page 8

147 15 2
                                    

*KWARYA TA BI KWARYA*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 8*

Kawar Zinatun hannunta ta jawo ta mai data ta zauna tana "Zinatu mai haka zaki tara mana mutane kamar ya saukar zuku tayi kinsanta ne"?

Zinatu da bama tasan ta mik'e tsaye ba tsabar tashin hankalin da ta shiga da ganin wai Ameera akayi ta zubawa wanan uban kyautatukan,tama d'auka a zuci tayi maganar bata san a fili tayi magana ba.

Kanta har wani Sara mata yake tana cigaba da Jiyo kabbarar da ake daga gidan gaba da kyautatukar da Ameeran ke ta samu.

yaushe har aka haifi Ameera da ta isa sauke Qurani gabad'aya,har wai a ringa zuba mata wanan kyautatukan idan kunnenta daidai ya Jiyo mata kamar Kujerar Hajj taji za'a biyawa Sule da Hanne,bayan ita ko zuwa ba ta tab'a yi ba.

Ganin idan ta cigaba da zama zuciyarta na iya tarwatsewa yasa ta mik'e tayi wajen da tayi parking din motar ta,hararo sule da Hanne kawai take a jirgi bayan ita bata tab'a hawa ba.

Kawarta kuwa sai kiranta take amma ko ta kanta bata bi ba.

Tana tuki tana yarfa gumi,canjin rayuwar da Sule ke neman samu da Hanne ya matukar daga mata hankali,ko kusa ko alama bata san su samu wani hanyar cigaba tafi so duk dangi ace Babu kamar ita da mijin ta,tafi so ace duk dangi ba wayanda suka je kasa mai tsarki sama da ita da mijinta,babban burinta shine taga taje saudiya ta ganta da fararen hakoran macca guda biyu, tasan tana zuwa ta gama zama hajiyar da take so ta zama,sai gashi wayanda ta raina bama ta kawo su a sahun mutane da zasu tab'a Jiyo kamshin Airport balle har wai suje saudiya a gaban idonta aka ce zaa biya musu ba iya su ba har da Ameera.

Har fadawa Rami tayi tsabar tunanin da ta tafi tana yi.

Ko da ta isa gidan a gaban tv ta tadda Su Amrah suna Kallo kamar yadda suka saba aikin kenan idan har suka dawo daga boko,a sati bai fi sau biyu suke zuwa islamiyya ba.

duk Kuma bata damu ba dan gani take boko shine kan gaba akan islamiyya dan sai kayi karatun boko zaka iya zama cikakken mai kudi kamar yadda take hasaso Amjad a matsayin babban likita,Amrah a matsayin wata lecturer, Yaranta gabadaya dai da wani babban Matsayi.

Sai gashi wai Islamiyya da Ameera taje silarsa wai su Sule zasu tafi saudiya ga kyautar kudi da gida dan sauran ma bata iya jiyowa sosai ba saboda tashin hankalin da ta shiga.

Sam basu san da ta shigo ba sai labartawa juna labarin film din suke.

Sultana da take kusan sa'ar Ameera ta kurawa ido tana hararota a bainar jama'a tana zuba karatu cikin kira'a mai Dadi kamar yadda Ameera tayi dazu.

sultana tafi dacewa da wanan kyautatukan ba Ameera ba.

yanzu Ameera tafi sultana ta wani wajen kenan bayan su din suna da kudi.

Kamar wacce aka yiwa duka haka ta karasa kan kujerun.

kanta, zuciyarta komai na jikinta ciwo kawai yake mata tana jiyo muryar Wanda yake bayanin zai biyawa Sule da Hanne Kujerar Hajj a kunnenta.

Sai a lokacin su Amrah suka lura da ta dawo.

Bata sabar musu da gaisuwa ba shi yasa suka d'auke kansu.

A wani irin tsawace tace "Ku kashe min kayan kallon nan kuzo nan gabad'ayan ku"

Ido suka zuba mata dan bata sabar musu da haka ba

Sai da ta sake daka musu tsawa suka kashe kallon suna turo baki da tambayar su mai suka yi ne.

Sai da suka jeru a gabanta ta tuna bata ga Amjad ba tun safe

KWARYA TA BI KWARYA Where stories live. Discover now