NADAMAR.. 13

233 15 2
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

     *NADAMAR DA NA YI*

           _WRITTEN BY_
            *MRS OMAR*

               _STORY BY_
      *HAUWA M. JABO*

           _DEDICATED TO_
            *BEEBAH LUV*

     _Dis page is for you Zahra darma ina godiya da comment naki thanks_

            _PAGE 13_

*WASHE GARI*

Idan kaga Fatima baka taɓa ɗauka ita ce, duk da dama ita mai ƙyau ce amma Pendo Ummi ta gƴaramata skin ɗinta har wani sheki yake dan ƙyau,   fuskar nan tata ta koma kamar ta *Zaara Malik Khan* ko ke mace kika ganta kinsan Fatima matar manya ce.
Yau ta kama ranar wa'azi inda aka gaiyato *Malama Jiddah Aliyu* tana ɗaya daga cikin manya_manyan kawayen   Mom da take ji dasu bayan dimbin muta nan da aka gaiyata sun baiyana,
Pendo Ummi ta fito da amarya, ko ƙaramin yaro ya kalli fuskar Fatima yasan taci kuka amma mutane bazasu fahimci akwai wani abu ba zasuyi tunani ne kawai tana kukan rabuwa da iyayenta ne saboda ansan duk yarinyar da za'a rabata da iyayenta dole ta zama cikin wannan yana yin.
Pendo Ummi ta zaunar da Fatima dai_dai inda malama Jiddah Aliyu ke zaune itama ta samu waje ta zauna, a hankali malama Jiddah Aliyu ta fara buɗe wajan da addu'a kamar haka.

" _Bismillahin rahamanin rahim. Allaahumma salli alaa Muhammadin wa alaa aali Muhammadin kamaa sallaita alaa Ibraaheema wa alaa aali Ibraaheema innaka Hameedum Majeed Allaahumma baarik alaa Muhammadin wa alaa aali Muhammadin kamaa baarakta alaa Ibraaheema wa alaa aali Ibraaheema Innaka Hameedun Majeed._"

Tana kai karshe ta ɗaga hannunta ta shafa muta nen wajan suka mara mata baya wajan shafa wa nan fa taci gaba da wa'azi mai shiga jiki kamar haka.

"To Amarya Fatima muna godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana zaki zama matar Faruok da yardar Allah.
To amarya,shi dai aure ibada ne domin raya sunnar manzo ma'aki ne ki sani duk wanda yayi wasa da aure bashi ba rahamar ubangiji, aure ibada ne Fatima ki zama mai biyayya ga mijinki ki gujewa duk wani ɓacin ransa ki zama mace ta gari mai koyi da halaye irin na Nana Fatimatu uwar mumunai.
Idan har kikayi haka ina tabbatar maki Fatima zaki zama sarauniyar mata a wajan mijinki. sometimes zakiji wasu na faɗi ai wance ta mallake mijinta, to wallahi ba komi kesa haka ba sai biyayya ga mijinki.
Fatima kiyi biyayya ga mijinki domin aljannanki tana karkashen tafikan ƙafarshi idan ya ɗaga zaki shiga, kada ki yarda mijinki ya zama mai yawan fushi dake a koda yaushe ki zama mace mai saka mijinta cikin farin ciki.
Akwai wani abu da mata basu sani ba yau zan faɗa maku har yanzu akwai mata da da yawa suna kuskure wajan hakkin mazajensu, bance duka ba amma na ce wasu matan na miji kamar jariri ne yanda kika raineshi to ta haka zai tashi duk yanda kika koyar dashi idan kin koyar dashi sonki to wallahi duk inda yaje sonki na cikin zuciyar shi idan kuma kiyayarki kika kota mashi to fa duk inda yaje zaiji baya marmarin dawo gidan dan gudun bala'in daya bari.
Mata muyi biyayya ga mazajanmu Fatima ki sani aure ibada ne ki rike mijinki hannu biyu kada ki bari *SON ZUCIYA* ya kai ki da *SAI KINYI NADAMA* domin kuwa yan iya magana suka ce *MATAR MUTUM* kabarinsa ki sani yanzu Faruok shine *MASOYINKI NA HAR ABADA* saboda kin zaman to *KE DAYA CE* a cikin zuciyarshi. Idan har kika bashi zuciyarki haƙika zaki zama yar gata a wajan sauran matan duniya zaki zamo sarauniya a gidanki kina mulki yanda kike so, kada ki bari ki zama mai irin halin gimbiya Fiddausi a cikin *MAZA DA MULKI MATA DA TAKAMA* tayi mulki yanda take so daga baya kuma ta gane *NADAMAT DA TAYI* a baya, Fatima ki godewa Allah ba wani bare zaki aura ba balle ki dinga tunanin *MATSALAR DANGIN MIJI* ɗan uwanki ne Faruok.
Fatima wallahi kiji tsoran Allah ki guji fushin mijinki domin fushin sa babbar matsala ne a rayuwarki ba ke bama duk macen dake wajan nan ta guji fushin mijinta.
Akwai wasu matan idan sukayi faɗa da mijinsu mai makon su san yanda zasuyi su shawo kan mijinsu to wallahi mata da yauwa basu san yanda ake sauke miji daga fushi ba, wani namiji na fushi itama matar sai ta ɗauki fushi dashi daga nan sai a raba shinfiɗa to dan Allah ina amfani keke sama dashi ko shike sama dake?
Gaskiya wannan babbar matsala ce a tare damu wanda wallahi idan bamu gƴara ba to akwai matsala Allah yasa mu dace amin.
To Amarya da fatan duk kin ɗauki nasihar danayi maki Allah yasa ta amfanar da duk jama'ar dake wajan nan.
Naso yafi haka to lokaci ya kawo jiki zamu dakata a nan Allah ya bamu alkhari, Amarya kuma Fatima da angonta Faruok Allah ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a daiya ba.
Sallu anan nabi."

Tana kai karshe ta shafa.
Hak'ika ba amarya Fatima ba, da jama'ar wajan koni wannan wa'azi ya shiga zuciyata Allah yabamu ikon yin biyayya ga mazajenmu.

Bayan an gama su Pendo Ummi suka shiga bada littattafan *SIRRIN MIJINKI A TAFIN HANNUNKI* wanda *Princess Amrah* ta walla fa.
Babu wanda bai samu ba komi dangin Mom ne ke aiwatarwa dan kuwa Fatima babu wata ƙawarta data gaiyata su Hafsat ko da Aunty da Mom ɗinsu kamar su mutu sukeji babu wanda ya fito wajan hidimar, ita ko Mom ko a jikinta burinta kawai dai ƴarta tayi biyayya ga abinda suka zaɓa mata.
Direct ɗakinta ta nufa da gudu ta rufe ƙofa ta buɗe wani saban babin kuka haƙika duk wanda yaga Fatima dole ya tausaya mata tana cikin kukan ne phone ɗinta ya fara ringing a hankali ta kai dubanta ga screen ɗin wayarta sunan Musaddik taga yana yawo akai da sauri ta ɗaga kafin tayi magana taji yana faɗin.

"Fatima wayyo Allah zan mutu Fatima ki tausayawa rayuwata kiji tausayina Fatima zan mutu da sonki Fatima idan ba kizo ba nan da one hour Fatima zan rasa rayuwata Fatima ko kin daina sona ne? please Fatima help me atleast let me see u once again please"

Shiru tayi baka jin komi sai sautin saukar lumfashita na tasha kuka."

Please Fatima talk to me"

Cikin muryarta da ta dishe  tsabar kuka ta ce.

"Musaddik mezan ce maka ko kasan ni tawa rayuwar daf dake da salwanta, bansan inda zan saka kaina ba"
"Any way Fatima mubar wannan magana yanzu please kizo ki saman."
"Musaddik Dad ya hanani fita ko nan da ƙofar gida."
"Shikenan Fatima na fahimta yanzu baƙya sona duk kalamanki dama na yaudara ne ba damuwa."

Yana kai karshen maganar shi ya kashe wayarshi ido ta kurawa wayar kamar sakara yayinda hawaye sukaci gaba da aikin fita a fuskarta a hankali ta fara magana tana cewa.

"No Musaddik don't do dis to me.
Dole nazo na ganka i promise u no one can stop me from seeing uh my luv"

Da sauri ta tashi taja mayafinta ta fita saboda ta tabbatar jama'ar gidan duk suna ƙokarin yin sallah da sauri ta fita get ɗin gida yayin da masu gadi ma suna can wajan sallah.
Sauri take kamar zata tashi sama har Allah ya haɗata da mai adaidaita.
Tana zuwa ɗakin Musaddik tayi tsinke ƙwance ta samai da sauri ta isa wajansu ta fashi da kuka, da sauri ya tashi a sama ya fincikota jikinshi yana faɗin.

"Is ok Hubby yanzu kika tabbatar min da irin soyayyar da kike min"
"Musaddik na shiga ukku na,shi kenan yanzu lokaci ɗaya an ruguza mana mafarkinmu na kasancewa tare har abada?"

Hannu yasa ya kuma tallabota duk da ba ganni yake ba amma yana sanin inda hannuwansa ke zuwa.

"Fatima don't worry i will do something about it, mafita ɗaya ne Fatima ki amince mu gudu muje wani waje muyi aure.."
"What?"

Cikin firgicin maganar da yayi ta ce.

"No Musaddik i can't do dis to my family taya zan masu haka bayan irin tarbiyar da suka bani tsawon shekara nawa lokaci ɗaya na gujesu no I cant.."
"Dakata Fatima ya isa na fahimci inda kika dosa ce min kawai zakiyi kin fara son Faruok.
Ba komi Fatima na fahimta dama yaudarata kike babu komi kije abinki."

Take hawaye suka fara fita a idonshi, ya janyeta daga jikinshi ya koma kan katifa ya zauna yana mai zubar da hawaye.
Ciki tashin hankali Fatima ta isa gabanshi itama tana kuka tana faɗin

"No please Musaddik listen to me for a moment wallahi ina sonka duk lokacin da na yi tunanin bakai zan aura ba inajin kamar na kashe kaina Musaddik kaine farin ciki ruhina."

Ajiyar zuciya Musaddik ya sauke kafin ya cije lips ɗinshi yasa hannu ya kamota ya ɗan ƙwantar da ita saman ƙafarshi ya dan zame veil ɗin kanta yana shafa sumar kanta ya fara magana cikin muryar mai daɗin sauraro.

"Fatima ke tawa ce ni ɗaya shiyasa kikaji na ce maki mu gudu Fatima bazansa ido ba naga kina gidan wani bani ba.
Yanzu idan kika barni ina zansa kaina? kisani sonki a jinin jikina yake ki amince dani ki tuna alkawarin da mukayiwa juna. Please Fatima ki amince mugudu muje wani waje muyi aure na tabbatar kuɗin hannunki zasu ishemu rayuwa kinji ko?"

Kai ta ɗaga mashi hawaye sai fita suke a fuskakukinsu ....

*Please if this page has impressed uh I will love to c ur comments*

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now