🫧🫧🫧🫧

KANO

UMC ZHAHIR HOSPITAL

Wata kyakkyawar yarinyace me matsakaicin kyau zaune kan daya daga cikin kujerun da aka ajje a cikin dakin asibitin, sosai ta zubawa Wanda ke kwance akan gadon ido, kafun ta fara share hawa yan da suka tarar mata a ido, cikin sanyin murya ta soma magana "Allah sarki ummu na ,Allah ya jikanki da rahma", bata kammala zancan nata ba ta fashe da kuma me cikin rai, tana cikin kukan ne tashi alamun taba kofa , cikin sauri ta goge hawayen da suke zubo mata kafun ta kakalo murmushi a fuskarta, sallama nurse din tayi mata kafin maza wani matashin saurayi ya shigo dakin bayan sa kuma wani kamilllan dattijo ne , drip din da ya kare nurse din ta cire ,cikin girmamawa ta kalli dattijon nan, "insha Allahu ta kusa farkawa a ko Wana irin lokaci ",jinjina mata kai dattijon yayi kafun matashin saurayin gefensa yayi mata godiya, murmushi ta sakar masa tare da barin dakin bayan ta kwashe abin drip din data cire, kujerar da budurwarnan take Kai ta mike tare da sakar wa dattijon nan murmushi "Daddy ga waje ka zauna", binta yayi da kallo kafun ya sakar mata murmushi shima "nagode daughter" cikin takun dattakon ya karasa tare da zama kan kujerar, kallanta matashin saurayin nayi tare da hararar ta cikin tsokana yace "daman nasan yanxu ba kya sona , harda dauke kai kamar ma bakisan dani ba"dariya matashiyar yarinyar tayi "sorry yaya khaleed , kaima kasan inayinka over ", wani hararar ya je famata "daga baya kenan", yana gama fadar Haka suka karasa gaban gadon ,cikin tausaya wa yarinyar ta kalli mahaifin nata" daddy Yaushe zata farka" wani murmushin dattijon ya saki, kafun ya bude bakinsa yayi magana hannun ta ya soma motsawa kadan kadan,kafin a hankali ta fara bude idanuwanta ganin hasken da ya haska mata ido sosai ne yasata rintse idanuwan kafun ta kuma budewa hawaye na bin fuskarta, duk zuba mata ido sukai suna kallanta,"taheer!!taheera", shine sunan da kawai take nana tawa , kallan matashiyar budurwar mahaifinta yayi kafun ya kira sunanta "zahra" cikin Sauri ta amsa da "na'am dady" kallan matar yayi kafun ya kalleta, "tai maka mata", yanxun ma cikin sauri ta amsa "toh dady", karasawa inda take tayi ganin ta na kokarin tashi zauna ne yasa ta temaka mata,tunda ta zauna bata ce komai ba sai bin yan dakin da tayi da kallo,duk abunda ya farune ya shiga dawo mata kai cikin sauri ta zabura "taheer " shine sunan da ta fada tana kokarin sakkowa kasa, kallan ta mutuminnan yayi kafun ya dauke idanuwansa,cikin sanyin murya ya furta "kiyi hakuri kici abinci tukunna inyaso sai muyi magana "katsetsi oumma tayi tana fashewa da kuka "bazan iya ba, ina taheer dina yake , inaso na san halin da yake ciki, su wanene ku, me nake yi a nan wajan", kallanta mutumin yayi kafun ya soma magana cikin kamilalliyar muryarsa " kiyi hakuri ,mune wayanda muka kadeki sati biyu da suka wuce , sannan muka kawo ki asibiti sai yanxu Allah yasa kika farka", waro idanuwa oumma tayi "sati biyu" ta fada cikin rawar murya "kuna nufin satina biyu a asibitin "gyada mata kai mutumin kawai yayi, fashewa da kuka oumma tayi "shikenan na rasashi ", ta kara fashewa da wani saban kukan, kallan ta mutuminnan yayi idan bazaki damu ba zaki iya sanar damu wacece ke , me ya fito dake cikin dare ,naji kina maganar sunan wani da alama wani makusancinki kike Nema ", girgiza kai oumma tayi har yanxu hawayen basu dena zubaba,"zan baku labari na, sannan ina rokon ku da kumayar dani inda kuka dakko ni sabida na nemo yarona", jinjina mata kai dattijon yayi, yayinda mace da namijin suka samu waje suka zauna suma suna binta da kallo ganin yadda take kuka ," sunana maryam ni haifaffiyar buzuwace, 'ya'yana biyu taheer da taheera,mijina Allah yayi masa rasuwa.............." tundaga farkon labarin ta zuwa karshe sai da oumma ta basu tare da dalilinta na fitowa waje,sosai zahra take kuka shima saurayin da aka kira da khaleed shima sai da ya goge kwalla a idanuwansa , sosai suka tausaya mata, gyaran murya mutuminnan yayi "tabbas labarinki abin a tausaya miki ne, Insha Allahu shima yaron naki zamu binciko miki shi da yar dar Allah, amma kafin nan zansa a baki sallama sai muce gidana gabaki daya in kin yadda damu, ni sunana Alhaji kabeer mai zamani, ga babban d'ana sunansa khaleed , sai autata sunanta zahra, mahaifiyarsu kuma Allah yayi mata rasuwa, ina fatan zaki amince", shiru oumma tayi kamar me tunani ganin bata da wani zabine yasa ta amince musu ko ba komai zuciyarta ta kwanta da su", sosai zahra dake sharan kwalla yin farin ciki har hakan ya bawa mahaifinta mamaki, ba a dau dogon lokaci ba aka rubuta musu sallama ganin wanda ya bada umarnin sallamar, cikin kankanin lokaci suka kama hanyar nasarawa G.R.A dake Garin kano.

🫧🫧🫧🫧🫧

Sosai ya ci abincin yanaci yana babbata fuskarsa, yan matan falon sai faman satar kallansa suke ta kasn ido ganin ammi na zaune a falon , kallo daya yayi musu duk suka mike , kallansu ammi tayi, "sai ina kuma " cikin sauri suka hada baki "ammi daman zamu je wajan abeey ne " kallan ammi kawai tayi tare da girgiza kai , suna gita ta kallesa tare da hararansa "ka kyauta da ka koresu" bai ce komai ba lumshe mata idanuwa da yayi tare da mike wa cikin takunsa ya zauna akan kujerar da take ,kansa ya dora akan kafadunta yana lumshe idanuwa, murmushi tasaki tare da zura hannunta cikin lallausan gashin kansa tana masa tausa a hankali "ka rage hade fuskarta nan son , kullum inasan ganinka cikin farinciki kamar yadda nasan ka a baya banasan rashin fara'arka" ta karashe zance cikin karyewar murya , saurin mikewa yayi tare da kamo hannunta,"am sorry ammi na" daga nan bai kara cewa komai ba sai mama tsa mata hannun da yake a hankali, ganin bayasan hirarne yasa ta dakko wani zancen daban, sun dau dogon lokaci suna hirar duk da rabin hirar ammi ce keyi kafin yayi mata sallama, direct part din ummey ya nufa , be wani jima a ciki ba sabida be saba zama ba yana gaisheta ya fito daga part din tare da nufar part dinsa.



🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA

"Aikin ku na kan gangara, baku da dogon lokaci wajan cikar ragowar burinku, watanni biyu ne sukai muku saura ku tabbata kun kawo jininsa,karkuyi saken da Jini biyu zasu hadu waje daya, kuna gab da tafka babban kuskure musamman idan Jini biyun nan suka kasance a waje daya ", a fusace take musu magana cikin bacin rai kafin ta dora "kun tabka babban kuskure kuyi kaggawar gyara abinda kuke kokarin batawa, baku da dogon lokaci kamar yadda kuka kawar da dan uwansa, shima ya zama muku dole Inba haka ba za kuyi kuka da kanku"tana kammala zan centa ta bace bat kamar bata taba wanzuwa ba. Ba Wanda bai razana da maganganun ta ba duk da kasancewar fuskokinsu a rufe yake babu alamar da za a gane mu su wanene, wani mutumine ya soma magana "tabbas yanxu ne ya kamata mu fara aiwatar da shirin mu, duniya ta muce dole mu mulki mutanan duniyar, dukiyar NAHYAN mallakinmuce dole mu karar da tsantsan su"......

Comment and share

Mss Lee 💖💖

Masu comment ina Godiya.....

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now