chapter 2

7K 170 14
                                    

FUNKASAU

Za a nemi alkama a bakace ta fes, a fitas da tsakuwa. Sai a kai injin, amma
Wanda zai kai nikan a gargadeshi sosai kada a fara nika gero kafin a jika alkaman, dalilin kuwa shine da zarar kwarar gero ya shiga cikin alkaman to ba zancen funkasau, don ba zai tashi ba, a fara nika masara ko dawa amma banda  gero, haka yeast ma in yayi yawa zai ki tashi.
Kaman a misali mun auni mudu 1 na alkama zamu nemi cokali 1 na yeast sai mu kwaba da dan tauri tamkar yadda masu gini ke kwaba kasa,  kada a cika ruwa ta tsinke kuma kada tayi tauri kamar fura, ki rufe ruf, yadda iska bazai shiga ba, a ajiye a waje mai dan zafi, a kalla kwabin yayi awa 5.
To kina budewa zakiga ta kunburo ta cika fal, sai a watsa dan gishiri, maggi, a yanka albasa kanana a sa aciki, a sa ludayi ko muciya a buga sosai yadda zata rinka iya rabuwa da hannun ki, to yayi kenan sai a dora mai a kasko a ringa diba da hannu ana bude ta ana sakawa cikin mai da kin saka zaki ga ta taso fuf, tabbacin tuya  tayi kyau.

ALKUBUS

Yadda muka gyara garin alkama na yin funkasau haka za a gyara nayi alkubus. Shima bari mu debi mudu 1, sai ki sa cokali 1 na yeast da ruwa ki kwaba, kwabin zai fi na funkasau tauri, shima za a rufe ruf yadda iska ba zai shiga ba, a ajiye waje mai zafi saboda yayi saurin tashi ya kunburo sosai, a kalla ya sami awa 5 a rufe.
Za a sami gwangwanayen madara wanda aka bude anayin alale, dasu     a ke alkubus.
Za a shafe su da mangyada yadda ake shafawa na alale, ki jujjiya kullun alkubus din ki, a na iya sa gishiri in ana so, sai a rinka dan mulmulewa da hannu ana sakawa cikin gwangwani, amma rabin gwangwani za a rinka zubawa saboda idan ya taso  zai cika har baki, za kuma aga sama shi ya tsatsage.
Idan mun tashi dora wa zamu zuba ruwa dan firit a tukunya sannan mu jera gwangwanaye, mu tabbatar ruwan be bai taboo rabin gwangwanayen ba, don da zarar ya tafaso zai iya shiga cikin alkubus, sai a rufe tukunya ruf da marfi da ba zai fidda turiri ba.

GURASA

Za a nemo filawa rabin kwano, sai mangyada rabin ludayin miya 1, da gishiri kadan, sai bakar hoda cokali 1, sai a hada gaba daya a kwaba da dan ruwa, muyi kwabin da taushi kada fa yayi ruwa, to sai mu rufe ta taso na mintoci ko awa 1 don ta taso sosai.
Sai u rinka diba muna murzawa muna bata fadi. Ga mai a wuta da yayi zafi, zamu fara tuya mu toye tas.

GIRKINMU NA MUSAMMAN Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu