Sun dau dogon lokaci suna d'ebo ruwan , lokacin har oumma ta kammala share tsakar gidan da ya dawo kamar bashine me tarkace ba. Tulun kayan wanke wanken suka hada 'kuda sai faman bin kwanukan suke, sundau dogon lokaci suna wanke kwanukan , dadin su daya ma haduwa sukai su duka suka wanke dan ba karamun kwanuka aka bata ba ,gama wanke wankensu ba dadewa aka kawo markadan wake , zama tahee tayi ta buga wannan kullun, yayinda oumma ke hura jikakken ican da aka jika duk idanuwanta sunyi ja sabida yadda hayakin ya cika mata ido.

Duk wannan abun da suke mutanan gidan sai faman kai kawo suke , ba wanda yace dasu ko sannu sai ma banzan kallan da ake binsu dashi da hantara.basu suka kammala ba sai wajan karfe shadaya,ragowar guntun dumamen tuwan jiya kaka ta bawa ta mikowa oumma," kar alashemu ace bamu baku abinci ba ko akai mu duniya" cewar kaka tabawa ,kallan tuwan da baifi cin mutum daya ba oumma tayi, batace komai ba sai ma daki da ta nufa , anan ta samesu sai faman sauke nunfashin yunwa suke ,kwallace ta tarar mata , ganin suna kokarin mikewane yasata saurin goge idanuwanta kada suga rauninta, tuwan da ke hannunta ta ajje musu, cikin sauri suka mike tare da wanko hannayensu,har sun saka hannu zasu fara ci sai suka fasa tare da zubawa oumman tasu idanu,sarai ta fahimcesu amma ko motsawa batayi ba, langwabar da kai sukayi kamar wasu yara oumma suka kira sunanta , girgiza kai kawai oumma tayi tare da mikewa tare da zama a tsakiyarsu.taheer ne ya kutsuro tuwan tare da kallan oumman tasu "oumma haa" dariya duk suka saki ganin yadda ya bude bakin nasa , cikin kulawa yasa mata tuwan, itama taheera saka mata tayi a baki, hannu oumma ta saka itama ta fara basu a baki , duk da tuwan bashi da yawa amma haka ko wannansu yasamu yaci , cikin farin ciki da kaunar junansu.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

