_"Yawwah!, ko kai fah bara na kira tah"_

_____
Bayan yan lokuta asiya ta shigo da trey babbah tare da duk abunda tasan  Yayan nata yana bukatah.

Bayan ta gaida shi ta fara hada masa tana mika masa.

Duk cikin gidan babu girkin wanda Dizhwar yake ci daga na asiya saina Mamanshi fulani, haka kuma bame shigar masa daki sai su biyu, sabo da Allah yayi masa kyankyami da tsafta, ko kadan baya san talakawa baya san nakasasshe, haka duk kuyangin gidan da masu aikin gidan babu ruwansa dasu.

Bayan ta gama hada masa ya fara ci, suna hira da Hajiya harya gama, mikewa yayi tare da fadin
_"Hajiya bara in yima su Mami sallama"_

Ba'a san ranta bah ta amsa da
_"Saika dawo Allah ya kiyaye hanya"_

Ameen ya fada yana fita daga cikin dakin nata.

Kai tsaye bangaran mahaifiyar tasa ya nufa, koda ya isa kannansa ya tarda zaune tare da ita kan gado suna hira da dariya.

Ganinsa yasa Asiya da Zakiyyah suka Fito daga dakin suna da da gaidashi.

Zama yayi gefan gado yana fadin
_"Wai dan Allah Mami Na gaya miki Ki daina zama da yaran nan, basu da aiki sai hira"_

Kallansa tayi tana fadin
_"Ni Bana san iyayi, daga zuwanka zaka takura musu, basai anyi hutu bah suke zuwa, kaida yake baka gani ka kyale, bana san takura, babu wanda ya takuraka kaima baka isa ka takura kowa bah"_

Shiru yayi dan abun yana kona masa rai, mikewa yayi yana fadin
_"Naje kano saina dawo"_

_"A dawo lafiya ta fada"_

Harya fita ganin ranta a bace ya dawo tare da zama kusa da ita yana fadin
_"Mami kiyi hakuri dan Allah, bana san kina fishi dani, kullum Cikin nunamin fishinki kike"_

Murmushi ta danyi kafin tace
_"Kaima haka Zalika kullum cikin takurawa yarana kake"_

_"Toh na daina wallahi, aimin addua saina dawo"_

_"Allah ya dawo dakai lafiya"_

_"Ameen"_ ya fada yana Murmushin farin ciki.

Kasan cewar me martaba yaje gaisuwa gidan wani amininsa yasa be je wajan sabah, cikin mota ya shiga ya nufi Airport.

🌸🌸
______

Misalin karfe 5pm, Ta fito daga wani katuwar plaza, hannuta rike da leda, ita da wata kawarta tana gefantah.

_"Rauda pls dan rike kin kayan nan ina zuwa"_

Wanda aka kira da Rauda ta amsa tare da fadin
_"Baki da aiki Kullum sai kinyi mantuwa bana san irin wannan"_

_"Pls kiyi hakuri mana, wayata fa na manta tana chaji"_

Amsar kayan tayi tare da fadin
_"Allah ya kawo ranar da zaki daina wannan mantuwar taki"_

Murmushinta me kyau tayi tare da mika mata kayan ta koma ciki tana dariya.

Tana nan tsaye harta karaso tana fadin,
_"Wallahi na manta ashe na sakata tana chaji kinga kuma na fito na barta"_

Ita de wanda aka kira da Rauda batayi magana bah ta mika mata kayan nata.

Duk rigar plaza dince jikinsu Red an rubuta sunan plaza din a bayansu,da kuma wando na jeans ajikinsu, sai karamin hijab, sai suka dora dogayan riguna bakake a sama.

Rauda da kuma Kawarta Lailah suka tare taxi suka nufi gida.

_______
Kasancewar ba unguwarsu daya bah, saida aka fara sauke Rauda tukun aka nufi Gida da Lailah.

Daida unguwarsu dake cikin Zamfara wato *Sabuwar kaura*, Daidai wani gida madaidaici, ana sauketa ta mika masa kudinsa tare da shiga cikin gidan.

Tsakar gidan ba babbah bace haka kuma daki biyu ne aciki sai bandaki da kuma kitchen.

Zaune take kan tabarma tana tankade gyari.

Kasancewar Iyayan nata kuramene, yasa batajin Sallamar da tayi bah sai ganinta tayi.

Murmushi tayi tare da ajje garin tana nuna mata da hannu alamun sannuda zuwa.

Zama tayi kan tabarmar kusa da ita, tare da janyo laidar, data shigo da ita, ta dauko mayafi daga ciki tare da mika matah, tana nuna mata da hannuntah,
_"Mamana wannan siya miki nayi sabo da baki dashi, acikin albashina yau an bani, kingani"_
Ta dauko sauran kudin tana nuna mata.

Dadi taji, sai kuma ta nuna mata,
_"Kudin haya kuma waye xai biya da kika kashe mana su"_

Hannunta ta kamo tana murmushi,
_"Mamana, ina sanku Sosai,duk abunda na samu Nakune, kuma zamu biya kudin haya, lafiya kiyi farin ciki"_
Tana nuna mata da hannunta yanda zata gane.

Dadi Maman taji,  ta mike tare da dauko mata abinci, Tana ci tana yima maman hira suna Dariya.




*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR Where stories live. Discover now