*SAFWA*

      Al'amarin Safwa fa kamar wasa kamar kuma kayan tsafi,tun daga ranar farko data fara amfani da turarukan da Aunty'nta ta aiko mata ta gama ganin abun al'ajabi,ba iya ƴan uwanta students ba hatta da lecturers ɗin su ta yi samari fiye da zato,within few days ta tara samari,don ba ta taɓa fita ta dawo gida ba tare da ta samu samari 5 zuwa sama sun biyota ba,tun daga kan ƴaƴan manya har zuwa jigari² wanda karansu bai kai tsaiko ba,da zarar ta yiwa mutum kallo ɗaya idan taga ba hannunta bane sai ta sallameka,mutum ɗaya take ta ƙwaƙwar son gani,shi kuma kamar bai da lokaci,chart ma da take ɗan ganinsa bai cika hawa ba yanzu,sai yai kusan sati bai leƙa whatsapp ba,sam chart bai damesa ba ba ya gabansa,sukan yi waya wani lokaci shima kuma sai idan ta kirasa ne yaga missed calls ɗinta sannan zai biyo,nan ɗin ma kamar a uzurce zai magana da ita ya katse,abun na damunta kuma yana ba ta mamaki sai dai batai maganar da kowa ba. Yau tunda ta taho gida daga new side take gwada kiransa,wayar na daf da katsewa ya amsa cike da izza me gauraye da gajiya,a hankali Safwa tace "dear how are u doing? These days ban san me ke faruwa ba,ba ka amsa min waya sam bare offline texts ɗina,idan akwai wani abu ne let me know please,ba na jin daɗin yanda kwana biyun nan kake shareni,komai nake ban manta da kai ba,why kake min haka kamar dai bamu san juna ba" shiru Wazeer yayi kamar ya sauka daga layin kiran,Safwa ta ɗaga wayar daga kunnenta tana kallo taga seconds suna reading,da sauri ta mayar da wayar tace "hello!" Wazeer ya sauke numfashi kaɗan yace "kina gida?" Tace "yanzu wai?" Yace "um'um! I mean zan sameki yau?" Da sauri Safwa tace "ehh! Yanzun nan zan koma ina hanya" yace "alright! Muyi waya anjima" wani irin buɗe ido tayi tace "are u for real?" Yace "in sha Allah" Safwa ta washe baki gaba ɗaya murna ya gama cikata,tace "ok! Da wane lokaci za ka zo?" Yace "after maghreeb" Safwa ta gyaɗa kai tace "ok! Sai ka zo.. Bye" tana katse wayar ta saki murmushi,underneath ta shiga lissafin abunda za tayi idan ta isa gida. Tana sauka napep ta sallamesa,da gudu² ta ƙarasa shiga gida,Umma na zaune parlour tana gyangyaɗi Safwa ta faɗo kamar wacce aka koro,a firgice Umma ta tashi tana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,waye haka ya faɗo da gudu kamar an koroshi?" Safwa tayi wurgi da jakarta tace "Umma ni ce fa" Umma ta kai hannu ta ɗauki ɗankwalinta da ya faɗi ta ɗaura,tace "amma wannan ai rashin hankali ne,sai kace ƙaramar yarinya za ki faɗo gida haka kamar wacce wani abu ya biyo" Safwa ta zauna kusa da ita tace "Umma kin san me?" Umma ta kalleta tace "sai kin faɗa" Safwa tace "ina wannan ɗin nan da na baki kuka gaisa a waya rannan?" Umma tace "me ya faru?" Safwa ta sake washe baki tace "shi ne zai zo yau" Umma ta gyaɗa kai fuskarta a sake tace "tou Allah ya kawoshi lafiya" Safwa tace "ameen.. Mmm! Amma Umma ba kya ganin ya kamata a shirya masa wani abu?" Umma tace "ehh! Ya kamata ayi" Safwa tace "to me za ayi masa?" Umma tace "tunda wannan ne zuwansa na farko ai masa dai ƴan abubuwan motsa baki" Safwa ta gyaɗa kai tace "to! Kamar me za'a siyo yanzu wanda babu?" Umma tace "samo takarda sai ki rubuta" jiki na ɓari Safwa ta samo paper sukai making list komai,Umma ta kira Awwal ta aike shi ya sissiyo musu abubuwan da babu,wanda suke da su kuma ta ɗiba suka shiga kitchen,itace ƙarfin aikin Safwa sai dai tayi ƴan small² things,kafin maghreeb sun gama komai tun bai kira ta a waya ba ta tafi tai wanka tai kwalliya,here ta zauna jiran kiransa.

