LAILAH-DIZHWAR

3.5K 123 5
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
         🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
          🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
  *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
  *ZAINAB NASEER SARKI*
       *_ (ZEENASEER😘) _*
       🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

'''Editing by : Ameerah Zarewa'''

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
                ☆We the best ☆

ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

*81*

____
Faisal kuwa bayan yabar gidan Uncle dinsa, gidansa ya nufa yau yana san su yita da Fareeda domin komai ya zama daidai aurene zaiyi bazai taba fasawa ba saide tayi abunda zatayi.
Yana yin parking motarsa part dinta ya nufa.

Ganin babu kowa kofar a kulle yasa ya jima yana tunanin inda ta tafi.
Bebar wajan ba ya kira number tah, saida tayi Ringing harta gama amma ba'a daga bah.

Hakan yasa ya gyara tsayiwarsa ya kuma trying number tata a karo na biyu, wannan karan ta dauka amma bata yi magana bah.

_"Kina ina ne? "_
Ya fada a takaice.

_"Sai yau zaka tambayeni inda nake, duk sauran lokacin baka damu da inda nake ba, toh ina gidan iyayena"_

_"Da izinin wa kika fita bayan baki gaya min bah?"_

_"Sannu Ubana tunda in zan fita har saina gaya maka kenan, toh ban gaya maka ba kuma na tafi gidan mu"_

Ranshi ya baci sosai, amma saiya hakura da abunda take fada masan,
_"Koma ina kikaje, bana san ki kara kwana daya ki dawo yau dinnan na gaya miki"_
Yana kaiwa nan ya kashe wayar tare da yin tsaki ya nufi nashi part din.

___
Ita kuwa bayan sun gama wayar bin wayar tayi da kallo tare da fadin,
  _"Lallai ma Faisal ya raina min wayo, shi da be damu dani ba har yake wani nunamin shi babba ne"_

_"Lafiya Fareeda kike magana ke kadai"_
Anty Amarya ta fada tana kokarin zama gefanta.

_"Faisal ne ya kirani, wai duk inda nake karna kwana na tashi na tafi gida"_

Kallanta Tayi tare da fadin,
_"Toh sai me, ki tashi ki koma ta hakan ne zamu samu damar cimma burin mu, ki nuna masa ko kadan baki damu da Auran nasa ba"_

_"Amma Mommy ni fa.. "_

Bata karasa ba ta katseta ta hanyar fadin,
_"Kiyi abunda nace miki, ki tashi ki shirya kije gidan ki, in yaso komai zai daidaita ni zanji da ita Lailah"_

Shiru tayi, bayan nan ta mike tare da shiga toilet, dan yin wanka ta shirya ta tafi gidan nata.

Anty Amarya tasa a hada mata dukkan kayanta,sannan tasa a kira mata drivan tah.

_____
Bayan kwana biyu da abunda ya faru, tun washe garin ranar da lailah ta dawo gida aka gyara musu gidansu harda saban Paint  dan dama ita tace bata san a canza mata wani gidan.

Kuma ta gama yanke hukuncin Zata koma gidan ta amma batare da sanin kowa bah, kuma ta yanke shawarar sanar dasu Mama duk da tasan da huya su kuma yarda.

Yanzu kuwa tana kula su Yusra dan kusan tare suke cin abinci,haka tare da Nina suke kwana,  sun saba da yaran sosai, amma bata wani sakin jiki da Babansu iyakacinta dashi Gaisuwa daga haka bata kuma masa magana, ko gani tayi ana hira dashi bata saka baki haka in sunayi yashiga saita tashi daga wajan, shi kansa yana ganin abunda take masa kuma baya jin dadi kowama na gidan baya jin dadi.

LAILAH-DIZHWAR Onde histórias criam vida. Descubra agora