LAILAH-DIZHWAR

1.7K 79 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
            🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
            🌷🌷🌷🌷🌷🌷
   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
         *_ZAINAB NASEER SARKI_*
             *_ (ZEENASEER😘)_*
          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*

*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*

*(35)*

__________

Koda Anty Amarya ta shiga daki, zama tayi bakin gado tana tunani akan Wannan bakuwa, dan ko kadan bata yarda da ita bah.

Wayarta ta kuma daukowa ta fito falon, har lokacin tana kwance inda ta barta.

Ganin fitowarta yasa Maryam tashi zaune tare da fadin,
_"Toh nizan tafi, sai na kuma shigowa nagode sosai"_

Cikin yake Anty Amarya tace da ita,
_"Toh nima na gode Gashi kuma baki gaya mana sunan ki bah"_

_"Maryam"_
Ta fada tare da fita daga cikin falon, tabe baki Anty Amarya tayi tare da binda da kallo.

_______
Humairah yau tunda safe tazo dan ganin part din Lailah yanda aka gyara shi da kuma abunda ya dace a siya matan.

Koda ta shiga cikin Part dinsu,babu kowa a falon sai Jafar da Asiya.

_"Sannu Romeo and Juliet kun kori kowa daga falon dan baku da kunya kuke Soyayyah"_

Asiya da take kwance jikin Jafar din Murmushi kawai tayi dan bata da alamun tashi, da alama wani abu yake Nuna mata a cikin wayarsa.

_"Bama san sa ido Malama"_
Jafar din ya fada batare daya kalle ta bah.
Zama tayi kan kujera tare da fadin,
  _"Ina su Mami? "_

Asiya ce ta ce da ita,
_"Ya Humaira yau ke kadai,Mami suna daki,"_

_"Eh suna makaranta, Jafar tashi muje naga part din mana, tafiya zanyi wallahi"_
Ta fada tare da tashi ta nufi cikin dakin

Shikuwa kamar badashi take magana bah.

Bata jima a ciki ba ta fito tana gyara mayafinta.

_"Jafar mana"_
Wayar ya mikawa Asiya tare da mikewa yana fadin,
_"Malama nifa kin takura min wallahi"_

Bade ta ce masa komai ba suka nufi wajan, ko ina saida ta shiga ba karamin kyau yayi ba kamar ba shi bah, duk an gyara flowers da suka bushe na wajan asa sababbi ga komai sabo sai kamshi wajan yake, babu kowa duk masu aikin sun gama Kayan furnitures ake jira kawai.

_"Gakiya waje yayi kyau, Ai ko part din Husna inaga be kai wannan bah"_
Humaira ta fada.

_"Gaskiya ya fishi komai, nima nayi tunannin nan za'a sakata kuma naga Memartabah be gyara shi bah"_
Jafar ya fada tare da rufowa bayan sun fito.

_"Gobe insha Allah kayan zasu iso, zan shigo sai a gaya musu masu aikin kaga ayi komai da wuri a gama, kuma kasa Mami ta zaba mata masu yi mata hidima danni bazan samu time din zama yanzu bah, Yanzuma hucewa zanyi"_

_"Ok babu damuwa, saikin dawo, Godiya muke"_

Jafar ya fada yana kallan ta, har mota ta shiga, bayan ta shiga ne, ta kuma kallan Jafar tare da fadin,
_"Dizhwar kuwa yana cikin gidan nan? "_

_"Wallahi ban sani ba, dan da er in yana nan, ki neme shi mana in kina san magana dashi"_

_"Hhhhh lallai Jafar, ko nice babba ba zuwa gidana zai ba, bare kanwar sace ni, inna shigo jibi maybe mu hadu dashi dan ina san zama dashi"_

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now