Mysha!

131 13 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.*

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*

'''D̶I̶S̶C̶L̶A̶I̶M̶E̶R̶:Tʜɪs ʙᴏᴏᴋ ɪs ᴀ ᴍɪx ᴏғ ʜᴇᴛᴇʀᴏʙɪᴏɢʀᴀᴘʜʏ ᴀɴᴅ ғɪᴄᴛɪᴏɴ. Iᴛ ʀᴇғʟᴇᴄᴛs ᴛʜᴇ ᴀᴜᴛʜᴏʀ's ᴘʀᴇsᴇɴᴛ ʀᴇᴄᴏʟʟᴇᴄᴛɪᴏɴs ᴏғ ᴇxᴘᴇʀɪᴇɴᴄᴇs ᴏᴠᴇʀ ᴛɪᴍᴇ. Sᴏᴍᴇ ɴᴀᴍᴇs ᴀɴᴅ ᴄʜᴀʀᴀᴄᴛᴇʀɪsᴛɪᴄs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄʜᴀɴɢᴇᴅ,sᴏᴍᴇ ᴇᴠᴇɴᴛs ʜᴀᴠᴇ ʙᴇᴇɴ ᴄᴏᴍᴘʀᴇssᴇᴅ,ᴀɴᴅ sᴏᴍᴇ ᴅɪᴀʟᴏɢᴜᴇ ʜᴀs ʙᴇᴇɴ ʀᴇᴄʀᴇᴀᴛᴇᴅ. I ʜᴏᴘᴇ ᴜ ᴡɪʟʟ ʟɪᴋᴇ ᴛʜᴇ sᴛᴏʀʏ ᴛʜᴇ ᴡᴀʏ ɪᴛ ᴄᴏᴍᴇs ᴛᴏ ᴜ.'''


01

#Mysha!

•••Haɗaɗɗen parlour ne irin na gidan ƴan gayu,yanda komai yake zaune a muhallinsa da ƙamshin da parlon yake fiddawa me sanyin daɗi da bawa rai nutsuwa,ya isa ya fahimtar da kai gida ne ba na gamagari ba,ko'ina it looks very clean and tidy,babu kowa parlon sai babban TV dake aiki shi kaɗai volume ɗin can ƙasa ba'a jin komai,yanda gidan yai shiru ko yaya kayi ƙwaƙƙwaran motsi za'a iya ji,a hankali wani sound me kama da kukan tsuntsu ya fara tashi da yasa parlon fara ɗaukan sautin,da sauri wata ƴar yarinya da baza ta wuce 14 yrs ba ta buɗe ƙofa ta fito daga kitchen,ba sai an maka describing kasancewarta me aiki ba musamman duba da yanayinta,though suturar jikinta masu kyau ne masu gidan na kula da ita ba kamar a wani gurin da aka ɗauki ƴan aiki wulaƙantattu da suke ƙasƙantar da kansu akan neman halal ɗinsu ba,to cut it short duk inda masu kuɗi suke daga kamanninsu kana iya ganewa. Beeping ɗin da wayar keyi daga saman center table ne yasa yarinyar ta taho da gudu ta ɗauka,duk da bata san me aka rubuta ba dan kana kallonta za ka san batai makaranta ba,a hankali ta tsurawa hoton screen ɗin wayar idanu na tsayin 2 minutes,kafin da sauri ta juya ta wuce corridor tana faɗin "Mimi! Ana miki waya" jin shiru² yasa ta buɗe ƙofar first bedroom ta shiga da sallama tana cewa "Mimi! Ga wayarki ana ta kira" daga cikin bathroom akai gyaran murya,ta kalli ƙofar kafin tace "ashe tana bayan gida" a hankali ta ƙarasa ta ajiye wayar saman bedside drawer sannan ta wuce ta fita ta koma bakin aikinta. Ba'a yi minti uku ba wata kyakkyawar matashiyar budurwa wacce baza ta wuce 28yrs ba fara sol da ita kamar ka taɓa jikinta jini yai tsaruwa ta buɗe ƙofar bathroom ta fito,ɗaure take da babban towel sai ƙaramin tada rufo kanta da shi,sam bata kula da babu kowa ba,da siririyar muryarta hausarta yai kamar ba asalin pure Hausa irin na mutanen Kano ba take faɗin "Suwaiba! Ina wayar yake? Wake kirana da safen nan haka?" Shiru tayi ganin babu kowa cikin katafaren ɗakin baccin nata,juyawa tayi a hankali tana goge ruwan dake jikinta tace "ohh! Ta fita kenan bata jira na fito ba" dai² nan wani kiran ya sake shigowa wayar ƙiran blackberry black color,saurin ƙarasawa tayi ta kai hannu ta ɗauka,sunan da ta gani akan fuskar wayar yasa tai hanzarin answering tana yin sallama "assalamu alaikum! Yaa Abuye ina.." Abunda kunnenta suka jiyo yasa ta sakin salati a ruɗe tana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Wane hospital ne?" Tana gyaɗa kanta tace "gani nan in sha Allah yanzun nan" jikinta ko'ina ɓari yake tace "tou!