🫧🫧🫧🫧🫧

Kiran sallar asuba na farko ne ya tayar dashi da kyar ya iya bude idanuwansa da sukayi masa nauyi, kallan yadda ya kwanta yayi kafun ya sauke idanuwansa a kanta ,sosai ta bashi tausayi, a hankali ya daga jikinsa daga kan nata ,yasan da kyar in wuyanta be mata ciwoba,gyara mata kwanciyar yayi kafun ya mike ya shiga wani door , be wani jimaba ya futo sanye da farar jallabiya tare da nadin larabawa, sosai kamanninsa ya kara fito wa na sak larabawan sai faman tashin kamshi yake kamar ba asubahi ba, a hankali yake yin komai ,mafarkin da yayi na kara dawo masa,ganin ana kokarin tada sallah ne yasashi fita a dakin gabaki d'aya. Be dade da fita ba tahee ta farka daga baccin ta,sosai wuyanta yake mata ciwo da cinyoyinta,dubawa tayi taga king bayanan turbune fuska tayi kamar yana kallanta kafun ta mike taje tayo alwala, tana cikin yin sallar yashigo dakin,kan gadon ya koma kamar Wanda akasa dole sai faman ya tsina fuska yake sabida yadda kansa yake tsananin sara masa,kafin ta tashi daga kan sallayar har wani baccin ya fara fisgarsa, a hankali ta fara taku ita a dole karta tasheshi taje ta kwanta itama a hankali,duk abunda take yana kallanta motsawane kawai baze iya va,be dade ba wani saban baccin ya daukesu gabaki d'aya.

9:45am tahee ta soma mitsi mitsi da idanuwanta kafun ta budesu gabaki d'aya,gefen da yake ta juya wayar taga babu kowa, da sauri ta mike tare da nufar hanyar fita, har ta saka hannunta da niyar bud'e kofar ta tuna gargadinsa "kada ki kuskura ki kara fitowa nan baki yi wanka ba,kaxama ",shagwabe bakinta tayi kafun taje tayi wankan shaf shaf ko munti 10 batayi ba kafun ta shirya cikin wasu riga da wando na pakistan masu taushi da santsi,gashin kanta da ya zubo mata kar gadan bayanta tayi kiciniyar daurawa ganin ta kasane yasata daukar ribbon din tare da nufar falo, ba kowa a falo sai kamshin daddadan kamshi da yake tashi ne cike da sanyayyar kamshin ac, kofar fita daga part din ta nufa hannunta dauke da ribbon dinta ga gashinta da ya dauko mata har wajan kwankwasanta sai faman sheki yake dauka,Daidai ta sa hannu zata bude kofar taji an turo kofar da karfi.

Sanye take cikin wasu kananan kaya da basu dame jikinta sosai ba ,fuskarta Tasha uban makeup da bakin glass a idanta sai faman taunar cingum take, a yatsine take bin tahee da kallo irin kallon up and down dinnan, ta be bakinta tayi tare da kokarin shigowa ciki,wani irin kallo tahee ta jefa mata kafun ta furta"wacece ke",daga hannu budurwar tayi tare da tsinkawa tahee mari a fuska"tanbayata kike wacece ni dan uwarki". Tunda ta cinka mata marin tahee take dafe da kuncinta,kalmar uwarkice ta tsaya mata arai,itama batayi wata wata ba ta tsinkawa budurwar mari hagu da dama kafun ta dago idanuwanta a zuciye tana binta da kallo, cike da tsantsan mamaki budurwar take bin tahee da kallo itama hannunta dafe da kumatunta, dan ba kadan taji zafin marin ba"ni kika mara "ta furta kamar me shirin yin kuka ,banza tahee tayi da ita kafun ta juya tare da komawa ciki, tana cikin tafiyar taji anwani fusgota tare da hankadata, rufe idanuwanta tayi sosai ganin tana kokarin faduwa, a maimakon ta fadin sai taji an tarota,tare da saukan tagwayen maruka dafe kumatunta tayi ganin ba ita aka mara ba ,kafun ta bude idanuwan a tsorace,Wanda ta ganine yasata sakin ajiyar zuciya kafun ta kara rikeshi gagam.

Suman tsaye budurwar nan tayi jin saukar marin da ba a taba mata shiba a duba,hawayene sosai suka cika mata idanuwa kafun ta dago da idanuwanta ta kallesa,sosai ya kara yi mata kyau fiye da kullum da take hasashensa acikin zuciyarta, kalllansa take kamar wacce tasami abun kallo kafun ta soma magana"yanxu king akan wannan shegiyar da take muku wasan kwaikwayo da rayuwa zaka sa hannu ka maran", kamar wacce tayi magana da dutse haka ya mayar da ita a wajan,ribbon din hannun tahee ya karba itama bai ce mata komai ba ya tufke mata gashin kafin ya ja hannunta suka bar wajan. Sakin baki tayi tana kallan abunda yake wa yarinyar da taji lokaci d'aya ta tsana ,abunda ko a mafarki in aka fada mata bazata taba yadda dashi ba ,wai yau shine yake taba mace ba ita ,ganin sun juya  ne yasata bin bayansu tda kallo ganin irin wulakancin da king yayi mata a gaban kaskantacciyar da takewa kallan me aiki"kamar ni, Basma isma'il yar governor guda aka mara agaban wannan kaskantacciyar",da karfi ta furta"impossible gaskiya bazai taba yiwuwa ba, dole ma mom kisan yadda zakiyi ayi auran mu da king cikin kankanin lokaci kafun nan kuma sai na gyarawa shedaniyar can zama" tana kammala zancanta tabar wajan cike da bacin rai.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now