Jin haka yasa ya kuma kallanta cike da mamaki,
_"Saki kuma Baby, Allah ya kiyaye,kar Allah ya nunamin ranar daxan taba sakin matata, har abada aurena nida ke Fareeeda, san danake miki bawai na wasa bane ko yaudara, ina sanki kuma bazan fasa aure bah, sabo da haka kiyi shawara da zuciyarki kibawa kanki hakuri, zan kasance tare dake"_
  Yana kawo wa nan ya nufi dakinsa.

Wani abune ya tsaya mata a makogaro ta yanda bazai iya hucewa ba in ba kuka tayi ba, hannu ta dora akai ta durkusa tana kuka.

_______
Akwana a tashi babu huya wajan Allah yau Lailah ta gama iddar tah dan haka, tana gida kwance kasancewar bata jin dadi dan period dinta daya zo.

Tun safe tana cikin daki, da gudu taji Aliyu ya shigo cikin dakin.

Kasa tashi zaune tayi dan daga kwancan ta dago da kanta tana kallansa.

_"Lailah dan Allah ina kika ajje wayarki"_

Nuna masa tayi, be jira ba ya dauka ya fita yana kokarin saka number, kasa mai magana tayi illah pillow da take kai ta janyo ta dora akan fuskantar tana murza kafafunta.

Mama ce ta shigo dakin tare da zama kusa da ita da roba da kuma hand towel a hannunta.

jin an daga mata riga yasa ta san mamace.

Ahankali take jika towel din tana matsewa saida dora mata akan marar tah, haka tayi ta mata har ruwan ya huce.

jin Lailah shiru yasa ta mike tare da janye Pillow, jikinta duk ya saki bacci me nauyi ya dauketa.

Dan dama jiya kusan kwana tayi ba bacci.

Gyara mata pillow tayi ta fita daga cikin dakin.

Ba ita ta tashi ba sai bayan La'asr,Wanka tayi, sannan ta zauna tana shan tea.

Bayan ta gama ta shiga daki dan daukar wayarta, tana tunanin gobe ko jibi zata koma makaranta.
Ganin babu wayar yasa ta fito dan dazu ta tuna Ali ya dauka.

Da sallama ya shigo, miko mata wayar yayi.

Amsa tayi tana kallansa, lafiya?

Zama yayi tare da fadin,
_"Wallahi ba afiya bah, Yaya Ahmad Kinsan sun koma jos, shine yayo min waya ana can ana fada, gaba daya an kona musu unguwar su, da er suka tsira daga su sai kayan jikinsu, ga matarshi da tsohon ciki ga yara biyu, yanzu na samu na tura masa kudin mota, gobe da sassafe zasu taho gida"_

Baki ta tabe tare da fadin _"wani gidan"_,

_"Lailah wani gida zasu daya huce wannan"_

_"Aikuwa bade nan bah wallahi ba yana aiki bah, kuma nasan ai bazai rasa kudi ba,bade nan ba wallahi"_

_"Haba Lailah waike wace irin yarinya ce ne, haka Yaya aminu yazo a haife ya haife ki amma kika ci masa mutunci yanzu kuma Ya Ahmad in shima haka zaki masa dan Allah ya isa haka"_

Tunda ya fara maganar take hararrsa.

_"Kuma da kike maganar yana aiki, ya jima da barin aiki, sabo da matsala da aka samu aka kori ma'aikata da yawa ciki harda shi, dan Allah ki barsu karkiyi musu wata magana kuma ki barsu da abunda ya dame su"_

Duk da bata jin dadin jikinta hakan be hanata magana bah,
_"Lallai Aliyu dole ka fadi haka, tunda dama ai duk bakinku daya, sai yanzu kasan da hakan, mu ba abun tausayi bane kenan, kasan irin gwagwarmayar rayuwar dana sha, har zubarmin da mutuncina akayi, amma na rasa wanda zai tsaya mun, ku da sunan ina da yan uwa maza wanda zasu tsaya min akan komai"_

_"Babu me tausayina, babu me kaunar mu, babu wanda yake zuwa wajan mu, ga halin da iyayena suke, nice na zama komai nasu yayin da kowannensu yake cikin daula, dama nasan komin daran dadewa wannan rana zata zo, ai iyayye ba abun wasa bane, wallahi kadan ma suka fara gani, dukiya masifar ta fada mai, ya godewa Allah daba shi aka kona ba kuma wallahi har abada bani basu"_

Tana gama fadar haka ta shige cikin daki tare da fadawa kan gado rubda ciki tana kuka.

Jin wayarta na kara yasa ta mike zaune tare da goge hawayanta ta dauka.

Jafarne yake kiranta bayan sun gaisa, yake sanar mata da jibi xaizo.

_"Gaskiya ba Lallai in ina nan bah, sabo da ina tunanin gobe zan koma makaranta"_

_"Haba Lailah bawai na hanaki karatunki bane, dan Allah kiyi hakuri a gama warware dukan matsala in yaso saiki koma amma yanzu ki jirani gobe toh dan Allah inyaso jibin saiki tafi"_

Shiru ta danyi kafin tace,
_"Allah ya kaimu"_

______
Dizhwar yanzu komai ya fara dawo masa daidai, yana tafiyar da harkar Sarautar yanda ta kamata hakan yasa Memartabah jin dadin jajin da aka samu, yana taimako sosai gashi kullum yana cikin bada shawarwari,in ya samu lokaci yakan je ya duba Mami amma batare da sanin Memartabah bah.

Husna kuwa tayi kiba ta kuma yin kyau, kullum cikin kwalliya take da badanci, bata da aiki sai yawan biki da party, yau tana wannan kasa gobe tana wancan kwata kwata yanzu bata da lokacin kanta balle na Dizhwar, shima kuma baya ta tata, dan yanzu ta dawo da Lailah yake kuma.

Yayin da Anty Amarya, ta fita daga harkokin su, ta nufi wani shashancin kuma, ita kuwa Hajiya Babbah kullum cikin karama tawada ruwa take dan bata san a dawo da Mami.

_____
Aliyu be sanar dasu mama zuwan su Ahmad ba kawai Lailah ya gayawa wanda ita kuma ko kadan batayi kokarin sanar dasu hakan ba, illah shirin tafiya makarantar ta da takeyi, yauma tunda safe ta tafi kasuwa.



*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now