*******

A firgice aunty ta koma part din ta , ko ganin hanya batayi sosai tana shiga falon ta tarar da ba amrah a falon, cikin sauri ta nufi dakin da amrah take ,tana shiga ta tarar da ita tana waya,ganin yadda aunty ta shigo cikin dakin ne yasa ta kashe wayar ,duk atunaninta mutuwar taheen ce ta komar da ita haka ,"aunty ya karin hakurin ku", ta fada tana kyalkyalewa da dariya, cikin ba'kin ciki aunty ta kalleta "ubanki Kena ya karin hakurin "mikewa zaune amrah taji jin abunda aunty tace, waje ta samu ta zauna tare da fashe wa da kuka, tsaya kallanta amrah tayi,"wai ke aunty lapiya na ganki haka,mu da yau ta kasance ranar farin cikin mu", bata kai karshen maganar ba ,aunty ta kudun Dino zagi ta dire mata,"ubanki ke da farincikin,dan ubanki da kinsan abun bakin cikin da naje na tarar bazaki mun wannan banxan zancen ba,toh bari na futo miki a mutun tunda bakya ganewa,ban taba sanin cewa sheguncan tsinannu bane se yn Andy, kamar ni zasu ha'inta"kamar ya aunty ban gane ba,cewar amrah ,wani dogon tsaki aunty ta karaja yanajin yadda zuciyar ta ke soyuwa da bakin ciki,"toh in baki sani ba yanxu ki sani,shegiyar yarinyarcan tana raye bayan tayi loosing memory dinta",jin karshen zancan ta yasa amrah sakin ajiyar zuciya "aunty wannan me sauki ne tunda tayi loosing memory dinta ,kinga sai muyi anfani da wannan damar mu kasheta kawai", a tsawa ce aunty ta tashi"ke dan ubanki me yasa kullum kwakwalwarki ta Kifi ce,to bari na fito miki dallah dallah, shegiyar yarinyarcan sun daura Mata aure da king, yanxu haka tana bangaransa ", kalmar an daura mata aure da king ne kawai ya shiga kunnanta, take a wajan ta yanke jiki ta fadi sumammiya, da sauri aunty ta nufi toilet,muntuna kadan tafito hannunta dauke da ruwa, watsawa amrah dake kwance tayi a wajan,tana farkawa tasaka kururuwa tana birgima kamar wacce aljanu suka shigeta,"bazata sa'buba wallahi bazan yadda ba , king nawane ni kadai ba wata shegiya da ta isa ta zama mallakinsa sai nii,wallahi sai naga bayanki, sai na kashe ki" itama aunty bata kulata ba sai ma barin dakin da tayi, sosai amrah ta haukace, sai faman fashe fashe take tana kururuwar bazata yadda ba ,tanayi tana kuka ,lokaci zuwa lokaci tana sakin dariya kamar me tabun hankali, da sauri ta nufi daya daga cikin a kwatunanta, tana budewa wasu magunguna ne a ciki, guda ukun cikinsu ta bude tare da kwankwadewa gabaki d'aya,lokaci d'aya ta bugu sai faman surutai take.

➰➰➰

A 'ban garan mamy ma cikin futar hayyaci ta nufi 'ban garanta,lokacin ihsan da sumayya suna zaune suna kallo, ganin yadda ta shigo ne yasa suka bita da kallo,"mamy lapiya naganki haka "cewar ihsan tana mikewa,bata kulataba sai ma zagaye falon da ta fara ,"shikenan aikin da muka dade munayi ya tashi a banza shegiyar yarinyar can na tsanekiii", cikin hada baki suka kalleta"wace yarinya"yanxun ma bata kulasu ba, sumayya ce ta kulu cikin tabara tace"wai ke mamy ana ta miki magana sai wani faman ja mana rai kike",girgiza kai mamy ta fara tana buga cinyarta, "shikenan ta faru ta kare, yanxu abunda zayed ya d'auke mu kenan,ya daurawa king aura ba tare da sanin muba" za bura sukai baki Dayan su musamman sumayya datafi kowa firgita,cikin rawar murya ta soma magana"wane..wane king din wai"dogon tsaki mamy taja,"Wana king kika sani, to bari na fada muku kuji ba sa kowa aka daura masa aure ba sai da wacce shegiyar taheera take kowa, ni zasu rai nawa hankali suce wai tayi loosing memory ",bushi bushi sumayya ta fara gani, take a wajan ta fada kan kujerar da ta tashi, d'age kafada ihsan tayi"toh mamy Menene aciki dan ya aureta inda da abincewarsa" bata karasa zancan taba taji saukan maruka dama da hagu" shegiya daman nasan ke ba Kaunar cigaban mu kike ba" 'bace mun da gani,tana kammala zancanta ta kama hannun sumayya suka nufi up stairs,akabar ihsan da rike kumatu.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

KANO

Knocking din kofar dakin akai, "shigo "oumma ta bada umarnin shigowa ,khaleed ne ya shigo dakin cike da sallama,"oumma barka da hutawa" ya furta yana sakin murmushi,itama murmushi ta sakar masa,"barka khaleed"ta fada da sigar tabbatar wa, sosai ya washe hakwaransa, baki manta sunana ba oumma,Kai naji dadi" itama oumma murmushi ta sakar masa,"oumma hira na zo na tayaki kar abar mun ke ,ke kadai "yanxun ma murmushi ta sakar masa, yana cikin maganar sane zahra ta shigo dakin itama "Laa,yanxu yaya khaleed ahaka Allah yace ,shine ka gudo kabarni ni kadai wajan dadi"dariya khaleed ya saki"nasan halinki ai shiyasa nazo bude fadata ", da sauri zahra ta shigo ta itama ta zauna kusa da oumma,"oho dai nide bazan yadda ba", kallan oumma tayi ,"oumma Aini zaki fi so ko"gyada mata kai oumma tayi ,da sauri khaleed ya kalleta,ni bakya sona kenan ko, girgiza masa kai tayi "Aah Kai ma ina sanka", kama hannunta yayi "toh oumma zaki dauke Muma kamar taheer da taheera ", ya fada a raunane tunowa da mahaifiyarsu da sukayi, itama zahra kwallace ta tarar mata ,ganin yanayinsu yasa oumma sakin guntun murmushi"sosai ma kai kamar taheer kake a waje na ,itama kamar taheera ta take"sosai farin ciki ya bayyana a fuskarsu,suna cikin zaman nan ne dady ya zo wajan,kallansu yayi tare da girgiza kai"me kuke anan ku taso kuzo ku kwanta kun cika ta da surutu"dan turo baki zahra tayi" to dadi zan kwana a..."bata karasa ba dady ya kalleta"Ah ah fa, ku tazo maza" tashi sukai tare da kallan oumma cikin hada baki,"oumma sai da safe", Allah ya tashemu lapiya ,suna gama fadar hakan suka wuce,shima dady kallanta yayi"sai da safe" be jira amsarta ba ya bar wajan.

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖💖

Mss Lee 💖

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now