Chapter 4

5.7K 149 4
                                    

POTATO SOUP

Abubuwan da ake bukata
Kori, dankali,nama,Albasa,karas,peas,maggi,attarugu,tumatur,gishiri,mangyada,kayankamshi

YADDA AKE YI
Atafas nama da albasa da gishiri a dan soya
A soya kayan miya
A tsayar da ruwa a juye nama sa maggi da kayan kamshi
Idan ya Tafasa a saka dankali da peas da kori a bari su nuna. Za a iya amfani da kaza ko kifi idan ba a so a maimakon Jan nama.

WHITE SOUP
Abubuwan da za a tanada daidai da potato soup sai dai in ana so za cire dankali. Yadda ake yi kusa daidai da potato soup, sai dai shi idan komai sun nuna, sai a kada filawa da kori sai a agauraya a miyan bayan an rage wuta idan ya yi dan a kauri sai a bar shi ya kara turaruwa na mintina sai a sauke. Ana amfani da shi a inda za a iya amfani da stew ko kuma a mixed grill a maimakon sauce.

FANKE

Abubuwan da ake bukata
Filawa, sugar, baking powder, yeast

YADDA AKE YI
Zamu kwaba suga amma mu na iya jika yeast din mu da ruwan zafi sannan mu kwaba da filawa kwabin ya kasance ruwa ruwa idan ana so yayi auki zamu iya kwabawa tun dare ya kwana da safe mu rinka soyawa zaiyi kamar kwallo.
Idan kuma na sauri ne anan take muka kwaba Muna iya soyawa.

GINGER DRINK

Abubuwan da ake bukata
Danyar citta, A barbada, suga, lemon tsami.

YADDA AKE YI

Zamu kankare bayan cittar mu tafasa cittar, tare da bawon abarba. Idan mun sauke zamu tace idan ya huce mu zuba suga mu motsa dan lemon tsami mu motsa asa a firig mu jira yayi sanyi. Amma idan ba mu son bawon abarbar zamu markade abarbar mu ne. Idan mun tafasa cittar mu sai mu hade su mu tace, da abarba da cittar sannan mu zuba suga da lemon tsami.

ZOBO DRINK MAI GUAVA DA ABARBA

Abubuwan da ake bukata
Zobo, danyar citta, kanumfari, sugar, guava, abarba.

Yadda ake yi
A tafasa zobo da bawon abarba da citta da kanumfari.
A diga dan kanwa ya cire tsamin
A barshi yayi sanyi
A markada guava asa
A markada abarba ma asa
A sa suga
A garnishing wato ado da cucumber
A barshi yayi sanyi

GIRKINMU NA MUSAMMAN Where stories live. Discover now