chapter two

180 9 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 002



                           *1995, AZARE*

Iya Abu ke zaune a ƙofar ɗakinta, tana ƙoƙarin saita rediyo dan ta kamo labaran yammaci. Rediyon sai shiiii shiiii shiiii yake alamar dai ba a kamo setin tasha ba.
Ta sa hannu ta fara bubbuga rediyon dan ta ɗan fara jin alamar magana amma ƙaran ya hana maganar fitowa.

Ta buɗe bayan rediyon batiran ciki sun kumbura har sun fara baƙi-baƙi. Ta ciro su ta ɗan bubbugasu ta sa harshe ta ɗanɗani saman batiran, ɗan garɗin sinadatin acid da ta ji ya tabbatar mata batiran da sauran ƙarfinsu. Gashi rana ta yi sanyi balle ta saka su a rana.  Ta dai sake bubbuga batiran sannan ta maida su cikin rediyon ta kunna. Wani murmushi ya suɓuto mata lokacin da ta ji ta fara jin magana da kyau ba kamar ɗazu ba.

Ta miƙar da ƙafanta kan tabarma tana riƙe da rediyon dai-dai kunnenta. An riga an gama karanto kanun labarai dan haka dole ta nitsu ta ji ko za a ambaci maganar hutun 'yan makaranta.
Ai kuwa cikin labaran da ake ta ji ana maganar gobe za a kammala jarrabawar 'yan Sakandare ta WAEC inda kwamishinan ilimi ke jinjinawa waɗanda suka samu damar rubuta jarrabawar sannan ya musu fatan samun nasara.

Alhamdulillahi ta faɗa, zuciyarta wasai. Nasirunta ya kusa dawowa.

"Salama Alekum" wata yarinya da ba zata fi shekara takwas zuwa tara ba ta shigo cikin gidan.

Iya Abu ta amsa sallamar tana ajiye Rediyonta a gefe

"Iya Abu wai inji Mamana a bani Omo da gishiri"
Yarinyar ta miƙawa Iya Abu sabuwar naira biyar, ta karɓi kuɗin ta shige cikin ɗaki ta ɗauko wata fanteka da ke ɗauke da hoton General Sani Abatcha.

"Ungo" ta miƙa mata ƙullin gishiri da ƙullin omo.
"Ki cewa Mamanki babu canji, ki dawo anjima ki karɓa"

Yarinyar ta karɓi saƙonta ta fice da gudu.

Iya Abu ta gyara zamanta ta shiga lissafta sauran kayan nata. Gobe dole ta aiki Malam ya siyo mata kwanon gishiri a kasuwa saboda ƙulli ɗaya ya rage.
Ta duba  daddawa da kuka ta ga da sauransu. Gishiri ne da sugar suka ƙare.

Bayan ta gama lissafi ta maida fantekarta cikin ɗaki ta shiga madafarsu wanda ke can gefe ta wajen rijiya. Ruwan miyanta ya tafasa ƙwarai yadda take so. Ta zauna a wata ƙaramar kujera ta fara kaɗa miya. Babu nama ko kifi a cikin miyar amma yadda miyar ta ji daddawa da citta da wake gaba ɗaya sai ƙanshi take.

Iya Abu na cikin rarraba abinci yaran gidan suka fara shigowa da sallama sun dawo daga makarantan Allo.
Hauwa'u da Hussaina suka shigo suka gaisheta kafin suka wuce ɗaki. Sauran kam sai da suka shiga ɗaki suka cire gyalensu tukunna suka fito suna yi mata sannu.

Da dare bayan Isha'i suna zaune a ƙofar ɗaki akan tabarma, yaran na cin abinci yayinda Iya Abu ke ta fama da bubbuga Rediyonta. Dole dai ta faɗawa Malam ya siya mata sabon batir.

Iya Abu akwai son jin Rediyo. Rediyon Malam ne amma saboda yadda take amfani da ita sai ya haƙura ya bar mata.  Safe, rana, dare ba zaka raba Iya Abu da Rediyo ba.
Sauraron Rediyo ya rabata da shiga sha'anin 'yan gidansu. Ba zaka taɓa ji wai tana balbalin wata ana gulma da ita ba. Idan Malam ya fita kasuwa, yaran suka je Makaranta Rediyon ke ɗebe mata kewa.

Haruna yaron maƙocinsu ya shigo wai ance ya karɓo tuwo.
Iya Abu ta miƙe ta shige ɗaki ta ɗauko abincin Malam ta bawa yaron. Abincin dare kam tunda ta auri Malam shi da maƙocinsa da ƙaninsa Basiru suke zama su ci.

GENERAL NASEER  ZAKI (Book 1)Where stories live. Discover now