*******

WASHE GARI

Tahee na zaune kan lallausan medium carfet din dakin tana karanta azkar din ta aka kwankwasa kofa , bada izinin shiga tayi, a hankali asabe ta turo kofar bakinta Dauke da sallama sai faman kawar da Kai take gefe , TAHEE na kula da yanayin ta amma batace mata komai tunda itama Allah ya tseratar da ita .gaishe da asabe tayi, duk sai asabe ta tsargu ta kasa cewa komai har tazo fita sai ta Waiwayo kanta a kasa,"uhm dama hajiya ce tace idan kin kammala cin abincin ki same ta a falo", toh kawai tahee tace mata kafun asabe ta bar dakin. Tana kammala cin abincin da aka kawo mata kamar yadda ammi ta umarcetan falo ta nufa, anan ta tarar da ammi na kallo a tv, ammi na ganin ta tamike "Yawwa daman ke nake jira , nasan kowa yana falan dada", da karfi zuciyar tahee ta buga ,  tuno fuskarsa da tayi "nashiga uku , yanxu ya zanyi idan naganshi acan", ammi ce ta katse Mata tunanin da ta fara ,"muje ko"murmushin yake tahee ta saki har ynxu zuciyarta bata dena bugawa ba ,a haka suka nufi part din dada kasancewar hijabi ne a jikinta.

Zazzaune suke a falon dada , sai faman hiransu suke gwanin burgewa , shigowar su ammi ne yasa ko wannansu maida hankali kan har yar shigowa, amrah na ganin tahee take a wajan wani tsanarta ya darsu a ranta, ji take da za ta kashe mutum babu wannan da zata kashe face wannan maiyar. Cikin sanyin jiki ta gaishe da kowa na falon , ganin irin kallan da kowannansu ke binta dashi, sabanin ummey da abeey da fuskarsu ne dauke da murmushi, sai kuma dada dake faman washe hakwaranta. "Zonan kizauna kusa dani"cewar dada , a hankali tahee ta koma kusa da ita , nuna abeey dada tayi "kinga wannan , toh shine babban dana , kuma shine baban yaran gidan, daga yanxu Kema zaki dinga kiransa da abeey kamar sauran", sai musaddiq da uncle Saleem da ta nuna, " wannan kuma Itace babbar maman ku, ana kiranta da ummey, ga kuma matan kawunki musaddiq , ana kiran wannan ta farko mamy sai kuma momy gatanan, sai kuma ta karshen su da ake kira da aunty , ita matar kawunci salim ce, ga yan matan gidan kuma ,duk da nasan zuwanki zaki iya saninsu tunda kullum suna wajan maman yara, bayansu akwai babbar yayarsu dake aure a saudiya sunanta samareena (samreen😂) ana ce mata ukuti( ukhti)zaki ganta wataran,akwai maza guda biyu suna karatu a turai, sai sadauki" tana ambatar kalmar sadauki gaban tahee ya fadi , jitai dada na cewa " zaki ganshi shima wata ran amma kiyi taka tsantsan , ah too in fada miki gaskiya, ga autar gidan kuma can" ta nuna zoya dake kwance kan cinyar ammi tana bacci,kadan tahee ta dago ta kalleta "amma kyakkyawace sosai " ta fada a zuciyarta"Nima akwai yar autata da ban fada miki ba sunanta "zarmeen sai danta kwallin kwal wato mijina sha'aban ".kallan abeey da ummeey tayi "nasan ku ai duk kunsan da zuwan ta ko" eh dada duk suka bata amsa , har yanxu da Sauran guntun murmushi akan kumatun ummey," toh sunan ta tahura" yalwataccen murmushi abeey ya saki "taheera dai ko dada", gyada masa kai dada tayi " au kai da kasan da sunan ma amma sai ka wahalar dani", wani murmushi abeey ya kara saki batare da ya ce komai ba , kallan ta hajiya ameena tayi cikin sakin fuska" gata kuwa kyakkyawa da ita kamar ka sace", sosai ran amrah ya baci da Jin kalaman auntyn tata, ranta ya baci sosai da irin yadda kowa ke karbarta, "Shegiya in ma asiri kikai musu nice zan karyashi " ta karasa tare da binta da kallan tsana bata re da kowa ya lura da ita ba .

