Chapter 1

10.6K 367 25
                                    

FRIED RICE
Abubuwan da ake bukata
Shinkafa, karas, danyen koren wake, peas, kabeji, nama, liver ko kidney, albasa, kori, butter ko mangyada, gishiri, maggi, kayan kamshi.

Yadda ake sarrafawa
A zuba tafashesshen ruwan zafi akan shinkafa, abarshi ya dan jika na minti biyar da dan gishiri sai a wanke  a baza ya sha is ka.
A wanke nama ko liver ko kidney a tafasa shi da gishiri da rabin albasa, thyme da dan kayan kashi sai ya nuna, a tsame a yayyanka kanana a soya, a ajiye ruwan na man.
A kanka re karas, a yayyanka shi, a yanka koren wake, kabeji, a hada su da peas baki daya a wanke da gishiri.
A narka butter a tukunya, ko a dumama mangyada a soya. A soya wankakkun  ganyennan, a sanya kori da gishiri lokacin soyawa, sai a tsantsame man da ke jikinsu da matsami.
A mai da mai kan wuta, a soya shinkafa da wata dai sai har sai yayi wasai ya watsu amma a sa sauran korin  a cikin suyan.
A juye na man ko hantan ko kodan, da soyayyun ganyennan da ruwan nama, asa maggi, da sauran kayan kamshi, a sai da ita ruwan yadda zai nunar da shinkafan.
A rufe  idan ya kusa tsotsewa a janye wuta  sosai har sai ya nuna

RICE BALLS

Dafefen shinkafa,Kwai, flour, kayan miya, tafashesshen nama, kayan kamshi,

Yadda ake yi
Akada Kwai a zuba akan shinkafa a mots a
A barbada flour ya dan yi karfi
A yanka kayan miyan kanana  a zuba da nama da duk kayan kamshin
A fara curawa
A dora mai yayi zafi a rinka soyawa kamar yam balls. In kuma na sugar za a yi, murje kwakwa a zuba da sugar a cure a soya.

DAFUWAR SHINKAFA DA BOTA

Itama kamar yadda ake dafuwar farar shinkafa ne. Ki zuba gabadaya ruwan da shinkafa, idan sun tafaso ki juye ki wanke, ki mayas a wuta da ya dauki tafasa ki kawo bota dai dai, kamar shinkafa mudu ki zuba bota rabin gwangwani amma karami.
Ki yanka albasa kanana a zuba tare da gishiri, a rage wuta kadan. Za aji kamshi na tashi.

DAFUWAR SHINKAFA DA KWAKWA

Idan shinkafa ta tafasa za a wanke sannan a maida wuta, da ma an gurza kwakwa kanana an ajiye a gefe daya, sai a zuba cikin shinkafan da ke bisa wuta da dan gishiri da albasa su ci gabadaya da dahuwa.

DAFADUKAN SHINKAFA DA KWAKWA

Za a tafasa shinkafa a wanke a ajiye gefen
Ga nama yanka kike, an wanke an data yayi laushi.
Za a dora mai a wuta a yanka kayan miya kanana, a sa maggi, gishiri, albasa, da kwakwa da aka kusa.
Sai a soya sama sama, sannan a hade da shinkafarnan da aka tafasa a kara ruwa da ruwan kwakwa dai dai yadda zata shanye tsab ba tare da ta cabe ba, da zarar tafara kamshi sai a sa curry.

DAFADUKAN SHINKAFA DA KAYAN LAMB

Zamu nemi shinkafa, nama, kabeji, karas, sannan gishiri, maggi, kori, mangyada, da sauran kayan kamshi,

A dafa nama da gishiri, maggi, albasa, thyme, yayi taushi.
Ga kayan miya an jajjaga, za a soya da mangyada, a tsaida ruwan, idan ya
Tafasa a wanke shinkafa da already an par boiling, a zuba kabeji, karas, koren wake, alaiyahu, sunanan kusa yan yanka su, an wanke fes.
Da shinkafan nan ta soma juya wa sai a zuba gaba daya, in ana  Bukatan kiyi shima sai a gyara a wanke da ruwan zafi a zuba gaba daya, da vegetables da curry
A rage wuta, don ta dafu ba tare da tayi kauri ba.

DANBUN SHINKAFA

Za a kai inji a baza a tankade gain a gyara tsakin wanda da shi Za a yi dan bun.
Sai a wanke shi fes, a tsame shi an hada madanbaci ko irin na zamanin iyayen mu, ko kina iya sa karamin kwano  a kasan tukunya ki wanda zai yi ci al halin kin zuba ruwa kadan a can kasan kwanonyadda dai ruwan ba zai bull ba.
Sai a zuba wannan tsakin shinkafan da kika wanke cikin rarity a A rufe da led a ko jarida sannan a datse da marfi ruf  ka da a yadda tiririn ya fito na tsayin minti 35.
Sai a suke, a kwashe.
Kin yanka attarugu, albasa, mai ga aleyahu, inda hali kin tafasa nama kin data sai a sa kori.maggi, gishiri da mangyada, a motsa sosai sai a duba ruwan tukunyar idan ya lone a kara, sai a killer dan bun a led a, Yadda ake kulle alale, a rufe shi ruf.

BIRABISKON SHINKAFA

Zamu nemi shinkafa, mangyada, gishiri, maggi amma ajino motto.
Sai a wanke shinkafa fes, a shanya ta bushe sannan akai inji a barza, a tankade a find a grain muyi amfani da tsakin, zamu turarashi sai mu sauke, mu hada a yayyafa dan ruwa da gishiri, maggi, sannan mu mayar wuta.

SINASIR NA SHINKAFA

Zamu samu danyar shinkafa, mu jika ta kwana, sannan mu  tsame tasha iska, mu kai inji a mayas gari fari sol, da daddare zamu kwaba garin da cokaliin yeast 1, kamar yadda ake kwabin waina.
Da safe zamu motsa mu zuba gishiri, sugar da yar kanwa amma in yayi tsami sai ruwa kadan.
Sai mu nemi kwanon da muke tuya Kwai, mu shafe sa mai, musa kaman ludayi 2 na gullin sunasir mu rufe da karamin faifai ko ko wani marfi.
Ki barshi na tsayin mintoci kamar 5, sai ki bude, ki sauke ki sake goge mai ki mayas wuta ya dau zafi, a haka harki gama.

WAINAR SHINKAFA

Zamu jika danyar shinkafa, da daddare, da safe mu wanke ta fes, mu baza ta sha iska, mu kai inji, a mayas gari fari sol, idan mun tashi kwabin wainar zamu nemi in a misaligned mudu 1 na shinkafa, cokali 1 na yeast, zamuyi talge kaman na tuwon, sai a sauke ya huge, kamar za a iya soma hannu, sai a dauki sauran garin a ringa motsawa a cikin talgen har sai ya tuku kar a manta a lokacin ne za a jika yeast a sa garin kwabin.
Da safe idan zamu soma tuya zamu motsa yar garin kubewa kamar cokali 1 mu zuba mu yanka albasa, mu hada da gishiri mu zuba da ruwa kadan muna motsawa, sai munga kullin wain ar yayi kamar kaurin ko ko.
Sai mu gyara tanda a dora  bisa wuta ana zuba cokali 1 na mai, da gullin ludayi 1. Haka za ayita tuyawa har gullin ya karemu.
   

GIRKINMU NA MUSAMMAN Where stories live. Discover now