PROLOGUE

39 4 0
                                        

JIRWAYE

Khadeejah Bint Ismail

Young talented writers association (YOTA)

PROLOGUE (THRILLER)

Cikin sanyin jiki take fitowa daga cikin bedroom ɗin ta tana tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, sai dai tana zuwa corridorn da zai sadata da parlor ta tsaya tana dafe ƙirjinta da ke nan kamar an ɗaura mata dutse a kai.

Ɗan leƙowa tayi da kanta taba duban wacce ke zaune kan kujera, kusan kamannin su guda in ka ɗauke wasu ƴan abubuwa da suka bambanta su.

Jin alamun ana kallonta ya sa ta waigo ai ko karaf suka haɗa idanu, da sauri ko ta maida kan nata ciki tana kuma dafe ƙirjinta cikeda tsoro.

Murmushin mugunta ta saki tana takowa cikeda aji har izuwa gabanta tana cewa '' Mrs R right? Oops my bad Ray of hope ake ce masa ko?".

Yawu ta haɗiye tana cewa '' I'm sorry twin''.

''Yau kuma ni ce twin ɗin taki? I thought I was but a mistake and why would you be sorry? Oops playing the good twin card right? Sai dai kin makaro you were absolutely wrong as you are nothing close to been good, you are evil kin sani na sani''.

''i'm sorry ba laifi na bane, i know that I've been bad.......''

''May be nawa ne right? Har kina da bakin magana ne saboda ban buɗe sirrinki a faifai ba ko? Ko dai in buɗe ne?".

Da sauri ta kuma zaro idanunta ta na kallonta baki take motsawa da niyyar magana ta gaza saboda tsabar rudewa.

Murmushin cin nasara ta saki tana cewa '' You wouldn't want that do you? Na tabbatar you'd make a good headline aesthetic by Teeyah the model connived with kidnappers to kidnap her only twin a day to her wedding just to marry her supposed husband to be, but you don't have to mind don ban taɓa son shi ba he's a trash I've been looking for a way to trash out and you did help me dump on yourself so bravo for that''.

Nisawa tayi tana tafiya ɗaya-biyu kafin ta tsaya tace '' duk da haka there's a price you'll have to pay for that, with your life that I'd make it a living hell. You'd regret sharing same womb with me so enjoy kafin hell ɗin ƙi yayi befalling miki''.

Ta ƙarashe so deadly and real, duk wannan murmushin muguntar ya kau daga face ɗin ta. Juyawa tayi ta bar mata parlorn ba tare da ta tsaya sauraronta ba.

Zamewa tayi kan rug tana sakin ajiyar zuciya cikeda fargaba tana mai janyo duk addu'ar da ta iya tunawa har ya zo kan harshen ta.............

''Mayaudari mahainci, mugu azzalumi wallahi ba zan zauna da kai ba. Da in zauna a gidan ka gwara mota ta bi ta kaina in mutu ka sake ni nace maka!!! ''.

''Do you need help with that? Ko ba maganar mota ta bi ta kanki naji kina yi ba?'' ya tambaya cike da isa yana zaune a inda yake ko motsi bai yi ba.

Yawu ta had'iye tana kallon shi ta gaza cewa komai sai kawai ta ji ya kece da wata kalar dariya da ko ba a gaya maka ba ta mugunta ce yace '' oops my bad ashe fa jira kike in baki hak'uri in shaida miki in babu ke ba zan iya rayuwa ba ko? Unfortunate for you it won't happen ga hanya nan maza ki fita Allah ya tsare ko an gaya miki nima ina son auren kin ne da kike min ihu a ka.....''

''Brother'' a ka furta daga bakin k'ofar shigowa parlorn, duka suka waiga suna kallon shi har ya k'araso ciki yana mai cigaba da cewa '' miyasa kake haka ne? Why don't you explain things to her tunda ka san sai tabbas an mata laifi?".

''Don an mata laifi shi ne zata tsare ni a gaba tana min ihu ni yaronta ne?".

''But ba ka ganin ba ita d'aya ba ce?".

''Ai ka san ban gani sai ka gaya min dallah malam bar nan wajen ha'a ko kaine kake auren min ita ne ban sani ba''.

Miyau ya had'iye yana cewa '' kayi hak'uri'' daga haka ya juya ya fita yana mai jin takaicin halin d'an uwan na shi, ita ko da ke zauna jin abinda ya gayawa wanda ta san su tare ne ya kuma karya mata zuciya amma sai ta tuna hak'kinta da ba zata tab'a ba shi damar ya tauye ba don haka ta mik'e itama  ta nufi hanyar barin d'akin wata kalar tsawa ta ji ya daka mata yana cewa '' don't you dare move an inch ''.

''Wallahi ba ka isa ba sai na bar gidan nan a yau ba gobe ba, ba zan tab'a zama da azzalumi irin ki ba.......'' kasa k'arasawa tayi sakamakon wani d'aci da ta ji a k'irjinta da sauri ta dafe shi tana fara kakari kamar wasa duhu ya mamaye maganan ta ta zube a wajen tana kiran sunan Allah...........

It is a story of betrayal deceit and love, toxic and unusual love. Sauyin k'addara abu ne da bai tab'a faruwa ba amma kun tab'a jin inda aka yi exchanging fates? Shin kun san rad'ad'in da ke cikin ahalin mutum su yaudare shi?.

Ba nace ba amma tabbas kamar yanda salon Nisfu Deeniy TYFLT yake daban haka shi ma wannan yake daban. Ku dai ki bi ni a sannu in muku unveiling rikitacciyar k'addara mai firgita kwanya.

Deejasmah✍️🌵

JIRWAYE Where stories live. Discover now