LAILAH-DIZHWAR

1.8K 92 6
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com


*103*

Ahankali ta rufe idanta tare da fadin,
_"Ya Allah"_

Budewa tayi, tare da saka number da tazo mata cikin kanta batare da tasan ko number waye bah.

Ahankali tana kallan Zaliha ta kara a kunnanta.

Nan da nan ta fara shiga, shiru ba'a daga ba daga ita har Zalihar sun jira.

Can bayan lokaci aka daga cikin muryar damuwa Ya furta,

_"Wake magana haka"_

_"Dan Allah koma wane na kira ban san number waye ba na tuna acikin Kaina, sunana Lailah, anyi kidnapping dina ina neman taimako dan Allah "_

Jin haka Jafar yasa yayi saurin tashi daga wajan da yake tare da fadin,

_"Lailah Jafar ne, number ta kika kira nine Jafar, muna nemanki ina kika shiga, meyasa zaki kirani da private number"_

Kukane ya taho mata da sauri ta kalli zaliha tare da fadin,
_"Ki masa kwatance nan ina nane"_

Mika mata wayar tayi Sannan ta shiga yima Jafar kwatance suna Zamfara.

Bayan ya gama jin kwatancan nata ta mika ma Lailah,

_"Hello Dan Allah Jafar kuyi sauri kuzo, ina cikin hadari wallahi, Kasheni zasuyi dan Allah...."_

Bata gama magana ba aka buga kofar dakin da sauri ta saki wayar kasa tana rawar jiki tare da kankame Zaliha.

_"Zaliha, wallahi in baki bude kofar nan ba am going to deal with you guys"_

Shiru sukayi dukkansu babu meyin magana, sabi da Lailah ta hana dan bata san Yaci gaba da magana haka.

_"Zaliha, Am i not talking to you, how dare you close my room"_

Banza suka kuma masa, hakan yasa ya kuma harzuka tare da dukan kofar da kafarsa da karfin tsiya.

Kara makalewa sukayi jikin bango,Lailah sai faman addu'a take yi tana rawa a wajan sabo da tsoro.

_____
Jafar ko shiga cikin station beyi ba ya huce gida, nan da nan ya shirya ya nufi airport bayan ya kira Yan sanda Zamfara waya ya sanar musu da inda Lailah take.

Koda ya kara so babu jirgin da zai tashi lokacin sai wanda zai tashi da yamma, abun beyi masa dadi ba gashi in har mota zaibi hakan bazai samu ba dole ya hakura ya dawo ya sanar ma dasu Dizhwar abunda yake faruwa.

Tare suka runkuta, nan da nan aka shirya wa Dizhwar jirgin da sauran jama'ar sa harda Jafar din dan tafiya zamfara yayin da Faisal kuma yana tsare wajan yan sanda duk da besan anga Lailah bah.

_______
James dukan kofar yake da dukkan karfinsa, ganin bata da alamar budewa yasa ya shiga neman abunda zai karya ta.

Hakan ya dauki tsawan lokaci, da er ya samu wani katan Rashe acan waje, sai yaja baya saiya rugo ya Ya daki kofar.

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now