LAILAH-DIZHWAR

1.7K 95 6
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*74*

______
Lailah bata dawo gida ba sai bayan La'asr, iya gajiya ta gaji, dan da er take tafiya.

A kofar gida me taxi ya ajjetah, fitowa tayi tare da daukar kayanta, yayin da take mika masa kudinsa, daga kan da zatayi ta hango Jafar zaune cikin mota, ya bude ya fito da kafarsa guda waje.

Bayan ta sallami me taxi din, cikin tsoro ta ajje kayan dan daga gani ya jima yana jiranta.

Da Sallama  ta karasa inda yake.

Ganinta yasa ya mike zaune tare da fadin,

_"Sannu da zuwa ranki ya dade"_

_"Yawwah"_
ta fada tana kallansa.

_"Daga gani kin gaji, ai be kamata ki shiga kasuwa da kanki haka bah, kinfi karfin hakan"_

Murmushi kawai tayi.

_"Ina ta kiran wayarki a kashe, gashi babu wanda zan tura ya kiraki, sai Allah ya fito da wannan yayan naki"_

_"Ohk Yaya Aliyu kenan, wayar tawa tana can cikin jaka bama naji kiran ba wallahi, ya hanya"_

_"Alhamdulillah, mutumin ne dai ya kuma tasoni kan maganar tamu"_

Shiru tayi tana kallan kasa kafin tace dashi,
_"Gaskiya nayi tunani kuma nayi shawara da zuciyata, bana san na kuma shiga halin dana shiga a baya, yanda matsayina yake da kuma sanin koni wacece, ina bukatar samun inda zan samu kwanciyar hankali, zan zauna da wanda yake daidai da ni, basai nakai kaina zuwa wani matsayi ba, inda babu abunda yake haifamin sai kuka da bakin ciki"_

Shiru Jafar yayi yana sauraranta duk da besan inda maganar tata ta dosa bah.

_"Lailah ban gane abunda kike nufi bah"_

_"Akwai wanda na yanke hukuncin xan aura, sabo da haka ka bama wa Dizhwar hakuri"_

Rufe ido Jafar yayi yana jin wani iri cikin ransa.

_"Haba Lailah pls kar muyi haka dake, dan Allah karki mana haka, wallahi wallahi Dizhwar a shirye yake da yayi komai akanki, inma bakya san zama cikin gidan sarauta saiya sama miki wani gidan, amma karki kara furta bazaki koma gidan sa bah dan Allah "_

Tabbas tana tausayin Jafar kuma tana ganin girmansa, amma ko kadan bata san komawa gidan sarauta, tana bukatar samun sabon farin ciki, kuma taga hakan a tattare da Faisal.

_"Dan Allah dan Allah inde kana kaunata a gaske a matsayin yar uwarka kamar yanda kake bukata, ka taimaka kaso abunda nake so, Faisal nake so kuma shi xan aura, sabo da haka kayi hakuri"_

Tana kaiwa nan ta juya ta shiga gida tana kuka tare da daukar kayanta.

Shikuwa Jafar ya zama kamar gunki tamkar shine Dizhwar din haka yake ji, yasan ko yana hauka bazai taba tunkarar Dizhwar da wannan maganar ba, dole ya shiga ya fita yasan yanda zaiyi.

Be jira komai ba ya shiga motarsa ya tuka yabar layin.

_____
Lailah tana shiga gida kai tsaye dakinsu ta shige tare da ajje kayanta ta haye kan gadon tana kukan.

Tana cikin hakan ta janyo wayar ta tare da kiran number Faisal.

Ba'a dau lkc bah ya daga tare da Sallama.

_"Hello Faisal kana jina, dan Allah in da gaske  kana sona, ina san ka taimaka ka turo manyan ka domin ayi magana da iyayena ka aure ni dan Allah bana san abun ya huce cikin wannan watan ka taimaka min"_
  Tana magana tana kuka, tayi sauri ta kashe wayar.
kara fashewa tayi da wani kukan mai sauti, tana kaunar Dizhwar fiye da tunanin me tunani, amma tana san tayi forcing kanta akan ta rabu dashi ko zata samu dadi acikin ranta, dole tayi yanda xatayi dan bata san soyayyar sa ta taba mata zuciya, tabbas inta auri Faisal zai rage mata wani abun, tunda zai zama mijinta dole ta soshi.

Haka tayi lamo a kwance ko Mama bata san da shigowar ta bah.

_______
Faisal jin Lailah tana kuka kuma ga abunda take fada hankalinsa yayi mugun tashi.

Tunaninsa menene yasa Lailah wannan magana kode tana cikin matsala ne, nan ya kasa zaune ya kasa tsaye, gashi inya kirata bata dauka harya gaji, yasan akwai babbar matsala dole gobe ya tafi zamfara dan jin abunda yake faruwa, ko lokacin tashi daga aiki beyi ba ya nufi gida.

____
Fareeda tun ranar da Faisal yaje Zamfara kuma ya gaya mata wannan maganar ta shiga gaba dashi, ko kadan ya daina ganinta haka itama, ya nemeta yafi sau a kirga amma ko kadan taki sauraransa, hakan yasa ya hakura ya rabu da ita dan baya san takurata.

Babu wanda zata gayawa damuwarta daya huce Maman tah, sabo da haka dole ta sanar da ita abunda yake faruwa ko zata taimaka mata.

Bata kirata a waya bah, illah mota data hau ta nufi Zamfara gidansu, wanda rabanta dashi harta manta.

_______
Koda ta iso gida yana nan yanda yake illah yan gyare gyare da aka samu, kai tsaye part din Mommynta ta nufa shima an gyara shi.

Cikin sa'a duk da bata sanar da ita zuwanta bah, amma ta same tah.

Cikin falon gidan ta shigo ta zauna, ganin babu kowa yasa ta kuma gyara zama tana jiran wani ya fito.

Wata kuyanga ce ta fito, ganin Fareeda yasata mamaki kasancewar ta jima agidan duk da ta canza mata amma ta gane tah.

_"Sannu da zuwa ranki ya dade kunzo lafiya?"_

_"Ina Mommy take?"_

Abunda ta fada kenan batare data amsa gaisuwar data mata bah.

_"Tana ciki ranki ya dade"_

Tayi mata nuni da dakin dake kallansu.
.da sauri ta mike batare data dau mayafin ta waya ko jaka bah, tana tura kofar dakin ta sameta kwance tana kallo, ganin Fareeda ba karamin mamaki tayi bah.
da sauri ta karso tana kuka tare da fadwa jikintah.

_"Lafiya menene ya faru haka Fareeda ina Faisal din"_
Anty Amarya ta fada tana kallan kofa.

Bata bata amsa ba illa kukan da take ta faman yi matah.

Saida tasha kukan ta gaji tukun ta fara magana.
  _"Mommy nashiga uku bansa yaya zanyi ba tun farko dana kasa jin maganar ki, Faisal ne wai xai kara aure"_

Gaban Anty Amarya ne ya fadi da sauri ta furta,
_"Aure? "_

_"Tafdi jan!, lallai ya tafka babban kuskure, wani irin aure, nima in ba dole ba zan zauna da kishiya ne? da har zaije ya kakalo miki wata banzar kishiya ki kwantar da hankalinki, dani yake zancan, yaushene bikin? "_

_"Nima ban sani ba amma da alama yana nan kusa"_

_"Ya isa ya isa, kukan ya isa haka, karki samu damuwa zan san yanda za'ai, zaki zauna anan har sai komai ya kammala zan maida ke, zai san yayi babban ganganci"_


*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now