page 11

240 14 3
                                    

*KWARYA TA BI KWARYA*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 11*

            Past

Habu da fashashen baki ya bi Yaya Ibrahim cikin gidan da yaji Yana jijjiga k'ofa da k'arfi

Dan daki Zinatu ta shige da balain sauri jikinta na rawa,dan haka kawai Allah ya saka mata tsoronsa,dan ko Habun ma shakkar sa yake.

Yaya Ibrahim kuwa jijjiga k'ofar yake Yana "Ki Bud'e idan kinsan kin cika cikakkiyar Yar iska wallahi sai na sumar dake inya so Habun idan yasan shi din dan Halak ne ya kuma haifu ya sa a kulleni nima"

"Yaya Ibrahim kasan mai Sulen yamin ne da zaka zo ka shigar masa har baka ji ta bakina ba ka rufeni da duka"?

"Habu Hala kudin da kayi hauka ya saka ka da rashin Hankali,da irin wanan kudin naka wallahi Habu gwara ma zama a cikin Talauci wai har akan Sule ya tab'a Maka mata zaka kulle Sule yanzu tsawon sati uku da kwana hudu,kanka daya kuwa Habu ko dai kana shaye shayene?Sule kaninka da kuke uwa daya uba daya kasa aka kulle dan kawai ya tab'a matarka?

"Kai yanzu zaka yarda na tab'a lafiyar matarka Yaya Ibrahim?sau biyu sule na tab'a min mata,na farko fyade yaso Mata na biyu Kuma ya so ya makantar min da ita,wallahi Allah ne ya takaita da yanzu Zinatu bata gani,haka kawai zai Sako min Mata a gaba,kaga dukan da yayi mata"?

"Yanzu dai ka zabi matarka akan dan uwanka,yanzu dai akan matarka ka daura damarar wulakanta dan uwanka saboda kawai kana da kudi?kana wajen a lokacin da Sulen ya daketa?,uban mai ya kai ita Zinatun gidan Sulen?duk baka yi bincike ba matarka ta zo ta tsara Maka karya ka hau kai ka zauna Habu?dan kawai kana da kudi kake tunanin zaka taka Wanda ranka keso har da dan uwanka a ciki?a kaddara a gaske Sulen ya daketa,idan matuniyar arziki ce ita zata so ka kulle shi?har wai ka gudu saboda kar ma a roke ka sake shi ko"?

"Yaya Ibrahim so kake kaima kawai ka goyi bayan Sule,amma ko Kai sule yayi wa matarka abinda yayi wa Zinatu wallahi sai ka d'auki matakin da yafi nawa,kaga fuskar Zinatun a lokacin da ta dawo zagewa yayi ya ringa dukanta kamar ya samu Dan uwansa namiji"

"Kana wajen ne Habu ka tambayi tsinanniyar matarka abinda tayi wa sule kafin ya kai hannu Jikinta"?

"Gaskiya Yaya Ibrahim Ina ganin girman ka Ina baka girman ka a matsayin ka na yayana ya kamata ka ja girmanka dan idan Kai Sule yayi wa abinda yamin wallahi sai kayi Abunda yafi nawa gaskiya ka daina tsinewa matata har cikin gidana kazo kana dukana,shikenan dan Ina da kudi Allah ya rufa min asiri zaku hada min Kai duk abinda nayi ba mai goya min baya sai Sule kuke goyawa baya"

Kallonsa kawai Ibrahim yake Yana Jin wani irin b'acin rai na Kara taso masa Yau ban da Gwaggo na cikin matsanacin hali da ba zai tab'a taka kafarsa yazo wajen habu ba,dan daga lokacin da yaga ya dorawa kansa wani girman Kai dan kawai yayi kudi ya tattara shi ya watsar,Wanda hakan da yayi na Jan girman sa yasa Habun ke shakkarsa.

Duk da ba kudi ne dashi ba Shima buga bugan yake cikin rufin asiri hakan yafiye masa da dai yazo neman wani abu a wajen Habu

Cikin wani irin murya ya fara magana Yana "Habu kayi asarar rayuwarka idan har akan mace da zaka iya canza ta sau dubu,zaka kulle dan uwanka da baka Isa canja shi ba,zaka jefa mahaifiyarka a cikin mawuyacin hali har silar abinda kayi mata ya Kai ta da kwanciya sai dai a kwantar a tayar,Kai ma kasan idan ba dan ka kulle Sule ba wallahi baka isa ka ga kafata a gidanka ba,dan ko duniya kake dashi Habu wallahi ba abinda zan zo nema a wajenka,banga kudin da kake dashi da har yasa ka dorawa kanka wani girman Kai,a yanzu rayuwarka na cikin mugun hatsari da ka hau motar da zata jefa ka cikin masifa na kudi da mace,daya daga ciki kawai idan baka dace ba zai kai ka ne ya baro balle har da ka hada biyun kana wulakanci saboda kana da kudi,ka fifita matarka akan danginka, Habu wallahi sai kayi nadamar wanan abun da kayi ka rubuta ka ajiye mu din da ka raina ka fifita tsinaniyar matarka akan mu wallahi watarana sai ka neme mu idan a yanzu ba zamu Maka amfani ba saboda kawai bamu da kudi watarana sai kudinka sun gaza maka abinda Yan uwanka zasu ma idan  har ka sa aka  saki Sule Kai din ba dan Halak bane ba"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 24, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KWARYA TA BI KWARYA Where stories live. Discover now