da gudu tazo gun lado tana baba mama tamutu, kazo gani

Kedallah demin ihu karki taramin jamaa dare ne, ranar husna bata iya bacci ba Banda kuka ba abinda takeyi, dasafe yadauketa suka wuce can gidan su.

Farida da husna Banda kuka babu Abinda sukeyi, shima lado kuka yakeyi shanene,  Amma kukan munafuncinne  suna gani aka dauketa aka wuce da ita gidanta na gaskiya.

Har suma husna tayi, bata taba tunanin zaluncin lado yakai hakaba, sai yau, akwanaki ukkun nan ko magana batayi bata cin abinci, sai kuka kawai,

Shima lado haka, anata bashi hakuri yana sunbatu, husna kallan Shi kawai take tana mamakin hali irinna lado.

Ranar da aka gama sadakar ukku, iya tace tabi babanta sakoma gida tukun amma taki, da kyar akasamu tabishi.

Suna zuwa yace ke koda wasa kika sake kika fada nine na kashe Indo wallahi kema saina kasheki, kina jina, ta Gyada masa kai

Tindasuka koma yaciga da harkokinsa, ko ganinsa batayi,Dan lokacinda zefita bata tashiba, lokacinda zedawo kuma ta kwanta.

Kusan satinguda haka suka, ranar tashirya ta wuce gidan kawunta wato yayan mamanta.......

Sorry nayi skipping nomba 9 bansaba manage it like dat

Don't forget to vote and comment

SAKAMAKO.......THE OUTCOMEWhere stories live. Discover now