*MUNIBA*

       Wani irin kallon mamaki da tsoro² Muniba ta dunga bin Lieut da ya wani hakimce a motar ta kasa magana,shi kansa haka nan ya karkace kai da kyau ya shiga aika mata wani kallo me gauraye da saƙonni masu girma,Husniyah da su Baniynah babu wanda yai magana suka dunga kallonsu,for about 3 minutes an rasa wanda zai fara yiwa ɗan uwansa magana,sai can su Abrar suka kwashe da dariyar farin ciki,a hankali Muniba tayi saurin kauda kai kunya ya rufeta,Hammad da ya kawo su ya buɗe motar ya sauko yana murnusawa da faɗin "Aunty'nmu! Barka da yamma" Muniba da kunya ya cika ta sake sauke kai ƙasa ta saki ɗan murmushi,a mutunce suka gaisa da Hammad,Lieut Abuu Turab ya buɗe motar ya sauko da ƙafarsa ɗaya ya ci gaba da kallon Muniba da tai bala'in yi masa kyau a ido,irin kallon da yake mata ya hana ta sake ɗaga kai ta kalleshi,cike da dauriya a hankali tace "ina yini?" Idanunsa a kanta ya kasa daina kallonta yace "lafiya lau! Ya kike,how is ur exams da su Mami?" Muniba ta ɗan ɗaga idanunta ta saci kallonsa da mamakin dama ya san tana exams? Sai kuma dai ta amsa da "lafiya lau alhmdllh" suka gaisa da Baniynah kafin ya ɗan kalli ƙannensa a miskilance,ba tare da ya ce da su komai ba Husniyah tayi murmushi tace "Yaa Hammad Mama ta ce mu shiga cikin gida,no need ka tsaya a waje" Hammad yace "ok! Muje mu gaisa.. Yaa Abuu Turab za muje mu gaida Mama" Lieut ya gyaɗa masa kai kawai,daga haka suka wuce suka barsu a gurin,back seat ya buɗe mata yace "get in please ki zauna,u are not a soldier kada ki gaji da tsaiwa,ku mata ƴan hutu ne" Muniba ta ɗan ɗaga ido ta kalleshi,yayi mata sanyayyan murmushi yace "na faɗi wani abu ne kuma akai min kallon nan?" Murmushi tayi da ya ƙara mata kyau,tana sauke idanunta ƙasa ta kauda kai kaɗan tace "idan ni ba soja bace,amma tunda ina tare da soja ai na zama" maganar ya zo masa unexpected,and he couldn't help it ya saki kyakkyawan murmushin da ya bayyanar da dimples ɗinsa,yana lumshe kyawawan idanunsa yace "that means kin amince da wannan military ɗin dake miki naci,right?" Muniba ta kautar da kai gefe tana murnusawa,ya jinjina kai farin ciki all over him ya sauko motar ya tsaya gabanta tare da zuba hannayensa duka biyu a cikin aljihunsa,ya ɗan jingina bayansa jikin motar da bai rufe ba,Muniba dake tsaye sai ta dawo wata ƴar mitsitsiya a kansa,yana kallonta cikin taushin murya kamar ba na soja ba yace "so i'm here dear,na zo jin ra'ayinki a kaina,ina son sanin matsayina da yanda kika ɗauke ni,even though wancan ranar kin sanar min on the phone,but ina son sake tabbatarwa.. Kin yarda kin amince kin bani dama na kafa kaina a gurinki da zuciyarki?" Ƙasa ta sake yi da kanta,a hankali ta gyaɗa masa kai,yayi murmushi yace "i know Abba ya yi miki maganata,right?" Nan ma ta sake gyaɗa masa kai,tace "Mmmm!" Yace "so ya kike gani? Shin na samu gurin da zan ɗan iya raɓawa a zuciyarki?" A kunyace ta gyaɗa masa kai tace "Mmmm" yayi wani lafiyayyen murmushi yace "maa sha Allah! This is the first