³ Sai na zo.." Kallo ɗaya za kai mata ka fahimci tana cikin damuwa,da sauri² ta sauke ƙaramin towel ɗin kanta ta yafa a kafaɗarta,nan baƙi siɗik ɗin gashin kanta da akaiwa wasu irin yiri²n kitso tsagarshi kamar wanda akai da allura da suke jiƙe da ruwa suka bayyana sun kwanta saman bayanta,asalin kyakkyawa ce tubarkallah ƙwayoyin idonta sun yi brown,kyakkywar round face ɗinta na ɗauke da dogon hanci da ɗan matsakaicin bakinta,kallo ɗaya za kai mata ka san ba Hausa/Fulani bace,saboda kamanninta sun fi da asalin shuwa arab,da sauri ta wuce ta buɗe wardrobe ta janyo doguwar rigar abaya,hankalinta a mugun tashe sai sauri² take bakinta na ɓari tana magana da kanta ita ɗaya,bata gama saka rigar ba ta ɗauko key ɗin mota ta fito tana ƙwala kiran "Suwaiba! Suwaiba!!" Daga kitchen yarinyar ta fito tana amsawa tace "ga ni Mimi" Mimi na kallonta ta miƙa mata key ɗin mota tace "yi maza ki kaiwa Isiyaku ya fito min da mota zan fita da sauri" hannu bibbiyu Suwaiba tasa ta karɓi keys ɗin tana cewa "tou Mimi" daga haka ta juya fita ita kuma Mimi tai cikin corridor ta koma bedroom ɗinta da niyyar ƙarasa shiryawa,komai a gaggauce take yinsa tana gamawa,taja babban hijab tasa akan rigar sannan ta ƙarasa ta ɗauki wayarta sai ƙaramar jaka da baifi purse ba da sauri ta nufi ƙofar fita bakinta na faɗin "astagfirullah wa'atubuu ilaik.." A corridor tana sauri² wani ɗan kyakkyawan fine boy da bazai wuce 8yrs ba ya taho,kana kallonsa za ka tabbatar duk inda ya fito jininta ne saboda tsananin kamar da suke,duk da ƙarancin shekarunsa amma hakan bai hana na tabbatar nan gaba zai tsayi ba,a shagwaɓe yana kallonta idanunsa da suke brown irin na mahaifiyarsa sak suna lullumshewa kamar yana jin bacci,da miskilin muryarshi na yara yake faɗin "Mimi! Unguwa za kije?" Cikin sauri tana gyara zaman hijab ɗinta tace "ehh Babana.. Zanje Nassarawa hospital su Yaa Abuye sun kirani an kai Mama bata da lafiya,tun dare basu kwana a gida ba an kasa gane meke damunta" a hankali ya gyaɗa kanshi jikinsa yai ɗan sanyi yace "Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗarta" Mimi da kamar tana magana da babba tace "ameen *ZAKIN* Mimi.." Har ta wuce ta juyo tana kiranshi *"ABUU-TURAB!"* Juyowa yayi yana kallonta a miskilance,tace "ina lil Mysha?" Ɗan turo baki yayi a shagwaɓe yace "i don't know,maybe she's out" Mimi tace "will u help me kaje ka nemota ku zauna gida da Aunty Suwaiba?" Kamar zai fashe mata da kuka yace "Mimi ni bana son zuwa gidan" buɗa ido tayi tace "wane gida?" Yai shiru yana kallonta fuskarsa a tsume ya ƙi cewa komai,girgiza kai tayi tace "ok! Jeka bari nasa Aunty Suwaiba taje ta ɗaukota" daga haka ta wuce ta barshi a gurin,taɓe ɗan ƙaramin bakinsa dake ɗauke da siraran lips yayi kafin a hankali ya wuce yana tafiya majestically kamar wani babban saurayi,kitchen Mimi dake ta sauri ta isa tana kallon mai aikinta tace "Suwaiba! Dan Allah ki shiga gidan Daada ki ɗauko Mysha,kada ki bari ta sake fita ko'ina,ban sani ba kou zan dawo da wuri,but ki kula da su please bazan tafi da su ba,idan kin ɗaukota ki kulle ƙofa kada ki barta ta sake zuwa ko'ina.. Yanzun