NADAMAR.. 12

216 12 0
                                    

*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

      *NADAMAR DA NAYI*

           _WRITTEN BY_
         *MRS OMAR*

          _STORY BY_
    *HAUWA M. JABO*

          _DEDICATED TO_
            *BEEBAH LUV*


             _PAGE 12_

          ************

Captain Bilal ne ya turo ƙofa a hankali.
Kayan jikinshi mofti ne watau ( kayan gida ) dai_dai bakin gadon da Faruok ke ƙwance captain Bilal ya ƙarasa da sauri ya kai hannunshi jikin Major Faruok yaji kamar ana hura wuta a jikin nashi."

"Ya salam Major what is wrong?"

Cikin muryar ƙasa_ƙasa Major Faruok ya samu ya furta.

  "Wayyo Captain Bilal marana zan mut.."

Bai ida magana ba ya koma rike cikinshi yana juyi.
Kai Captain Bilal ya girgiza sannan ya dawo dai_dai bakin gadon ya zauna ya ɗaga kan Major Faruok saman ƙafarshi ya kura mashi manyan idanunshi cikin sanyin murya ya ce.

"Ina kaje har wannan matsala ta sake faruwa and  u know ur problem but baka kiyayyewa kasan kanada yawan sha'awa Mojar amma baka kiyaye lafiyarka why?"

Da ƙyar Major Faruok ya iya ɗago kai ya kalli Captain Bilal ya ce.

"Please Captain Bilal just forget about this,we will talk about everything later,
Please yanzu ka samu ka tsaida min ciwon nan wallahi ni kadai nasan wahalar da nakeji yanzu Hafsat kin.."
"What? Hafsat me tayi maka ba dai ita ta sakaka cikin wannan matsalar ba?"

Shiru Major Faruok yayi ya kasa ƙara magana kai Captain Bilal ya koma girgizawa sannan ya iya firta.

"Alright ina ka aje alluranka?"

Hannu ya ɗaga a hankali ya nuna mashi locker gefan gado da sauri Captain Bilal ya nufa wajan ya ɗauko kwalin alluran bai wani ɓata lokaci ba ya haɗa duk wadda ta kamata yayi mashi take guda biyu Captain Bilal yayi mashi.
Shi dama a cikin aikin soja a ɓangaran  medical yake, kusan cikin soja za'a samu electrician kafinta da dai sauransu...

★★★

K'wance take akan ƙafarsa yayin da yake shafa gashin kanta mai santsi idanunta a rufe suke da alama tana jin daɗin yanda yake shafa kan nata cikin muryarta mai daɗin sauraro kamar sarewa ta ɗago kanta ta kama fuskarshi, ta fara magana kamar tana cikin wani hali.

"Ya kai k'yakk'yawan basaraken dake mulkin fadar zuciyata
_nazo da littafin ƙauna dake rubuce da kalaman soyayyar ka, ka bud'e babin farko tareda haskawa dake hasken zuciyata domin bin kalaman cike mai ɗauke da  kaunarka_
kasani a fadar zuciyata kaine kake mulkinta banida kamar ka ina maka son da bana yiwa kaina saboda kaunar danake maka yasa nasa maka suna da larabci Ya Faruok hakika a baya naso na tafka babban kuskure dana rasaka da bansan inda zan saka rayuwata ba ashe kaine masoyina na gaskiya i love u Ya Faruok."

Jiyayi kawai ta jawoshi jikinta tana kiss nashi da sauri shima ya fincikota yaci gaba sa aika mata saƙoninshi iri_irin yana faɗin.

"Fatima are u sure yanzu kin amince dani wayyo Allah nagode maka fat.."

Dukan da Captain Bilal ya kai mashi ne ya farkar dashi daga mafarkin da yake ga pillow nan rike a hannunshi ya rikeshi kam.
Kai Captain Bilal ya girgiza yana mai cike da bakin ciki halin da abokin shi ke son saka kan shi.
"Haba Major what's wrong with u.
A kan mace kana so ka haukata kanka haba Faruok kaifa namijin duniya ne."

A hankali Faruok ya tashi zaune ya lumshe idonshi ya buɗe su ya sake murmushin takaici ya fara magana cikin muryar mararsa lafiya.

"Captain Bilal,hmm u will never understand me.
Ina tunanin dakai ka faɗa cikin halin da nake ciki tabbas da yanzu ka shiga wani yanayi, wallahi tunda kayi min allurar nan na samu barci nake mafarkin Fatima. Faruok wallahi idan ban mallaki Fatima ba rayuwa ta na dab da salwant..."
  "Ya salam Major what are u saying haba mazaje kada ka bada maza mana.
Amma Faruok me zai hana ka amince ka aure Hafsat."
  "What? Hafsat never! I Will never marry a useless woman like her. Captain,Hafsat? No"
  "Why?."

Kai Major Faruok ya girgiza ya cije lips ɗinshi ya ce.

"Tarbiyar Hafsat Captain Bilal sanin kanka ne bata dace dani ba a kullum ina addu'a Allah ya bani mata ta gari.
Bilal komin nayi tunanin na cire Fatima a raina sai naji na kara sonta, na tabbata Fatima ita ce zaɓin da naketa fatan Allah yayi min."

A hankali Captain Bilal ya ɗaga hannunshi ya dafa kafaɗar Faruok ya ce.

"Na yarda dakai Major Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen."

Captain Bilal har ya tashi sai kuma ya ce.

"Au Major wai kana nufin haka za'ayi hidimar bikin ba komi."

Murmushi yayi ya shafa sumar kanshi ya ce.

"Hmm Captain Bilal kenan ai hidimar bikin ana yinta ne  idan ma'auratan na cikin farin ciki da junansu.
Ni kam kaga namu auran za'ayi shine kawai."

Take fuskar Faruok ta sauya duk da dama fuskar tashi yau sai a slow.
Bilal yaga yanayin abokin nashi ya sauya dan haka sukayi ban ƙwana ya fita da sauri ya barshi..

«««««««««««««

_Washe gari_

Duk wata hanya da Fatima zatabi dan su haɗu da rabin ranta Musaddik ta kasa samu Dad ya hana ko nan da bakin get a barta ta fita.
Zaune take ta rasa mafita Mom ta turo ƙofa tana tare da wata mata mai ƙyau baza ta wuce shekarun Mom ba.
A hankali ta ɗaga kai tana kallonsu cikin girmamawa ta duka har ƙasa ta cewa matar.

"Pendo Ummi jam6an duna."
"Jam Fatima noi shomri?"
"Jam pendo."

Mom duk tana jinsu bata saka baki ba pendo Ummi ta samu gefan Fatima ta zauna tasa hannu ta kama na Fatima ta ce.

"Fatima duk Adda Shamsiya ta faɗa min komi har zuwa yanzu ta ce kina nan a kan bakanki na kin amincewa da auran Faruok anya idan kika bijirewa iyayenki kinyi masu adalci?"

Shiru Fatima tayi tana wasa da yatsanta.

"Fatima magana nake maki."

A hankali Fatima ta ɗago kai tana kallon pendo Ummi take idonta suka cika da kwalla.

"Kinga Fatima ba kuka na ce kiyi min ba.
Amma ya kamata kiyi tunani sosai ki gani inda iyayenki suka dosa."
"Hmm Ummi ai bazata taɓa fahimtarki ba saboda yarinyar nan yanda kika san ba Fulani suka haifeta ba."
"A'a Adda kada ki faɗi haka ki dan bamu waje insha Allah zata fahimta."

Mom bata tsaya ɓata amsa ba tayi waje abinta.
Pendo Ummi ta ɗago kan Fatima suna kallon juna ido cikin ido ta fara magana duk da Hausa.

"Fatima ki tausayawa mahaifiyarki kada kisa ta shiga cikin wani hali.
Wallahi Fatima Faruok shine mijin da ko wace mace ke fata ta mallaka, ya kike son wasa da damar da Allah ya baki ban ce maki Musaddik shima ba alkhairi bane amma ya kamata ki amshi zaɓin iyayenki dan kada daga baya kiyi dana sani."

Cikin muryar kuka Fatima ta ce.
"Pendo Ummi wallahi nayi duk yanda zanyi dan na cire soyayyar Musaddik a zuciyata amma na kasa.
Na tabbata ina dab da rasa rayuwat.."

Bata ida ba pendo Ummi tayi saurin rufe mata baki da hannu tana faɗin.

"Don't say so please."

Hawayen da Fatima ke makakewa ne suka zubo da sauri pendo Ummi tasa hannu tana goge mata.
Ta daɗe tana bata baki kafin daga baya ta ciro wasu abubuwa a cikin handbag ɗinta ta kama hannunta suka nufi toilet.
Bata bata lokaci ba ta shiga haɗa kayakin cikin ruwa iri daban_daban masu kamshin gaske ga garin lalle duk ta haɗa a ciki.
Sannan ta ce Fatima ta shiga cikin bathtub ta ƙwanta na wani lokaci bayan ta cire hayan jikinta Fatima na jin kunya pendo Ummi babu yanda zatayi haka ta amince da abinda ta faɗa mata tayi..

Kuyi hakuri naso page ɗin yafi haka, amma ina..

NADAMAR DA NAYIWhere stories live. Discover now