time da na saurari wani abu da ya faranta min rai tun bayan da na kama aiki.. Ban san da me zan kwantanta abunda nake ji right away ba,but i assure you that ban zo da niyyar ɓata lokaci ba,shekaru suna ta wucewa girma na neman kamani without na ajiye iyali,idan kin amince min and kina jin za ki iya haƙurin zama da ni da yanayin aikina,a shirye nake nan da ɗan taƙaitaccen lokaci na sanar da su Dad ayi komai a wuce gurin.." Muniba dake fidgeting fingers ɗinta ta ɗan ɗago kaɗan ta kalleshi,kamashi tayi ya tsareta da wani mayen kallo,a kunyace ta ɗauke kanta tace "ni ka bar kallona haka" ya buɗe ido da kyau yace "whatttt?" Tace "Mmmm" yayi murmushi yana leƙa fuskarta yace "Muniiy! Look at me ki sake faɗa" tace "um'um! Ni dai ka bar kallona haka,kunya kake sawa ina ji" ya buɗe ido da kyau yace "kunya? Nawa wai?" Ta gyaɗa kanta tace "Mmmm" yace "don't be shy please,idan kina jin kunya ta yaya za mu fahimci juna?" Tace "to ka rage" yayi murmushi yace "a'a sai dai na ƙara kaɗan" kwaɓe fuska tayi tace "zan yi kuka" yayi wani murmushi yace "na iya rarrashi babu matsala" ta saki wani murmushi me cike da kunya,shima yayi murmushin yace "thanks for the smile and chance,Allah yasa tarayyarmu ya zama alkhairi" a hankali tace "ameen.." Hira ya ɗan dunga janta da shi,sun jima a gurin kafin ya ɗago hannunsa,tsadadden agogon dake ɗaure wrist ɗinsa ya kalla ganin 6pm ya kusa,yace "i think ya kamata su fito mu wuce" Muniba tace "baza ka shiga ba? Ko fa ruwa baka sha ba" yayi murmushi yace "next time dear" ta ɗan gyaɗa kanta kaɗan tana shirin cewa za taje tai musu magana,ya kira Hammad a waya,yana ɗauka yace "Hammad ku fito mu wuce ko?" Daga haka bai jira me Hammad zai ce ba ya katse kiran,yana ɗan danna wayar dake hannunsa ba tare da ya kalleta ba yace "we are going dear,yaushe zan sake zuwa na ganki?" Muniba tace "anytime" yace "a bani rana da lokaci" tace "i'm available,ba na zuwa ko'ina" ya ɗago ya kalleta,yace "wait.. Anya kin je gidan Mohan kuwa?" Ta girgiza kanta kaɗan tace "a'a!" Yace "me yasa?" Tace "ai basa nan,kuma ko bayan haka ina exam ba na fita" ya gyaɗa kansa yace "idan sun dawo ki shirya za muje musu yini" tayi ɗan murmushi tace "Allah ya kaimu" ya amsa,fitowar su Hammad yasa yace "sai mun yi waya?" Tace "Mmmm! A gaida min Mom,Allah ya tsare ya kaiku gida lafiya" yace "zan faɗa mata in-law ɗinta na gaisheta" tayi murmushi kawai ba tare da ta sake cewa komai ba,su Baniynah na isowa sukai sallama,Husniyah tace "Aunty kinga abunda Mama ta bamu,a yi mana godiya" Muniba ta gyaɗa mata kai fuskarta da murmushi bayan ta kalli babban ledar dake hannun Abrar tace "in sha Allah" Hammad yace "Aunty'nmu za mu tafi,sai wani lokacin in mun sake zuwa" Muniba tace "na gode sosai da ziyara Yaa Hammad,a gaida Mom da kowa" yayi murmushi yace "mu ne da godiya Aunty,za su ji in sha Allah.." Basu jima sosai ba sukai sallama da su suka shiga mota suka wuce suna waving juna ita da su Abrar.

WAZEER!Where stories live. Discover now