nan Yaa Abuye ya sanar min Mama ce ba ta da lafiya suna asibitin Nassarawa,idan kinje ki sanar da Daada na tafi asibitin,dan Allah ki kula da su da gida" Suwaiba dake wanke² ta gyaɗa kanta tace "in sha Allah.. Allah ya bata lafiya,ayi mata sannu" Mimi ta amsa tare da wucewa ta fita cikin hanzari tana kai waya kunnenta,cikin few seconds ta amsa sallamar tare da faɗin *"HAMOOD* i'm going out,Yaa Abuye ya kirani suna hospital tare da Mama tun jiya" tana gyaɗa kanta tace "tou shi kenan.. Ameen thank u.." Gida ne babban family house,part² ta dunga ratsowa tana wucewa da sauri har ta kawo babban zauren gidan dake ɗauke da zanen sarauta da shimfiɗa kamar fada,sai dai kasancewar safiya sosai yasa babu kowa gurin,ta ƙarasa tangamemen giant ƙofar me wani irin tsayi kamar ba don saboda asalin mutanenmu akayi shi ba,sanda ta fito gidan babu mutane sosai a unguwar Galadanci,kasancewar ranar hutun ƙarshen mako yasa yai shiru sai tsilli² da ƙaran wucewar ababen hawa,da yake babu nisa daga gidan kana iya hango titi,inda motarta yake parke ta wuce cikin sauri²,Isiyaku daya fito da motar ya ƙaraso da sauri yana rusunawa da faɗin "Hjy barka da fitowa.. Ina kwana?" Hannu ta miƙa masa a ƙagauce tana kallonsa tace "lfy lou Isiyaku! Bani key ɗin zan yi driving da kaina" yana gyaɗa kanshi yace "tou Hjy! Allah ya tsare a dawo lafiya" ta amsa tana tafiya heading to gefen driver,tana buɗewa ta shiga ta tada motar ta bar unguwar Isiyaku na ɗaga mata hannu,gudu sosai take tana addu'ar tayi ta isa tasan halin da mahaifiyarta ke ciki. Sanda ta iso asibitin Nassarawa kai tsaye ta wuce ward ɗin da Yaa Abuye ya sanar mata,lokaci guda kuma tana kiran wayarsa,sosai take sauri kamar za ta faɗi,yana ɗauka yace "Hoor! Juyo bayanki" maganar da taji kamar ya rabu biyu yasa tai saurin waigawa,tsaye bakin ƙofar ɗakin ta hango babban Yayanta da suke tsananin kama,da sauri ta ƙarasa gurinsa idanunta na ciccikowa da ƙwalla ta riƙe hannunsa tace "Yaa Abuye! Ina Mama? Ya jikinta?" Mutumin dake kallonta wanda zai kai 40yrs yai mata ɗan murmushi yace "alhmdllh she's fine dear,zo muje suna ciki tare da su Mansoor" bin bayanshi tayi suka shiga ɗakin da sallama,zazzaune ciki suka tarar da mutane yayyunta biyu maza ne sai matansu,a hankali ta ƙarasa bakin gadon ta zauna tana kallon Mama dake bacci hannunta da drip sai oxygen da akasa mata,hawayen idonta tai saurin gogewa kafin ta kalli yayyunta ta gaishesu tare da tambayar me jiki,matan Yayyunta su Aunty Zainab suna mata ɗan murmushi tace "sannu Auta! Ya yaranmu?" A hankali tace "na barsu gida tare da Suwaiba" Aunty Zainab tace "Allah sarki" Yaa Abuye daya zauna saman filastic chair yai ɗan ajiyar numfashi,a hankali ta kalleshi da idanunta kafin tace "Yaa Abuye meke damunta naga ansa mata oxygen?" Ɗan murmushi yai mata yace "she had an asthma,but alhmdllh it's not chronic" zazzaro idanu tayi tace "innalillahi asthma kuma? Dama Mama nada asthma?" Yana ɗan girgiza kai yace "nima abun ya bani mamaki,tunda muka taso ban taɓa ganin wani alama dake nuna Mama nada asthma ba sai yau" Hooriyah ta sauke numfashi a hankali tace "but mene ne yai causing aka san tana da shi yanzu?" Yace "jiya sunje biki and the place babu iska sosai kuma an cika,ina gida aka kirani da wayarta akace nazo da sauri gurin,ina zuwa na tarar an fito da ita numfashinta ya tsaya,so daga nan mukai rushing nata to hospital,amma alhmdllh tunda ta samu bacci" Hoor ta gyaɗa kanta idanunta ƙur akan mahaifiyarsu dake sauke numfashi a hankali,hawayen da suke fuskarta tai saurin sharewa,idonta akan Mama dake bacci tace "Allah ya baki lafiya Mama" Ƴan uwanta suka amsa da "ameen.." Yinin ranar duka suna hospital,Mama kam nata bacci sai dai nurse ta shigo ta dubata,ruwan da akasa mata har ya ƙare tuni an cire,sai can magreeba sannan ta farka,da sauri Hoor ta isa kusa da isa ta kama hannunta idanunta na ciccikowa da hawaye tace "Mama!" Mama ta kalli ƴarta ɗaya tak mace tai mata murmushi,a hankali da muryar marasa lafiya tace "Hoor! Autanah!! Kinzo ashe,sun kiraki sun tada miki hankali kou?" Girgiza kai tayi da sauri ta kwantar da kanta jikin Mama ta rungumeta tare da fashewa da kuka tana cewa "ya jikinki Mama?" Murmushi Mama tayi tana shafa kanta tace "alhmdllh Auta,na samu sauƙi,bari kuka ba mutuwa zan yi ba,in sha Allah sai naga auren jikokina *ABUU TURAB* da Mysha,har ƴaƴansu in Allah ya yarda zan ɗauka nai musu addu'ah" Hoor tayi murmushi hawaye sosai a idonta ta ƙanƙame Mama tace "Allah yasa Mama" Mama tai murmushi tace "ina suke nema mutanen arziki,kou kin barosu a gida?" Gyaɗa kanta Hoor tayi tace "Mama hankalina ya tashi sosai shi yasa ban taho dasu ba na barsu da Suwaiba" Mama ta gyaɗa kanta tace "Allah sarki" dai² lokacin Yaa Abuye ya shigo tare da Dr Sulaiman,ganin Hoor a kusa da ita kyakkywa kamar ka taɓa jikinta jini ya fito ya ɗan ƙaraso yana kallonta,ɗauke kanta tayi saurin yi ta ɗan ɗaure fuska,har ya gama abunda zai yi ya fita,Yaa Abuye yana kallonta bayan ya dawo daga raka Dr Sulaiman yace "Hoor! Ya kamata ki tafi gida haka nan saboda yara,tun safe kina nan and Mama jikinta da sauƙi,in Allah ya kaimu sai ki dawo gobe ki sake dubata,Aunty'nki Zainab za ta kwana a nan gurinta" rau² idanunta suka yi tace "Yaa Abuye zan kwana" da sauri yace "No Hoor! Ki koma gidanki,mijinki bai ƙasar bai sani ba,kuma kin bar yara gurin me aikin da itama yarinyar ce" tace "Yaa Abuye please zan kirashi sai na faɗa masa" da sauri ya kalli Mama dake murmushi yace "Mama ki yiwa autarki magana ta koma gidanta please" Hoor ta juya da sauri a shagwaɓe tace "Mama dan Allah zan kwana kinji,ni wallahi zan kirashi na faɗa masa" Mama tana girgiza mata kai tace "a'a Auta! Ki koma goben sai ki dawo,ai na ji sauƙi tunda gani muna hira dake kou? In sha Allah ma goben kina zuwa za kiji an sallamemu" kamar za tai kuka take kallon Mama tace "Mama ni dai kin daina sona shi yasa za kice na tafi" Mama tace "a'a Auta,kin san Mysha idan bata ganki ba yau kuka za taita yi musu,gara ki koma ki kula da su" a hankali jikinta yai sanyi tace "shi kenan tunda kun koreni" Yaa Abuye dake kallonta yai murmushi,rigimar Hoor ya cika yawa ita kou tunanin ta girma bata yi,tai aure har da ƴaƴa biyu,amma