page 2

189 5 1
                                    

*KWARYA TA BI KWARYA*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 2*

Present

      Ameera yi tayi kamar bata ji shi ba ta cigaba da tafiyarta zuciyarta na san tilasta mata juyawa ta kalleshi a zahiri ba mafarkin da ta saba ganin sa ba.

Tana dab da tura k'ofar taji Anne na kwalla mata kira akan "Ameera baki ji Yayanki na magana ba"?

Sai da ta hade rai ta juyo fuska ba wani faraa har ya karaso wajen da take tsaye fuskar sa a washe Yana "Kanwata kina kallona kika d'auke kanki baki gani bane"?

"Yaya Amjad Ina wuni ya taro"?

Ameera tace kanta a kasa zuciyarta na bugu da ganinsa a gaban ta rabonta da shi tunda ya fita waje karatu

Murmurshi ya saki ganin Anne ta shige yasa ya dan matsa kusa da ita Yana "Ameera mai yasa baki tab'a nemana ba"?

A yadda yayi maganar yasa ta dago suka hada ido ta Kara Kau da kanta da sauri ta tura k'ofar tana "Bari na shiga ciki Yaya Amjad dan ba dade wa zamu yi ba"

Ameera da jikinta ke rawa ta shige da sauri tana Jin Yana kwalla mata kira da dan gudu ta tadda Anne dake dab da shiga cikin gidan.

Harabar gidan a cike da motoci kamar wajen siyar da motoci kaf gurin babu karamar mota.

A cikin sakani ta karewa gidan Kallo tana tuna irin rayuwar da suka yi a gidan duk da sauye sauye da canji da aka samu na zamanantar da gidan da akayi.

Tamke fuskarta tayi a lokacin da suka samu wawakeken palon da manyan mata ke zaune leshi na dukan leshi kamar gasar gwal ake dan duk kawayen Hajiya Zinatun sai walwali suke.

Anne jikinta rawa ya d'auka dan Sam bata ga kalarta a wajen ba sai taji ta muzanta ma da zuwan da suka yi ganin duk suna zaune akan kujera tuna Kuma wacce Hajiya Zinatun yasa ta fara k'ok'arin samu waje a kasan kafet ta zauna daga can gefe dan kadan da aikin Hajiya Zinatun ta ce su sauka kasa su zauna.

Ameera kuwa da sauri ta rike mata hannu tayi kasa da murya tana "Anne ya naga kina neman zama a kasa"?

"Ameera nima ban manta Hajiya Zinatu ba kar tazo ta disgamu a gaban mutane tace an hau mata kujera dan haka mu zauna a kasa idan ta fito muka mata Allah ya Sanya alheri sai mu tafi"

Ameera girgiza kanta tayi da sauri tana "Anne ba zai tab'a yuwa ba wallahi ba zamu zauna a kasa ba shi yasa tun farko da kika matsa min ke da Abba akan mu zo nace ba zan zo ba dan gudun irin wanan wulakancin dan haka tunda har muka zo wallahi Anne a saman kujera zamu zauna duk Wanda ya nemi ya wulakanta mu wallahi nima sai na wulakanta shi dan Allah ki zauna a saman kujera"

Ameera tace tare da samawa kanta wajen zama Anne sai da tayi Jim ta zauna a gefen Ameeran tana wurga ido da karewa palon Kallo dan itama ta jima rabonta da gidan Kuma gidan ya canza sosai ba kamar sanin da tayi masa a baya ba.

Daga ita har Ameera kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa duk sun tafi Tunanin rayuwar da suka yi a gidan.

Fitowar Amrah Amarya daga wani daki yasa Anne washe fuskarta dan idonta kyar a kansu ta Sha ado da wani material tana ta zabga kyalli gefenta wata ce itama da alama kawarta ce.

Ameera kuwa d'auke kanta tayi da ta mata Kallo daya duk da ta girme mata nesa ba kusa ba fuska a balain hade tana ta tunanin rashin kunyar da zata mata dan gani take ko Alhaji Habun  ne ya takata ba zata bar shi ba.

Suna zaune wajen Kujerar  dake bakin k'ofa.

Amrah kuwa wani irin Kallo ta musu kamar taga wani abin kyama ta d'auke kanta tana tunanin ko waye ya gayyace su.

KWARYA TA BI KWARYA Where stories live. Discover now