MB - 01

6K 692 266
                                    

5th OCTOBER 2015.
NATIONAL ASSEMBLY ASOKORO ABUJA.

A cikin turancinta mai yanayin na sauraniyar Ingila take jera jawabinta. Hanyar da ta dauka daga karamar hukumar Sandamu da ke Jihar Katsina, zuwa karamar hukumar Baure da abunda ya kewaye ta ce ke bukatar titi har izuwa tushenta, mahaifarta, garin Zangon-Daura.
Shekaru kusan ashirin kenan, ko kuma ta ce a iya tsayin shekarun da ta samu a duniyarta, ta san yadda yankinsu ke da bukatar ingantacciyar hanyar da zata taimaka wurin raguwar yawan hatsarin motar da ke yin asarar rayuka, da dukiyoyin mutane. Tun ba ta da wayau take jin labarin yadda yan siyasa ke ansar kudin gyaran hanyar, amma a karshe ba za su kara jin labarin yadda aka yi da kudin ba. Haka suke rayuwa a wahalce, tamkar garuruwan da suka saka kwarmatsatstsen titin a tsakiya ba kananan hukumomi ba ne ba.

Zaman gilashin da ya like a idanunta ta gyara tana ci gaba da kora jawabinta. Domin kuwa bayan inganta ilimin yara mata da ya kasance na farko a kundin ajendarta, gyaran hanyar shine abu na biyu da take mafarkin kaddamarwa ko dan ta sanya murmushi a fuskokin mutanen da suka turo ta wakilcinsu.

Har sai da ta kai karshe, kafun ta ajje kallonta a kan tarin yan majalissun da suka kewaye kujerun na National Assembly. Ta koma kujerarta ta zauna tana ba mai jawabi na gaba damar zayyana nashi korafin da abun da ya tara su a babban dakin taron.
Awanni kusan ukku suka shude suna zaune tare da bayyana manufofin wakilcinsu, haka kiran Capt. Anwaar Sarari ya dinga dagula lissafinta, ya dinga shigo mata a kai a kai, a karshe ya sanya ta kashe wayar gaba daya tana mika dukkan hankalinta a abubuwan da suka sa gaba.

Hon. Bamanga Jafaru ne mai jawabi na karshe da ya sanya ta kara nutsewa a cikin kujerar da take zaune, ta lullube idanunta tana tunanin dalilin kiran da Capt. Sarari ke mata bayan duk bayanan da ta gama jera mishi jiya da yamma. A hankali ta bude idanuwan, tana kallon jama'ar wurin da ke tattara takardunsu suna dosar hanyar fita. Mikewa ta yi itama, tana daukar jakarta kirar Aldo mahadin takalmanta, a lokaci guda doguwar jilbaab dinta mai kalar makuba tana zarcewa domin lullube kyakkyawar surar da ta kan zamo barazana a gare ta da duk namijin da ya sauke kallonshi a kanta.

"Hon. DanGambo."

Ta ji sautin maganar a setinta. Ba wai bata san mai muryar ba ne, sai dai yadda ya kasa fahimtar babu wani abu da take bukatar ya hada su shine abun da ya hana ta juyawa. Bai yi kasa a gwiwa ba, domin kuwa zira'in tafiyarshi ya kara har sai da ya kai kafada da kafada shi da Ruqayya Manaaf DanGambo. Ya kalle ta, irin kallon da a ko da yaushe bai taba barin idanunshi ba, a hankali ya ce

"Idan ba fada me ya kawo gaba?"

A saman kafafunta ta dakata, kafun ta juyo da fuskarta tana kallon Hon. Bamanga Jafaru da ya kafe ta da nashi idanun. Abun da ta kasa fahimta a lokacin shine yadda tun bayan rantsar da su a matsayin yan majalissu watanni ukku da suka wuce mutumen ke bibiyar lamurranta. Ya kasa gane yadda ba wannan ba ne abun da ya sanya ta neman kujerar House of Reps. Kamar duka sauran mutane, shima ya kasa fahimtar yadda ba ta da lokacin batawa wurin sauraren maganganun sauran yan siyasar da bai shafi aikinta ba. Wasu daga cikinsu sun gane hakan har sun hakura sun daina kula ta, sai dai Bamanga Jafaru ne ba ta san ranar da zai bude kwanyarshi ya zuba manufarta a cikinta ba. Bata san har sai zuwa wane lokaci ba ne zai gane babu wata alaka da zata iya shiga tsakaninta da sauran mazajen duniya da ta dade da yiwa kudin goro a kasan ruhinta. Hakan ya sa a duk wasu harkokinta babu namiji ko guda daya a jerinsu. Direbarta mace ce, haka yan sanda biyun da suke tsare lafiyarta, ma'aikatan gidanta, da hatta mai gadin kofar gidan tsohuwar kurtun soja ce.

Ajiyar zuciya ta sauke, ta kalle shi sosai tana ganin yadda yake fadada murmushin fuskarshi kafun ta ce

"Ban san ta ya zan fara gaba da mutumen da ban taba sani ba, mutumen da fuskarshi kadai na sani sai kuwa sunanshi da nike ji a bakin mutane."

MATAR BAHAUSHEWhere stories live. Discover now