saboda Auta ce idan ta ganta a gaban Mama taɓara take shuka musu,sai da tai sallar isha kafin taiwa Mama sallama tana ta bata saƙon gaisuwa gurin *ABUU-TURAB*,tare da Yaa Abuye suka fita shi ya rakata har inda tai parking motarta a carline na asibitin,sai da yaga ta tada motar tare da kama hanyar barin asibitin kafin ya koma ciki. A hanya ita kaɗai take tunanin yaranta,though ta san Suwaiba za ta kula da su,duk da yarinya ce itanma amma ta horu da aiki a ƴan shekarunta ga tarbiyya,guraren 8:30pm ta shigo unguwar Tudun wuzirci dai² gidan Wazirin Kano tai parking sannan ta sauko ta rufe ta isa babban zauren da take hango mutane zazzaune,da sallama ta iso tun daga bakin ƙofa ta cire takalmin ƙafarta,har ƙasa ta tsuguna kanta a sunkuye ta shiga gaida kyakkyawan farin dattijon dake zaune saman kujera fadawa zagaye da shi "Abba barka da dare" yana kallonta da kyau yace "yawwa Hooriyah! Ya me jikin?" A hankali tai murmushi tace "alhmdllh da sauƙi" yace "tou Allah ya ƙara lafiya ya tashi kafaɗu" ta amsa da "ameen² Abba.." Fadawan sai sannu suke mata tare da yi mata addu'ar samun lafiya ta amsa kafin tace "a tashi lafiya Abba" ya amsa mata ta wuce cikin gida,tafiya take tana wuce part² kamar ɗazu da safe har ta iso nasu,knocking entrance na parlour tayi,daga ciki Suwaiba dake ta jiran dawowarta ta taso ta buɗe,tana ganinta ta ɗan koma baya ta bata hanya tana faɗin "sannu da dawowa Mimi" Hoor ta amsa tana wucewa ciki take faɗin "yauwa Suwaiba,ya gidan da yara? Na san Mysha tai bacci kou?" Suwaiba data tsaya tana leƙen waje tambayarta ya ɗaure mata kai sosai,jin shiru yasa Hoor waigowa tana kallonta,a hankali kuma sai ta tsaya tace "ya dai? Me kike a nan? Ki rufe min ƙofa kada sauro ya shigo mana" saurin rufe ƙofa Suwaiba tayi ta taho jikinta a sanyaye tace "Mimi! Baki tafi da Mysha ba dama?" Hoor da gabanta ya wani yanke ya faɗi ta girgiza mata kai a daburcewa tace "a'a ban tafi da ita ba,ba ke nacewa ki nemota ku zauna a gida ba tunda zan fita? Me yake faruwa? Me kike son ce min?" Suwaiba ta gyaɗa kanta hankalinta na tashi tace "Mimi wallahi tou duk na je na duba bata gidan nan,duk zatonmu ma kou da kika fita kun haɗu ta biki" saurin mayar da hijab ɗin data cire tayi tana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Ina Mysha ta tafi ni Hoor,waye ya ɗauketa? Allah kasa ba ɓata yarinyar nan tayi ba" da sauri ta juya ta buɗe ƙofa ta fita,hankalinta idan ya kai ɗari duk sun kai ƙololuwar tashi,ƴarta ƴar ƙarama da bata fi 3yrs ba,ina ta tafi tun safe? Me yasa babu wanda ya kirata kou a waya ya tambayeta idan suna tare? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take maimaitawa har ta kawo babban apartment ɗin dake can cikin gidan,tana yin knocking baiwa ɗaya daga cikin bayin gidan tazo ta buɗe ƙofa,tana ganinta ta koma baya ta bata hanya tana faɗin "barka da zuwa ranki shi daɗe" Hoor ta wuce ciki da sauri tana faɗin "Daada na nan? I mean batai bacci ba?" Baiwar tace "ehh batai ba amma ta shiga ciki babu jimawa" hanyar bedroom ɗin data san Daada na nan ta nufa,zuciyarta sai bugawa yake fast² hankalinta na ƙara tashi hawaye sun cicciko idanunta,ita fa haka take wata irin mutum ce da lokaci guda take birkicewa,sai data fara yin knocking kafin ta buɗe ta shiga da sallama muryarta a karye,kyakkyawar bafulatanar matar da ta kai 54 yrs tana ganinta ta amsa tana sakin fuska tace "Hoor! Kin dawo ashe?" Gyaɗa kanta tayi tace "ehh Daada! Ina yini?" Daada ta amsa tana kallonta a nutse tace "ya mai jikin?" Hoor ta amsa a sanyaye kafin tace "Daada! Mysha bata nan dan Allah?" Daada ta girgiza mata kai tace "rabona da ita tun sassafe data shigo min,bata fi minti goma ba ta fita gidan nan.. Kou ɗazun da safe Suwaiba ta zo nan ai tana nemanta,itace ta sanar min an miki waya Hjy Kalthoom bata da lafiya" Hoor ta gyaɗa kanta tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Ina Mysha ta tafi" kallonta Daada tayi tace "lafiya dai Hoor?" Hoor tace "ba lafiya ba Daada.. Tunda zan fita nace da Suwaiba taje ta nemota su zauna a gida,saboda ban san ya jikin Maman yake ba,nima Yaa Abuye ne ya kirani yace min suna asibitin Nassarawa,yanzun nan dawowata kenan ina tambayarta ita tace min wai ai ta yi zaton mun haɗu da ita dana fita na tafi da ita" Daada dake ta saurarenta ta gyaɗa kanta tace "ehh tou tabbas nima kusan haka nace mata,in dai ta dudduba gidajen bata ganta ba ta yiwu kin tafi da ita ne" Hoori da hawaye ke mata zuba ta girgiza kai da muryar kuka tace "wallahi ban tafi da ita ba,ni ban ma ganta ba tun safe da na shiryasu suka fito gidan,na dai ga Abuu-Turab da zan fita,ita ɗin ce ban gani ba,na bar saƙon a nemota su zauna gida har na dawo" Daada ta gyaɗa kai tace "tou kuma duka sauran gidajen an tabbatar bata nan?" Hoor tace "Suwaiba ta ce min bata ganta ba duka ta duba" Daada tace "tou tashi muje parlour,bari nasa a kira mazan gidan su bazama su dubota.. Bari kuka za a ganta in sha Allahu" Hoor dake kuka ta taso ta biyo bayanta tana share hawaye akai² tana addu'ar Allah yasa ba wani abu mara daɗi ne ya samu ƴarta ba,a parlour suka zauna Daada na kan kujera Hoor ta zauna saman carpet tana ci gaba da kuka,Allah ya sani zuciyarta bala'in raɗaɗi take mata kuma sai tsinkewa yake,Daada ta kira baiwarta Jummai tana kallonta tace "kiyi maza kije ki sanar da Abba Waziri ya shigo idan babu abunda yake da sauri" Jummai ta tashi ta fita da sauri,Daada dake kallon Hoor tace "ki bar kuka Hoor,in sha Allah za'a ganta,tunda ba fita suke ba ƙarƙari bai wuce ace tana wani ɓangaren a cikin gidan nan" Hoor dai ta kasa daina kuka,ba'a jima da fitar Jummai ba ta dawo ta durƙusa ƙasa kanta a sunkuye tace "ranki shi daɗe yana hanyar shigowa yanzun nan" bata gama rufe bakinta ba sai ga Abba Waziri ya shigo da sallama suka amsa masa,zaunawa yayi saman kujera yana kallon Daada yace "Sa'adatu lafiya kika aika min nazo?" Daada na kallon Hoor tace "wallahi ranka ya daɗe Mysha ce ba'a gani ba,mu nan duk munyi zaton Hoor ta tafi da ita hankulanmu duk a kwance,sai yanzu data dawo ta shigo min take cewa wai bata tafi da ita ba" Abba Waziri na kallonsu da rashin fahimta yace "tou duk an duba cikin gidan ba'a ganta ba?" Daada tace "shi ne dai yanzu nasa aje a bincika" Abba Waziri ya gyaɗa kanshi yana faɗin "in sha Allah za'a ganta,bari kuka Hooriyah.." Hoor dai na zaune ne amma ta kasa daina kuka saboda hankalinta dake tashe sosai²,tunanin ƴarta kawai take da inda ta shiga,cikin few minutes bayin da suka fita neman Mysha duk suka shigo suka zube suna faɗin "Allah ya taimakeki Daada,duk mun bincika gidajen amma bata can,wasu ma sunce sun kwana biyu basu ganta ba" sabon kuka Hoor ta fashe da shi hankalinta na sake tashi,al'amarin kamar wasa sai gashi ƙaramar magana tana neman zama babba,Abba Waziri dake zaune ya shiga buge²n waya yana tambayar kou wani ɗan uwa ne yazo ya ɗauketa ba'a sani ba,haka fadawansa duk yasa suka shiga cikin unguwa suna tattambayar kou an ganta,tun guraren 8:30pm har 11pm babu wanda ya bada labarin ya ganta,zuwa lokacin hankalin mutanen gidan duka ya gama tashi,Hoor banda kuka ita da Suwaiba mai aikinta babu abunda suke,da ƙyar tai waya da Yayyunta ta sanar musu halin da ake ciki na ɓacewar little Mysha,su kansu hankalinsu ya mugun tashi,ranar duk wanda yace yai bacci cikin nutsuwa a gidan sai dai ya faɗa dan jin daɗin bakinsa,Hamood kansa da bai ƙasar Abba Waziri ya kirashi ya sanar masa saboda babu amfanin a ɓoye masa kasancewarsa uban yarinyar da ake nema,alhalin yana da hakki ya sani ai tun a daren ya nemi ticket,hankalinsa duk a tashe ya kira Hoor yana ta faɗa da tambayarta garin yaya tai sakaci yarinyarsa da take just 3 yrs ta ɓace? Ita dai kuka kawai take bata ma iya amsa masa,ƙarshe da yaji haushi ya kashe wayarshi zuciyarsa na tafasa,kafin safiya duka family'n Waziri sun san batun ɓacewar Mysha,wanda za su iya zuwa duk sun hallara,gida ya cika da ƴan jimami da jaje,masu kuka na yi masu addu'ah na yi,tunda sassafe Abba Waziri yasa aka kai hotunan Mysha gidan Radio da TV,kafin kace me labarin ɓacewar jikar Wazirin Kano Alh Aliyu Yusuf ɗan uwa ga Mai martaba Sarki Abduljalal Yusuf ya baza garin Kano da kewayenta,sai dai abun mamaki har sannan babu labarin wanda yace ya ganta duk da yanda zancen ke sake bazuwa,su Mama da su Yaa Abuye ma daga Nassarawa hospital ana sallamar Mama suka wuto Tudun wuzirci gidan Waziri,nan suka yini ana ta nema amma shiru. Can da dare bayan kowa ya fawwalawa ubangiji al'amarinsa,dangi sun tafi kowa ya koma gida ana dai ta ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana,guraren 8pm Hamood ya iso ƙasar,bai bi ta kan Hoor ba dan ya san bama zai sameta a waya ba saboda ita kanta bata san inda ta jefa wayar ba,ya kira Daada mahaifiyarsa ta tura masa Isiyaku driver ɗin gidanshi yazo ya ɗaukoshi daga airport,Daada ta amsa masa kafin ta aika a nemo mata Isiyaku ta sanar masa saƙon uban gidansa,daga nan ɓangaren Isiyaku yana fita ya wuce gidan uban gidanshi,a bakin ƙofar parlon Hooriyah yai sallama,Suwaiba ta amsa masa ya shiga,Hoor ta ɗaga kai ta kalleshi da kumburarrun idanunta da taci kuka ta gaji,Isiyaku na ɗan risinawa yace "ranki ya daɗe na zo na karɓi mukullin mota ne,zanje na ɗauko yallaɓai a filin jirgi" Suwaiba dake zaune ta juya ta kalla a hankali saboda kanta dake masifaffen ciwo tsabar kukan da tayi,daga jiya da daddare zuwa yau ka kalleta dole ta baka tausayi,tai zuru² ta fita kamanninta kamar ba Hooriyah ba,kou abinci ta kasa zama taci saboda rashin sanin halin da ƴarta take ciki,a hankali tai magana tace "ɗauko ki bashi" Suwaiba ta amsa ta tashi da sauri ta ɗauko keys a cikin shelf kusa da TV ta kai masa,ya amsa tare da juyawa ya fita yana faɗin "sai an jima" Hooriyah dai bata ce komai ba Suwaiba ce ta amsa masa,babban motar jeep ɗin uban gidansa da yasa aka wanke jiya kusa da wanda Hoor ta fita da shi jiya ya ƙarasa yasa key ya buɗe,wani irin azababben warin da ya bugoshi yasa ya koma baya da sauri ya bar motar a buɗe yana rufe hancinsa amai na taso masa,within few seconds gurin ya game da mummunan wari,irin warin nan na mushen abu,da ƙyar ya iya daurewa hancinsa a rufe ya ƙarasa kusa da motar yana fito da touch light daga aljihunsa,abunka da mutumin ƙauye ba lallai sai bafulatani ba,dama baka rabashi da fitila saboda yanayin gari musamman duhun dare,haska cikin motar ya shiga yi bai gano komai ba,saboda glasses ɗinta masu duhu ne,back seat ya kai hannu ya buɗe yana hahhaskawa,abunda ya gani ya matuƙar girgiza shi,ya tsoratar da shi,a ruɗe ya zazzaro idanunsa yana faɗin "me sunan Daada.. Ƙaramar Hjy" sunkuye take a ƙasa bayan seat ɗin driver ta ɓoye kanta,jikinsa na ɓari ya tura murfin motar da sauri ya rufe,a matuƙar rikirkice ya bar garage ɗin ya kama hanyar zauren gidan gurin Abba Waziri,yana shigowa da sallama ya zube yana haki yace "Allah ya taimakeka,yanzun nan na je gareji zan ɗauki mota na tafi filin jirgi ɗauko yallaɓai.." Nan ya labartawa Abba Waziri komai yadda ya faru,yace "wallahi ranka shi daɗe duk neman nan da akewa me sunan Daada ashe tana cikin motar yallaɓai" hankalin Abba Waziri a tashe ya miƙe tare da fadawansa yace "muje da sauri" gudu² sauri² Abba Waziri yake tafiya kamar zai faɗi,Isiyaku a gaba sai sauri yake har suka iso gurin motar,Isiyaku ya tsaya baya yana zazzaro idanunsa,ɗan buɗe motar da yai gurin har ya amsa warin,suna toshe hanci da baki duka suka tsaya gurin,fadawa Abba Waziri yasa su buɗe motar,Isiyaku yana haska musu da fitila,ana buɗe bayan mota sai gata kamar yanda ya faɗa,duk taurin zuciyar mutum yaga wannan abun da ya faru sai ya ji tausayin yanda akai yarinya ƙarama ta mutu cikin mota,Abba Waziri banda salati babu abunda yake yana faɗin "a samu abu a ɗaukota a kai cikin gida..."

#Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Wannan wane irin al'amari ne haka ya faru? Ko yaya Hoor za taji idan taga gawar ƴarta? Shin yaya Hamood zaiji idan yazo ya riski wannan mummunan tashin hankali? Salon labarin yayi muku? Me kuke zaton zai faru? Ku dai biyo ni muci gaba da tafiya cikin wannan sabon labarin nawa.. Allah ya sani ban yi niyyar post yau ba har sai ranan 1/Sept,amma babu yanda na iya ne na saki link da wuri,maimakon page 2 da nai niyyar bayarwa ranar ɗaya ga watan da zai kama,ga ɗaya nan na baku yau as gift..




#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.
#30th/August,2023..

WAZEER!Where stories live. Discover now