*MUNIBA*

         A hankali lokaci ya fara tafiya,kwanaki suka fara turawa,biki na sake matsowa Mami sai shiri take yima yaranta,tunda aka tsayar da maganar aurensu,duk weekends Khalidah da Aunty Wahidah basa zama sai sun fita siyayya,su ne aminan Mami ko'ina za'a kuna ko me za'a yi ko siya su take sawa suje su siyo,duk abunda za ta bada biyu² ake kawo mata iri ɗaya hatta color,duk da Muniba da Baniynah suna zuwa school amma kaga wani extra kyau da suka ƙara za ka sha mamaki,sai dai bayan school ɗin babu inda suke zuwa,sai gidan me gyaran jikin da Mami ke kaisu da kanta,kowa a family shiri yake da gaske,sai count down ake na kwanakin da sukai saura,saboda ɗokin bikin kowa yake. A gefen Lieut ma dai da Khalifa suma shirin suke,duka gidajen babu zama don maganar kai lefe ake ta yi,a yanzu shi ne next move wanda daga shi abunda zai yi saura a fara biki bai da yawa. On the other side su kansu amaren ba'a barsu a baya ba,duk wani shawara da za suyi basu da ƙawar data wuce Khalidah sai ko Safwa,duk abunda ake ciki suna kiranta su sanar mata,kuma da ita ake tsara komai,biki ya rage saura 1 month duk wani shiri kusan an gamasa,sai abunda baza'a rasa ba. Kiran da Mama ta yiwa Mami a waya,yasa Mami dake zaune ta sha lulluɓi da babban veil,gefe ga haɗaɗɗen tsadadden handbag ɗinta,hannu ta kai ta ɗauka suka gaisa then suka shiga maganar da za suyi,bayan sun gama ta ɗan yi murmushi,lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalli ƴan matanta da suke saukowa tace "hurry up muje kuna ɓata mana lokaci" Baniynah da ta taho da veil a hannunta tana yafa take cewa "Mami za mu biya ta gidan?" Mami tace "um'um! Gida za mu dawo,me za kuje kuyi a can,bayan duk week sai kunga Maman naku.. Ni ku wuce muje kada yamma yayi mana,kun san Abba zai dawo yau,banda dai na gama abunda ke gabana kuma Khalidah bazai yiwu nace tazo ta kaiku ba saboda kada mu shiga hakkin mijinta da aurenta,ai da ita zance ta kaiku,to na san shiririta za kuje kuyi na haɗa ku" Muniba tayi ƴar dariya kawai ba tare da ta ce komai ba suka fice Mami na masu magana cikin sauri². Cikin week ɗin wanda ya rage 4 weeks to the wedding aka kawo lefe da komai na aure,kayan da aka zubawa both of them zai baka mamaki,set ɗin boxes masu shegen kyau da tsada kowa 4 sets banda wasu adudi da akayi suma cike da kaya,lefe sai kace na ƴar shugaban ƙasa,kuma kamar baza'a mutu ba,kana kallo za ka san kowane gefe sun kashe makudan kuɗaɗe,kuma bikin ba wai na gama garin mutane bane,haka ƴan uwa da ƙawaye sukaita zuwa ganin kaya,Safwa da Radhiya da suka je kallon kayan nan kamar kada su tafi sai santi suke,sun fitar da ankonsu daban² Mama dake harkarta ne ta musu order,zuwa yanzu cards ma da komai sun iso an fara rabonsu ma ƴan uwa na nesa.

*SAFWA*

    Since ta fito masu da chairs biyu ya zauna ya ɗan zame ba normal zama ba ya yi kamar ya kwanta haɗe da miƙa ƙafafuwansa,a hankali Safwa da ta zauna tana kallonsa tayi shiru kamar yanda shima ya zauna ba tare da ya ce komai ba,bayan ɗan lokaci Safwa ta sauke wani ajiyar zuciya mai nauyin gaske and began to say "baby ya kake?" Idanunsa a lumshe ya amsata da "alhmdllh" gyaɗa kai tayi,sai suka sake yin shiru su duka,while Safwa na tunanin yanda za ta sanar masa maganar lefen Muniba da aka kawo yau da kuma kiran da Baba yake masa,idan da hali buri take ace ta samu kamar lefen nan ko sama da haka,but looking at his ɗan madina slippers da jallabiyar jikinsa yasa ta haɗiye wani yahu mai mugun kauri da ɗacin bala'i,tana runtse idanuwanta da suke wani mugun zafi,kamar mai fizgar maganar da ƙyar tace "Baby baka mana murna ba fa,yau an karɓi lefen friend" the way tayi maganar yasa shi fahimtar yanayinta,but duk da hakan ba tare da ya ɗago ya kalli fuskarta ba yace "Allah ya sanya alkhairi" Safwa da idanunta ke kansa tace "ameen.. Saura na mu" ɗago gaze ɗinsa Wazeer yayi ya sauke ƙananan idanunsa a kanta ya kalleta a bit,kafin ya janyesu daga kanta ya sake yin ƙasa da su kamar mai shirin bacci,ba tare da ta yi tunanin zai ce wani abu ba sai kuma taji ya ce "Allah ya kaimu lokacin" cikin ɗan yanayin rashin kuzari ta furta "ameen.." Underneath kuwa cewa take "uhmn! Lallai kuwa.." Suka sake yin shiru kafin tace "yawwa Baby.. Baba fa yace na sanar maka yana son ganinka" Wazeer ya ɗaga idanunsa tare da tsareta da kallo me cike da tuhuma yace "hope ba laifi nayi ba?" Tana girgiza kanta tace "i don't think so.." Yace "when yace yana son gani na? Or kin san dalilin da yasa yace yana nemana?" Safwa ta girgiza masa kai tace "i don't have an idea akan komai.. Kawai dai idan ka samu lokaci sai kazo lokacin da yake nan,almost 1 month fa kenan da ya faɗa min maganar na kasa sanar maka" ya gyaɗa kansa kaɗan yace "ok! Allah ya kaimu.." Suna ta zaune gurin babu me cewa wani komai sai ga Baba ya yi horn,Bilal ne ya fito da keys a hannunsa ya tafi ya buɗe get,Baba ya shigo da motarsa yayi parking,Bilal ya rufe get ɗin da ɗan gudunsa ya ƙarasa gurin motar Baba yana faɗin "Baba sannu da zuwa" Baba ya amsa yana kallon inda su Safwa suke yace "buɗe booth ka shiga da kayan da suke ciki gida" Bilal yace "to Baba" excuse Wazeer ya nema gurin Safwa yace "let me greet Baba" tace "ok" ya tashi ya ƙarasa gurin motar ya yiwa Baba sallama,Baba ya amsa yana kallon yanda ya durƙusa ƙasa yana cewa "barka da dawowa Baba" Baba yana kallonsa yace "barka dai" suka gaisa a mutunce kafin yace "kai ne kake son Safwa?" Wazeer yayi ƙasa da kansa kafin ya ɗan gyaɗa kan nasa yace "ehh Baba" Baba yace "toh! Dama ina ta son ganinka,Allah bai nufa ba sai yau,but duk da haka na bada saƙo a sanar maka almost a month,sai dai na ji shiru,shin ya iso maka ko?" Wazeer yace "ehh! Ka yi haƙuri ban zo ba,ban jima da samun saƙon ba" Baba yace "toh babu damuwa,idan ka samu lokaci,kazo akwai maganar da za muyi" Wazeer yayi shiru kafin ya gyaɗa kansa yace "toh Baba" Baba yace "idan kuma kana da lokaci yanzunma sai muyi maganar" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa yace "toh Baba" Baba ya ɗaga kai ya kalli inda Safwa take yace "Safwa shiga gida ki jiramu za muyi magana" da sauri ta amsa tare da tashi tabi Bilal sukai cikin gida,Baba ya kalleshi yace "mu ƙarasa can mu zauna kada ka gaji da tsuguno" Wazeer yace "toh Baba.." Shiru ne ya ɗan ratsa tsakani bayan sun zauna kafin Baba ya nisa ya fara masa magana cikin taushin murya da kalamai yace "da fari mene ne sunanka ne?" Wazeer da kansa ke ƙasa kamar mace yace "Aliyu!" Baba ya gyaɗa kansa yace "maa sha Allah.. Ashe babban suna ne da kai" Wazeer ya ɗan saki fuskarsa kaɗan sai dai bai dai ce komai ba,Baba yace "Malam Aliyu.. Shin ka san dalilin da yasa nace ina son ganinka?" Wazeer yace "a'a" Baba yace "haka ne.. To dai duka ba kan komai bane illa game da alaƙarka da ƴata,ba zan ɓoye maka ba,akwai wanda yazo yake son aurenta yanzu haka,and he's ready ayi komai cikin taƙaitaccen lokaci.. Sai dai abunda ya hana ban amshi maganarsa ba har yanzu shi ne,saboda ta sanar mana akwai wanda take so,a zamanin da muke ciki ba ka ɗauki ƴarka kayi mata auren dole ba,don kawai mun damu muna son aurar da yaranmu mata,ba sai mun hura musu wuta sun kasa tsugune sun kuma kasa tsaye ba sannan zai sa ka samu abunda kake so.. A'a! Bawa zaɓin yaranmu muhimmanci yana daga cikin abunda zai sa ɗanka yaji daɗi kuma duk abunda kace ta zauna,zai maka biyayya.." Wazeer yace "haka ne" Baba yace "Toh! Alal haƙiƙa Malam Aliyu,matuƙar kana son ƴata Safwa da gaske babu yaudara,lokaci ya yi da ya kamata ka sanar da magabatanka su zo ayi maganar aurenku,idan kuma baka shirya bane ko ba yanzu za kayi aure ba,to ina ganin ya kamata ka dakata da zuwa haka nan,sai a bawa wani cikin masu nemanta dama suma.. Wannan shi ne saƙon a taƙaice,saboda haka don Allah a ƙoƙarta,idan har da gaske kake ba lokaci kazo ka ɓata ma ƴata ba na baka nan da 1 week,ina jira naji daga gareka,idan haka ta gagara to sai dai ayi haƙurin da na faɗa.. Allah yasa mu dace" Wazeer ya numfasa tare da gyaɗa kansa yace "in sha Allah Baba.. Na gode sosai,Allah ya ƙara girma" Baba ya amsa sannan suka yi sallama ya tashi ya shiga cikin gida. Not too long Safwa ta sake fitowa,sanda ta zauna tana kallonsa a sanyaye tace "huh! Ya kuka yi da Babanmu?" Wazeer yayi shiru kafin ya sanar mata abunda ya faru,ta ɗan gyaɗa kanta kaɗan tace "to yanzu ya kake ganin za'ayi? 1 week ɗin da Baba ya faɗa wallahi na san shi bazai wuce haka ba.." Wazeer ya ɗaga idanunsa ya kalleta a hankali yace "and this is ok for me too.. Zan sanar da Babana in sha Allah" Safwa ta gyaɗa kanta tace "ok!" Bai jima sosai² ba yace zai tafi,sukai sallama ta rakashi bakin get.

WAZEER!Where stories live. Discover now