*********

**************

Zaune take kan daya daga cikin daddiyar kujerar falon mahaifiyarta, tunda suka dawo daga falon dada take zaune a wajan hannun ta dauke da juice yayin da Dayan hannun nata ke dauke da wayarta sai faman latsawa take , sam hankalinta na kan abunda take a wayarta, jin taku a falon yasa ta saurin fita daga abunda take tare da sassaita nutsuwarta, hajiya hauwace ta shigo falan, tun zuwansu falon dada sai yanxu ne take dawo wa , cikin izza take taku har ta karaso kan daya daga cikin kujerun dake fuskanta sumayya. Murmushi sumayya ta saki, mamy daman ke ce , "nice mana akwai Wanda kike jiran zuwan sane ", tabe baki sumayya tayi ,"toh mamy daga tanbaya, tun dazu nake jiranki fa , amma daga zuwanki kina so ki bata mun fai ", washe baki hajiya hauwa tayi "Haba summy ta ne yayi zafi kinsa Nima wasa nake miki", jinjina kai sumayya tayi" mamy baki kula da yar iskar yarinyar da aka kawo gidan nan ba , ki duba ki gani fa yanda kowa ke kaffa kaffa da ita ko mu da muke jininsu ba ai mana wannan abun ma , musamman dada  da ke faman nanike mata, wallahi in bamuyi wasa ba sai dai mu zama yan kallo a gidan nan , se abunda yar iskar yarinyarcan ta fada sannan za'ai , kina kallanta kinsan ba haka taxo ba , akwia wata kullalliya a kasa , ni tsorona kartaje ta asircemun king, sabida kinga yawanci king acan yake wuni kuma mu ba mu isa shigaba in yana nan, gaskiya mamy ya kamata ki dauki matakin gaggawa, bazan taba bari cikar burina ya tafi a banza ba , inaso nayi suna, inasan duniya ta san da za mana , inasan mallakar king ko ta halin yayane mamy"kin Hana na nuna alamun ina san sa a fili har waccan banzar take tunanin auransa, dole mamy na mallakesa sannan dukiyar gidan nan mu ya kamata muji dadin ta ba wasu ba", ta karashe maganar tare da kurawa mahaifiyar tata idanu, sauke nunfashi hajiya hauwau tayi kafun ta soma magana "tabbas Kinyi gaskiya Nima na dade ina halkanta da hakan , a sannu zanyi maganin kowa dan bazan taba bari dukiyar da na kwallafawa Raina zubucewa ba , aure kuwa kamar anyi shine ". Sallamar ihsan ce ta katse musu zancensu , bin ko wannensu tayi da kallo tare da girgiza kai, tasan halinsu Sarai , fatan ta Allah ya shirya mata su, ganin yadda take bunsu da kallo ne yasa mamy mikewa tare da hararar ta sama sama ,bata jira cewar ihsan din ba tai wuce warts daki, itama sumayyan tashi tayi tare da nufar nata dakin,ganin duk sun watse ne yasata kiran number wayar da tayi saving da my yaya, bugu biyu ya dauka..

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Tunda ta dawo daga part din dada take safa da marwa , ita kadai tasan radadin bakin cikin da takeji, ta tsani yarinyar tsana mafi muni, ko ita lokacin da tazo ba a nuna mata kauna haka ba kamar yadda aka nuna wa waccan , "tabbas sai na lahantaki, lahanin da ko kyawun da akace kina dashi ze gushe, da kanki zaki bar gidan nan", duk wannan zan tuttukan ita kadai amrah take yinxu kamar wata zautacciya, tunani ta fara me zatayi mata da zai kunsasa mata , ta dade tana tsaye a falon kafun ta saki wani shu'umin murmushi, kitchen Dinsu ta nufa, ba a dau dogon lokaci ba ta fito sai faman sakin murmushi take , direct part din ammi ta nufa dan tasan har yanxu su ammi Suna part din dada, ilaikuwa tana shiga bata tarar da kowa ba sai kamshin turare da sanyin  Ac dake tashi, jin motsi a kitchen yasa ta kara sakin wani shi'umin murmushin, ta dau kusan mintuna biyu tsaye a wajan, jin alamun taku kamar za a fito daga kitchen din yasata zuba mangyadan da debo a kan  hanyar da ta san dole koma wanene ta nan zai wuce . Taheee ce ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bottle water tana sha dan ishirwane ya kaita kitchen din, bata san da mutum a falon ba , sai ji tayi an tura ta da karfin gaske, kafarta ta sulleba a cikin man da amrah ta zube, sosai ta saki gigitacciyar kara tare da tafiya Gadan gadan zata fada , ta rotan da taji anyi , a lokaci daya da gigitacciyar marukan da aka suke akan fuskar wanda bata sani ba ya kara girgitata, lokaci d'aya nunfashin ta ya dauke alamun ta suma .



Share ✍️

Littafin gidan aunty na kudine , akan 300 kacal , da zaran na gama free pages dina Wanda suka biya ne kawai zasu dinga samun update , mai don gidan aunty zai iya biyan kudin ta wannan account din 7041879581 opay, Ayshatou galadima sai a turo sheda ta wannan number 07041879581.

GIDAN AUNTYOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz