02: 1996

188 49 9
                                    

"Takan me zaka yi ta asarar kudi akan diya mace, bayan gidan wani zataje wataran. Gamu da diya maza a gabanmu ai su ya kamata su cigaba da karatun tunda su zasu riqe gidan wataran, ita kuwa Hadiza yanzu Allah ya sa albarka cikin secondary inda tayi". Jinjina kai Haji Modu yayi, bisa dukkan alamu maganar da me dakin sa tayi na tasiri akan shi.

"Yanzu in ta samu miji sai mu mata aure asirin ta a rufe. Koh ba haka ba Haji?". Be ansa ta ba ta cigaba da magana "Ai aure shine darajar diya mace. Shine kuma babban gatan da mu a matsayin mu na iyayen ta zamu iya mata"

"Hakane Yaburra" ya fadi yana murmushi itama Yaburra din murmushin take "Toh Khadi kin dai ji me mamanku ta ce, sai mu jinginar da zancen WAEC. In Allah ya kawo miji ayi aure koh?". Toh kawaii Hadiza tace Baba ya shafa kanta yana sa mata albarka a yaren su na kanuri. Bata miqe ba sai da Baba ya bar dakin tukun itama ta miqe zata futa taji Yaburra ta watso mata zagi a harshen kanuri. Bata tanka ba tayi wucewar ta zuwa dakin da take sharing ita da kanwar ta.

Kan katifa ta zube ta fara kuka mara sauti. A duniya ba abunda Hadiza ke matuqar son taga tayi kamar karatu, ta cika burin ta na zama architect dan ita sosai aikin da architects suke yi yike burge ta amma gashi Yaburra ta hana Baba ya biya mata kudin zana WAEC ta tafi makaranta. Ba da jimawa ba Hadiza ta ji an tabo ta koh da ta miqe yar uwar ta ta gani zaune gefen ta, ta dawo daga inda Yaburra ta aike ta.

"Me ya faru, ya kika kwanta kina kuka? Hanaki kudin Baba yayi?". Fusam ta tambaya dan dama tana sani da qudurin Hadiza na tambayar mahaifin su kudin zana jarabawar WAEC a ranar. Fada mata yadda suka yi da Baba akan furthering karatun ta tayi. Itama Fusam din hawaye ne suka fara sauka kan kumatun ta. "Ni dama na san ba mu da ranar barin azaban Yaburra. Bamu da rana da Hadiza".

Duka su biyun suka shiga rarrashin juna kamar yadda suka saba a kullum dan dama dole ne duk wayewar garin Allah sai sun zubda hawaye a gidan ubansu. Sai da suka sha kukansu har suka gaji tukun suka share hawayensu suka daina suka shiga hira.

Kanwar su ce Mairam ta shigo dakinsu ta watso kayan uniforms dinta da na kannen ta. "Yaburra tace ku wanke su yanzu sannan in sun bushe ku yi guga". Ta fadi ta ruga a guje ta fice ta bar su. Madadin hakan ya su baqin ciki, sai aka samu aqasin haka dan dadi sukayi ta ji sabida koh ba komi zasu samu su dauraye kayansu da ruwan sabulun wankin uniforms din yan uwansu.

"Rabona da wanke uniform tun ranar talata. Jiya sai da na sha bulala hannun labour prefect dinmu" Fusam ta fadi kan ta qara da "Allah nagode maka". Kusan shekaru biyu kenan ake haka Yaburra bata basu sabulun wanki bata basu detergent sai dai in Baba ya basu kudi su siya da shi, kuma kudin ma sai wanda ya basu a bayan idonta dan indai akan idon ta aka basu sai ta bi ta karbe tace suna yara me zasuyi da kudi baccin daidai da pad bata basu bayan ta san duka su biyun sun fara ganin baqon su na wata wata.

Da saurin su suka futo Hadiza na wanki, Fusam na doraya har suka gama wankin qannin su tukun suka wanke dirty clothes dinsu da ruwan sabulun. Suna gamawa suka koma ciki suka tararda yan uwansu na cin shinkafa jollof ya sha kayan hadi ga manyan manyan yanka nama a sama.

"Yan wankin uniforms da be kai ya kawo ba shine tun dazu kun tsaya kuna ta jan jiki gashi har an cinye abincin baku samu ba. Wanda ya rage wanda Hamza zai ci ne anjima kan a gama na dare. Sai kuyi haquri ku jira daren". Toh kawai suka fadi suka wuce dakinsu dan wannan ba shine karo na farko da ake girki a gidan ubansu ba basa samu baccin har agolan gidan suna samu su ci su qoshi har a ije musu na anjima sai su asalin yaran gida basa samu. Yamma na yi aka kuma taso su aikin tuwon dare. Tunda suka fara aikin Yaburra ta sama kujera ta zauna bakin kitchen din don wai kar suyi girkin su deba abinci su boye. Daidai da naman da za a saka cikin miya sai da ta kirga wai dan kar su ci. Hadiza ce ta hada lafiyyar miyar kubewa ita kuma Fusam ta tuqa tuwon shinkafa. Kasancewar kowana yaro nada warmer da ake saka masa abinci idan aka gama ya sa ana gama abincin baccin sun kwashe komi sun saka a babbar warmer suka kawo gaban Yaburra kan suka wuce suka kwaso kulolin sauran yan uwansu suka ije gabanta. Abincin Baba ta fara serving Fusam ta dauka ta wuce parlorn sa da kayan abincin kan Yaburra ta bi kulolin yaranta su shidda ta zubawa kowa tuwo enough wanda zai ishe su har ma su ci su rage. Da tazo kan warmer dinsu Hadiza dan dama cikin warmer daya su ake hada musu abinci tare da Fusam. Warmer dinma duk ya fatattake ya futa daga hayyacin sa. Tana zuwa kan su Yaburra ta saka musu tuwo mulmula daya kuma the smallest mulmula a cikin wanda ya rage. Sauran mulmula hudun da ya rage tace na dumamen gobe ne. Miyar su koh arzikin qashi babu bare nama, idanun Fusam suka ciko suka kawo ruwa. Suna hada ido da Hadiza ta juya mata kai tana mata signal din kar tayi kuka dan in har ta kuskura tayi kuka ba abunda zai hana Yaburra lakada mata lafiyayyar duka dan tayi kukan me dalili.

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now