10:20 pm motarsu ta danno kai cikin gidan , kamar ba dare ba har yanxu akwai hasken futullu da ya haska ko ina na gidan, daya daga cikin building din gidan zaki yayi parking , ya dau kusan 2 minutes zaune a cikin motar idanuwansa a lumshe kamar meyin bacci, a hankali ya zuro da kafarsa guda daya kafun a hankali ya juro da gaba dayar kafar tasa yana mikewa,cikin takunshi me kama da na izza ya fara tafiya tare da nufar kofar da zata sadashi da babban falon building din.Babban falo ne me kirgan gaske da ya cika da tsadaddun furnitures na alfarma , iya haduwa falon ya hadu ba abudna yake tashi sai daddadan kamshi da sanyin ac, ganin bata falon yasa ya juya da niyar komawa, foot steps dinta da ji ne yasashi tsayawa kafun ya juyo a hankali,murmushi ta sakar masa"son " be amsa ba sai ma zuba mata kyawawan idanuwansa da yayi, sannu a hankali ta karaso wajan, sanye take cikin hijab hannunta dauke da tasbaha sai faman sakin murmushi take , sau da ta karaso inda yake kafun ya bude baki a hankali kamar wanda magana take wa wahala, cikin cool voice din shi me shegen dadi ya kira sunanta "Ammi,"hararar wasa ta jefa masa"sai yanxu ka tuna dani"lebensa ya motsa kamar me sanyin magana sai kuma ya fasa tare da dauke kansa, kamo hannunsa tayi tare da zaunar dashi kan daya daga cikin kujerun falon,"oya zauna ka ci abinci nasan yau kwata kwata ba abuncin kirki kaciba , na kusa yi maka aure kwanannan ko zaka shiga taitayinka",bece komai sai hade fuska da yayi tare da kau da kansa, murmushi ta sakar masa "mai da wukar son wannan hade rai haka, nima wasa nake maka , ai samun wacce zata siyo zuciyar ka sai anshirya "a jiyar zuciyar da ko ammi dake kusa dashi bataji ba ya sauke tare da sassauto da fuskar tasa kadan . Abincin ta dakko masa da kanta tare da jerasu can center table din gabansa,zubawa tulun abincin data ajje a gabansa idanu yayi sai kace mutum goma zasu ci, bece komai ba sai idanuwansa da ya zuba mata ,sarai ta gane me yake nufi"duk suna part din dada tunda kai cin abinci cikin yan uwan naka ne bakaso", lumshe fararan idanuwansa yayi, itama ammi bata kuma cewa komai ba sai abincin da ta zuba masa cikin hadaddan plate din da ta dakko, "oya haa" bude lumsassun idanuwansa yayi tare da kallanta, yanda tayinne yaso bashi dariya amma kwata kwata be yitanba, a hankali ya bude bakin nasa ta fara feeding din nasa , 7 spoon yayi tare da kawar da kansa,"son karkace mun kakoshi"lumshe mata ida nuwansa yayi, girgiza kai kawai ammi tayi tare da dakko masa hadaddan kunun ayar da tayi masa, sosai kuwa yasha kudin ayar bayan ya kammala shane ammi ta mike, "oya tuzuru aje a kwanta sea da safe", bai ce mata komai ba sai mikewar da yayi , dariya amminta saki"bani na kar zoman ba rataya aka bani"inda sabo ta saba da halinsa na kinson yin magana tunda tasan halin kayanta,"Ammi sai da safe " ya fada cikin husky voice dinsa, side hug tayi masa , Allah ya tashemu lapiya ka kwanta da wuri dan na san ka gaji, jinjina mata kai yayi alamar toh tare da ficewa.

Har yanxu zaki na waje kikam kamar bushiya , inda ya barsa anan yazo ya samesa be ce masa komai ba , shima zakim bude masa kofar mota yayi, cikin takunsa na kullum ya nufi motar, haryasa kafa zai shiga sai kuma ya daga idanuwansa tare da kallan wani building sai kuma ya lunshesu tare da shiga cikin motar, daidai part dinshi zaki yayi parking yanxun ma shine ya bude masa kofa . "Sai da safe king"hannu king ya daga masa kabar bazai ce komai ba sai kuma ya bude baki a hankali "good night". Murmushin jin dadi zaki ya saki be bar wajan ba har saida yaga shigewar king sannan shima ya barwajan.

Direct yana shiga part din sama ya hau ta elevator , yana shiga dakin rawanin kasansa ya bayyana,kofar da zata sadashi da toilet ya nufa, ya dau mintuna a cikin toilet din kafun ya fito da wasu white pj mas masu laushi , imperial majesty ya fesa , dakin ya kara dauka da kamshin turaransa da ke kama daki,kan gadan sa ya nufa kai tsaye cikin luntsumeman gadansa, har ya kwanta sai kuma ya mike tare da dakko wasu magun guna .maganin hannunsa ya sha tare tare da bude bedside drawer. Har ya bude zai zubasu idanuwansa suka sauka kan wani hoto dan karami, daukan hotan yayi tare da zuba masa ido . Wasu matasan larabawane a jikin hoton sun rike hannun junansu, kana ganinsu kasan ba karamun kaunar junansu suke ba. Sauke ajiyar nunfashi yayi tare da mayar da magun gunan, shima hotan mayar dashi ma a daninsa yayi tare da danna wani remotes take futulun dakin suka dauke , wasu kaloli masu kyau da haske suka fara cika dakin me kama da dim lights , sannu a hankali bacci ya daukeshi.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Comment and share

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now