2~So Sanadi

5.3K 225 2
                                    

🍀****🍀****🍀****
ZUCIYAR MUTUM BIRNINSA
****🍀****🍀****🍀
*What a freaking love story,
Ummy_Saudah✍

®*Saudah Adam Isah*
2

A yau din daya kasance Litinin misalin qarfe 12 dai dai na Rana,

cikin ziyarar dana kai Kanopoly(SOT),a department dinnan na SLT(science laboratory technology),dalibai ne a ko ta ina maqil na tsaka da yin harkokin dake gabansu,
a can na hangi zahra cikin casual look dinta na baqar Abaya,harda sauran 'yan gang dinta zaune kan concrete seats irin wanda aka tanadar dan zaman dalibai,
a daidai gindin wata qatuwar bishiyar cashew inda suka baje koli,
dangin littafai,irinsu pamphlets,manuals,graphs,plainsheets din dake gabansu basa qirguwa,
a lkcnda ko wannensu ya tattare dukkanin hnklnsa ya aza akan aikin dake gabansa se naga zahra ta fita zakkah,
dan da ace zaka lura da itan se kai ta faman qirga tsakin da taketa jerawa babu iyaka,at thesame time kana ganinta ka gama sanin zurfin datai cikin duniyar tunani ba dan qanqani bane,
sai can naga ta sauke hannun tagumin tana qoqarin maida qwallan daya cika mata ido,"Allah ya isa na",ta fada a kan lebenta tana kuma buga wani tsakin,ranta duk a dagule tasa hannu ta wafci wata takaddar dake gefen hagunta,
a dai dai lkcn ta kifa kanta tana kwashe rubutun dake kan takardar a cikin record book,
bata dauki wani lkc me tsawo ba ta dago tana kallon wadda ke kusa da ita me suna yusrah,
"babe,gashinan an kammala yin recording,sauran ki qarashe drawing din,idan dakwai wasu ideas din sai ku qara kafin ai submitting",
zahra tai zancen tana ajje record book din kan cinyan yusrah,daga bisani ta miqe tsaye tana tattare tarkacenta gu daya,
sai a sannan yusrah'n ta dago daga duban da take ma ipad din hannunta tana maida kallonta ga zahra,a cikeda tuhuma ba tareda tayi magana ba,
hkn yasa zahra wara mata manyan idanunta masu haske,
"nd whats with dat look",ta fada tana rufe murfin biron dake hannunta,
"malama ina zuwa kuma",yusrah ta tmbyta,
"where else banda gidan ubana",zahra ta bata amsa tana murmushin yaqen da be kai ko maqogaro ba,dan takaici da baqincikin da take na skipping lectures din da zatai ba dan qarami bane,kawai dan batada wani choice din me sauki bayan wannan shys,sanin ko ya take qaunar karatun,lafiya da kwanciyar hnklnta ne a gaba,
cikin rashin gamsuwa yusra ta cabe baki tana fadin,"u re not serious right!,tunda kema kinsan yanxunnan zamu shiga heat energy(STP112),kuma a bayanshi ga electronic logic for science(STP114)",
cikin wani yanayi zahra ta tabe dan qaramin baqinta,da fuska ba alamun wasa tace,
"wallahi Allah da gaske nake,
masifaffen ciwon ciki ya bi ya addabeni,
gwamma na tafi gidan shine zefi",
tai qarya coz d real fact din shine tsoron karta doshi yammaci bata fita skull din bane,dan sam baza taso abinda ya faru da ita rannan sake maimaita kansa ba,bugu da qari gashi yau raheelah bata zo ba,kuma gashi cikin tarin qawayentan da suka hada department daya daga ita din se raheelah ne suka hada hanya guda,
se a sannan wacca ke kusa da yusrah me suna zainab da namijin dake dab da ita wato ammar suka tsoma bakkuna sunai mata Allah ya sauwaqe,
ita zainab cikin raha da daga murya ta cigaba da fadin,
"amman fa wannan ciwon cikin naki qunqume ne kam,tunda har ya saki breaking golden record",
yusrah tai saurin amshewa,"for d first time in history,
d whole sensational genius in our pot,
d whole miss Mukhtar naAllah wan skip lectures today wo",
ta qare zancen cikin dariya suna cafkewa da zainab,
"banni da lkcn sauraron haukan mahaukata de",zahrah ta fada a cikeda jin haushin su ta juya tana tfy kamar bata son yi,
ai kamar ana tunzurasu naga sun kuma kwashewa da wata gagarumar dariyan,
"ai da sauqi tunda jirgi daya ya kwasomu duka,
kinga knn ke dimma a cikin jerin mahaukatan kike",inji zainab tana kuma fashewa da dariya,
"kanku akeji fa",zahra dake tafe ta fada cikin sautin muryan datasan zasu jiyo,
"Twinkle,ki rabu dasu de kinji,
inanan anan gun zan rama miki ne",
cewar ammar cikin daga murya,
daidai lkcn kamar wacca ta tuna abu zahra tai saurin juyawa tana kallon ammar take fadin,
"yauwa ammar zo ka rakani bakin gate dan Allah",

ZUCIYAR MUTUM BIRNINSAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz