Chapter 2:Thriller

Beginne am Anfang
                                    

*

 
     Daga ciki Hamood da ya taso da ƙyar ya buɗe,ganin driver ɗinsa yasa shi sauke numfashi,cikin girmamawa driver yayi masa sallama ya amsa,sanda suka gaisa kafin maganarsa a hankali kuma cike da damuwa ya furta "ohh! An tashi dinner?" Driver ya amsa yace "ehh ranka ya daɗe" Hamood da bai kula da Safwa ba sam har sannan yace "but na ce fa ka dunga tafiya da key ɗin,idan an gama hidimar sai ka dawo da shi,think haka zai fi" driver yace "ehh ranka daɗe ba maganar mukullin bane,dama Hjy ce tace na rakota" cike da mamaki Hamood yace "wace Hjy?" Driver ya ɗan waiga tare da kallon Safwa,sam ya rasa wane suna zai faɗawa Hamood da zai gane,kawai yace "gata nan ai tare muke" dubansa Hamood ya kai inda yake ganin alamar tsaiwarta,Safwa ta taho tana cire niƙab ɗin da ta sa,Hamood cikin shock ɗin ganinta a lokacin da bai zata ba yace "Safwahh! Da wannan daren? Why kika zo?" Wani irin kallonsa take tun farkon tsaiwarsa,sosai taga alamar rashin lafiya a jikinsa don ko ya yi rama sosai a cikin kwanakin,bata iya cewa da shi komai ba ta taho za ta shige,hanya Hamood ya bata ta wuce ciki,lokaci ɗaya yana kallon driver ɗinsa yace "ka jira a waje za ka mayar da ita gida yanzun nan" driver ya amsa respectfully tare da juyawa,saurin mayar da ƙofa Hamood yayi ya rufe,lokaci guda ya nufo inda Safwa take tsaye.

*

      Around 9am Umma da taji shiru ta sake fitowa,ranta a mugun ɓace ganin kusan 2 hours kenan da ake ta jiran Safwa amma shiru har sannan bata shigo gidan ba,gashi ƴan uwan Abba sai mita suke an barsu zaune kamar marasa abun yi,in baza'a kira musu ƴar tasu ba su san inda dare yayi musu tun wuri,fitowa tayi a fusace saboda yanda ƴan uwan Abba suke ta maganganu,sanda ta shigo gidan Mama bata parlour,kai tsaye ta wuce upstairs,ɗakin su Baniynah da tasan can suke ta buɗe ta shigo tana faɗin "wai Safwa don ubanki baki ji saƙona bane? Almost 2 hours nazo nace Babanku na kiranki,amma kin ƙi zuwa dole sai da kika ja min magana sannan hankalinki ya kwanta" wuƙi² ɗin da Radhiya dake kwance tayi ne yasa Umma yin shiru tare da binta da kallo,hankalinta a kan ɗakin da babu kowa sai su kaɗai ita da Radhiyar da kusan ta sume saboda bata taɓa zaton Umma will come har saman ba,a wani iri hankali Umma dake kallon alamun rashin gaskiya a fuskar Radhiya cewa "ina Safwan take don ubanta?" Radhiya tayi shiru ta rasa me za tace,lokaci ɗaya ran Umma ya ƙara ɓaci,tana kallon Radhiya da tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa,in a serious note tace "Radhiya tell me ina Safwa? Ki faɗa min tsakaninki da Allah kada ki ɓoye min,ni mahaifiyarta ce zan fahimta,idan kin ɓoye min kin san dai baza ki ɓoyewa Allah ba ko?" Gyaɗa kanta Radhiya tayi a hankali ta ɗago kanta,fuskarta na sauya yanayi tace "wallahil'aziim Umma sanda na hanata zuwa amma ta dage min sai ta je,ban taɓa tunanin ba a daren za ta dawo ba,shi yasa ma banje na sanar miki ba" Umma da tayi galala da baki tace "tun dare bata nan? Bata kwana gidan nan ba? Ina ta tafi? Gurin wa taje?" Umma ta jero mata tambayoyi da yawa,Radhiya ta gyaɗa kanta a saɓule tace "she said that za taje ta duba Hamood,ya sanar mata bai da lafiya tunda aka fara bikinsu and dalilin da ya hanashi zuwa all the event kenan.. Na so da ta yi haƙuri,don babu irin shawarar da ban bata ba,amma ta dage sai ta tafi.." Lokaci ɗaya hankalin Umma ya tashi ta dunga maimaita "can ta kwana gurinsa?" Radhiya ta girgiza mata kai tace "i'm not sure Umma,amma dai ni yanda muka yi da ita kenan da muka dawo gurin dinner" cikin damuwa Umma da hankalinta ya gama tashi ta furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Amma dai Safwa an yi wawuyar yarinya wallahi,yanzu ɗaukan kafa tayi tabi namiji? Meke damunta haka?" Knocking ƙofar ɗakin da aka yi yasa Umma juyawa tana faɗin "wallahi sai na saɓarwa yarinyar nan.. Don ubanki daga ina kike? Ina kika je kika kwana?"

*

     Wazeer na fita gidan Hamood ya zube saman kujera tare da dafe kansa dake wani irin sarawa da juya masa,how could he zai yi irin wannan maganar da ɗansa? Me ya kaishi cewa ya bar masa gidansa? Me yasa zai tsaya suyi duk wannan jayayyar da ɗan cikinsa? A fili ya furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Ba kaɗan ba ya shiga damuwa da tashin hankali,idan da ace ya san abunda maganar da zai yi zai haifar kenan,ko tantama babu ba zai taɓa yi ba,but ya zaiyi tuntuɓen harshe ne dai ya yi,kuma ƙarshe ga abunda maganarsa ya haifar,tambayar da ya fara yiwa kansa shi ne "ina yaron nan zai tafi?" Cikin kiɗima da tashin hankali yayi saurin ɗaukan wayarsa,number Isma'il ya shiga kira,bai daɗe yana ring ba Isma'il ya ɗauka respectfully yace "assalamu alaikum ranka ya daɗe" Dad da har wani zazzaɓi ya fara saukar masa yace "Isma'il duk abunda kake ina so ka bari kabi bayan Wazeer kaga ina zai je" Isma'il ya amsa da faɗin "to ranka ya daɗe.." Hamood ya sauke wayar tare da furzar da ajiyar zuciya,addu'ah yake Allah yasa ba gurin Hooriyah Wazeer zai koma ba,tunanin haka yasa nan da nan hankalinsa ya ƙara tashi,yanda Wazeer ya furta yana son mahaifiyarsa,haka itama Hoor ya tabbatar da irin soyayyar da take masa,babban damuwa da tashin hankalinsa a yanzu bai wuce ace Wazeer ya komawa mahaifiyarsa ba,ya tabbatar muddin haka ta faru ko shakka babu dole Wazeer zai sake tsanarsa ne kawai a rayuwa.

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: May 06 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

WAZEER!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt