🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Sanye take cikin maroon d'in abaya A shape,kayan sosai ya fito da shape din jikinta, cikakken gashin kanta ya fito sosai ta gefe gefen kanta da ya kwanta,kwance take kan 3 sitter din falon ammi tana bacci cikin kwanciyar hankali, zoya ce ta shigo falon itama cikin shigar ta sa'banin tahee ita kananan kayane a jikinta bink colour Riga da wando, kanta sanye da pink din hula itama gashin go shin ta sosai ya fito, gashin d'awisun da ta zo nunawa tahee take ta faman wasa dashi harta nufa hanyar dakin taheen sai kuma ta jiyo ganin ta kwance tana bacci, saurin rufe bakinta tayi tana dariya kasa kasa kafun ta salallabo a hankali ta nufi inda taheen take, gashin d'awisun ta dauka ta somayiwa tahee tafiyar tsutsa a tafin kafarta, motsa kafan kadan tahee tayi kafun ta gyara wanciyarta, kara sa mata gashin zoya tayi nan ma motsa kafar tata tayi a hankali tana ya mutsa fuska,ganin hakan yasa zoya cigaba da sa mata d'awisun, cikin sauri tahee ta farka har dan kwalinta na zamewa, sosai zoya ta fashe da dariya ganin yadda tahee ta 'bata fuskarta, itama tahee ganin zoya yasa ta mike da niyar kamota,sauri kaucewa zoya tayi tana dariya, ganin hakan yasa tahee binta da sauri, gudu zoya ta sa tana dariya tare da komawa bayan kujera, ganin hakan yasa tahee binta da gudu har dankwalin kanta ya faduwa kasa, bata damu da faduwar da yayi ba ta cigaba da bin zoya da niyar kamota ,itama zoyan ta ki bari ta kamota sai zillewa take tana mata dariya, ganin hakan yasa tahee sakin duk karfin ta ta biyo zoya da ta nufi hanyar fita da gudu gashin kanta sai faman lilo yake a bayanta, karan da tayi da abune yasata yin baya baya kamar zata fadi , batasan lokacin da ta fado kansa ba,sai daddad'an kamshin da ya cika mata hanci , da sauri ta wayo idanuwanta waje "na shiga uku ni tahee, kullum sai kinyi lefi", saurin sunkuyar da kanta kasa tayi  tare da soma wasa da yan yatsunka, dai dai ta bude baki da niyar yin magana taji an capko dogon gashin kanta me shegen sanshi da daukar ido, tanbayar da ya jefo Matane yasata zare ido " are you a non-Muslim da zakiyi Karin gashi a kanki" ya karasa zancen nasa da sauke idanuwanka kan gashin nata, sosai sukai masa dadin a tafin hannu musamman yadda suke kyalli amma a zahiri sai kara hade fuskarsa da yayi, "ni ban kara komai ba" ta fada muryarta na rawa rawa kamar me tsoran wani abu, kara damke kan nata yayi a hannunsa da karfi,sosai taji zafin yadda ya damki gashin nata ,bata san lokacin da dora hannunta kan nasa ba tana rintse idanuwanta, hawaye ne suka fara zubo mata cikin rawar murya ta soma magana "ka..kayi hakuri", pink lips dinta dake motsawa a hankali ya zubawa idanuwa kusan minti daya ganin tana kokarin bude idanuwan yayi sauri hankad'a ta tafadi a kasa, amaimakon yashiga cikin falon sai ya bar falon gabaki daya, bin bayansa da kallo tahee tayi tana hararar iska ,"arrogant kawai "ta fada cikin sauri kafun ta toshe bakin ta gudun kar wani yaji, mikewa tayi a hankali "ke kuma zan kamakii, sabida kisan halin kayanki shiyasa kika gudu ni kuma aka Huce akai na thank god be ganki ba"ta karasa maganar tana sakin murmushi kasa kasa tare da shafa gashin kanta "wai gashin doki"wani murmushin ta saki tunano kalamansa, lokaci d'aya kuma duk fara'ar fuskarta ta dauke tuno oumma da taheer da tayi, yau kusan sati biyu basuyi waya ba, tunanin hakan yasa ta fara tunanin yadda zata yi Waja da su wajan ammi.

4:30 ammi ce ta shigo falon bakin ta dauke da sallama , har yanxu murmushin fuskarta be 'boyuba, kallan tahee da ke zaune ita kadai tayi, "sorry daughter na barki ke kadai ", itama murmushi tahee ta sakar mata "sannu da zuwa ammi"saida ta zauna tukun na ta amsa mata, mikewa tahee tayi da nufar kitchen bata dade ba ta fito dauke da kara min tray, lemone a ciki masu sanyi gefe guda kuma kayan fruit ne cikin wa ni dan bwol, glass cup din dake kai tahee ta dauka da niyar zuba mata kunun ayar ammi tayi saurin Girgiza mata kai "no daughter ban dade da Shan ruwana ba , bani fruit din nasha ", bata ce komai ba ta ajje cup din tare da miko mata fruit din "nagode "shine abunda tace, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta ce komai ba , kallan ta ammi tayi sau daya kafun ta dauki banana , sai da ta kammala cin bananar kafun ta dauki wayanta, dan danne danne tayi kafun ta dora wayan a kunne ,kusan sau uku tana hakan kafun ta kalli tahee, "yau 3 days ina gwada number yaya amma bata shiga, kiyi hakuri zan kara gwada zuwa anjima sai ku gaisa nasan kinyi kewarsu "sauke ajiyar zuciya tahee tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi dan tunda tazo ammi take kyautata mata kamar yar cikin da ta haifa, kauda maganar tayi ta hanyar sa wata jiran, sun dade suna hiran su cikin raha lokaci  zuwa lokaci ammi na kara wayarta a kunne , kiran sallahn magariba ne ya tayar dasu ,ita ta nufi sama tahee Kuma ta nufi dakin ta, tun jiya take jin wani iri kamar period dinta zaizo, koda tayo alwala sai da ta duba tukunna kafun ta fito, sallahr magariba tayi bata tashi a Wajan ba har saida tayi sallahr isha bayan karatun alkuranin datayi, yau akan daddumar bacci ya dauke ta lokacin da take karatun azkar dinta.

GIDAN AUNTYOù les histoires vivent. Découvrez maintenant