Guilt-ridden

71 7 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*


                               09

#Guilt-ridden

*SAFWA*

          Tana haurawa sama ta cire wayarta daga jakar,sai data fara ajiyewa jikin bag rack,ta ƙarasa gaban wardrobe ta buɗe,tana tsaye ta ninke mayafinta ta ajiye sannan ta mayar da ƙofar ta rufe,juyawa tayi ta bar gurin,a hankali ta kwanta saman madaidaicin gadonta kafin ta janyo wayarta,ko da tayi online bata ga ALEY ba,kamar yanda tai saving number ɗinsa,kawai sai ta fita ta tafi duba groups data san ana posting novels,har wani farin ciki ta dunga ji da taga anyi posting novels,nan ta shiga karatu abunta,tana yi tana sakin murmushi,underneath tana furta "Allah ameen.. Allah kasa muna da rabon shiga arziki da jin daɗi marasa yankewa" idan taji ana maganar wealthy people,har wani ɗaukan kanta take tana sawa a position ɗinsu,abun na mata daɗi fiye da tunani,musamman idan ta hango friends ɗinta Muniba da Baniynah,wani zubin ana maganar yaran masu kuɗi da suke da gata,sai tace "kai kamar su Muniba kenan" ita kaɗai taita haukarta,tana ji akai kiran maghreeb,har aka shiga masjid aka fito bata iya motsawa daga inda take ba,tana ta bautar waya da karatun da iyakarsa duniya,ta manta da lahirarta da duk hanyar da za tabi wajen samun aljannarta,ba ita ta tashi ba sai da wani masallaci a can nesa suka fara kiran ishaa,sannan ta ajiye tana faɗin "kai! Ashe fa banyi maghreeba ba,gashi har an fara kiran ishaa kuma.." Idan da sabo barin sallah ya wuceta ba yau aka fara ba,sam bata damuwa da yin sallah akan lokaci,tou Umma ba wani damuwa tayi da sasu suyi ba tunma suna yara,kou azumi Safwa bata yinsa sai ta ga dama,kuma Umma bata taɓa ce mata danme ba,har sai da ya wajaba akanta sannan take yi,da zaran ance yau ana azumin Ramadan to fa baza ta moru ba,komai Umma ce za tayi na buɗe baki a gidan,girki da duk wani aikin gida na ɗiya mace,Safwa bata sanshi ba,duk budurwar da taga tana aiki a gidansu,kallon wahalalliya take mata,abu ɗaya zuwa biyu da tafi iyawa a rayuwarta,shi ne tai wanka ta saka kaya ta fice gidansu Baniynah ɗaukan hoto da za'ayi updating ma samari,sai kuma taci ta kwanta Umma ta ɗaure mata,yanzu ne da gumu tai gumu,sannan ta fara mata faɗan ta dunga yin aiki kada taje gidan miji bata iya komai ba,tana so ta ɗan samu hutu saboda ƙafafuwanta,amma ƙememe Safwa ta ƙi sauraren khuɗubar da take mata,sosai Umma ke cikin damuwar wasu cikin ɗabi'unta a yanzu,ta ƙarfi tana son tanƙwarata,ita kuma ta fito ta nunawa uwar bafa zai yiwu ba kawai tai haƙuri,ita bata gaji aikin wahala ba,fatarta ma bai son wahala ita kalar hutu ce matar manya,dole Umma take aikinta da kanta kamar dai ko da yaushe,tunda ƴar gwal ɗin ta kafe atafau baza ta iya aikin da take so tayi ba. Safwa na idar da sallan maghreeba,masallacin line aka fara kiran ishaa,shi kam ta yisa a lokacin saboda wayarta data cinye charge tas,tana tashi taja wayarta tasa charge sannan ta fita ɗakin saboda yunwar da take ji,ƙasa ta sauka ta tarar Umma ta musu tuwon semovita da miyar ɗanyen okro (kuɓewa) wanda tasa masa ogbono yai bala'in yauƙi,abunka da yare duk ta san kan sirrin girki,kallon tuwon Safwa ta dunga yi ranta duk babu daɗi,ita a son ranta ta fi so kayan kwaɗayi danginsu pizza and ice cream,ta tsani duk wani abinci dangin tuwo,wucewa tai parlonsu ta zauna tana kallon su Aasim da suke cin tuwon har faɗa suke,kasancewar Umma ba daga nan ba,ta iya sarrafa abinci yai daɗi,kaci sai kai zaton wata hamshaƙiyar chef ce daga wani ƙasar,da kallo ta dunga bisu fuskarta a kyaɓe kamar ana mata magana za ta kece da kuka,Umma bata ɓata lokacinta gurin kallonta ba though ta ga duk reactions ɗinta,Safwa dai na ta zaune wanting Umma ta tambayeta ya dai? Can dai Umma kamar za tai dariya,dan yanda Safwa kewa su Bilal masifa,tace "Safwa meke damunki ne wai za ki kama min yara da faɗa? Laifin me suka miki?" Cikin ƙulewa Safwa tace "Umma kin san fa ba na son tuwo,amma baki tambayi ra'ayina ba kikai" Umma na mata wani kallo tace "toh! Ai sai ki bari idan kinje gidanki sai kici abunda ranki yake so,nan kam gidana ne sai abunda naga damar yi,dukanmu muna son tuwon har Babanku,dan ke kaɗai baza mu fasa ba wallahi.. Kin san hanyar kitchen sai kije ki nemi abunda za kici,ko indomie kije ki bararraka kici kada ki kwana da yunwa,idan kina da kuɗi kuma yanzun nan za ki iya zuwa ki siyo abunda kike so,ko ki kira wani cikin samarinki ya kawo,har muma mu tayaki ci ko Awwal?" Awwal dake kusa da Umma yace "ni ta kawo ma zanje na siyo mata wallahi duk nisan gurin" Safwa ta maka masa wani kallo ta miƙe a ƙule ta wuce sama tana gunguni. Umma ta ɗaga kai ta bita da kallo kafin ta taɓe baki,underneath tunani take tunda har Safwa baza ta gyara halinta ba,kuma duk abunda ya kamata tayi ta yi,amma bata canja zani ba,ta yi faɗan,ta yi lallami duk a banza,yanzu ta gano hanya mafi sauƙi da za tabi da ita,cikin ruwan sanyi ba sai ta buɗe maƙogoro maƙota sun jiyota ba,za tasa tai give up ma duk wani ego ɗinta da take ji da shi,daga yau abincin duk da tasan ba ta so,su za ta dunga yi a gidan,sai dai kada taci. Shawaran Umma Safwa tabi,tana haurawa sama dake ta san kan logics ɗinta,musamman idan tana son wani abu gurin samarinta,sad emoji taje tai status da shi,kafin kace me fiye da ⅔ na samarinta da sukai viewing,sun fara tambayarta mene ne? Meke damunta? Ita da waye? Waye ya ɓata mata rai? Zo kaga yanda ake jan aji da shagwaɓa da kwantar da kai,cike da ƙwarewa ta faɗima da yawansu abunda ke damunta,gwaninta da son burga gurin maza,nan da nan aka fara kiranta ana lallashi,Wazeer ko nace Aley a gurinta kamar yanda tai saving number ɗinsa kawai da bata gani ba,babu alamar kuma ya ga status da tayi,tun safe da sukai chat,sai wayar da sukai ɗazu da yace ya ganta zoo road,dama kuma ita ke shisshige masa,ita ke fara yi masa magana,yanzunma sanda ta shiga contact ɗinsa sad emoji ta tura masa sannan ta fita,ta ci gaba da chat ɗinta.

WAZEER!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon