*SAFWA*

      Tun a daren Safwa dake online har guraren 1am taga text ɗinsa,bayan ta gama karantawa ta saki murmushi sosai tare da tura masa "and idan ka zo,ka tabbatar bakai min ganin nesa ka tafi ba,sai bayan nan sannan kace ai ka zo,idan kayi haka zan ɗauki zuwanka da wanda bai zo ba ɗaya.. See yah later.." Sanda ta tura masa good night text kamar yanda ta saba,sannan tayi offline ta ajiye wayar ta kwanta bacci. Da asubah ko da suka tashi dukansu,suka shiga bathroom suka yo alwala,suna idar da sallah bayan sun yi addu'o'insu suka hau hira,Muniba da taga babu me niyyar kama wani aiki su ragewa Umma wahala,ta tashi ta fara gyara ɗakin,tana gamawa ta wanke bathroom sannan ta fita ɗakin ta share mini parlour dake sama har zuwa staircase da parlour,tana gamawa ta kunna turare tasa,nan da nan parlon ya ɗauki ƙamshi,Umma data fito ɗakin Baba tana saukowa saboda ɗora abincin safe,taji ƙamshi ya baɗe ko ina,tayi murmushi tace "amma kuwa Allah yima wanda yai aikin nan albarka ko wane ne" tana maganar ta nufi kitchen za ta ɗaura tea,sai taga Muniba tana haɗa wanke² a kitchen,fuskarta da murmushi akai tace "a'a Muniba,ba dai ke kikai duka aikin nan ba?" Muniba na murmusawa ta durƙusa tace "ina kwana Umma?" Umma tace "lafiya lau.. Kun tashi lafiya?" Muniba tace "lafiya lau" Umma tace "ina Safwa? Ta barki kike ta aiki ke kaɗai haka?" Tana maganar ta buɗe murya ta fara ƙwala kiran "Safwa! SAFWA!!" Safwa dake ɗaki zaune sai chat da zuba hira take,ta tashi da sauri ta fito tana amsawa,tana saukowa ta shigo kitchen tana cewa "ga ni Umma" Umma na mata wani kallo tace "kina can kina riƙe da waya kina sanar naki,ita kuma tana nan tana yima uwarki aiki,ke ko kunyar azo gidanku aga ina maki aiki ma baza ki ji ba,wace irin mace ce ke kam?" Safwa tace "kai Umma dan Allah" Umma tace "kai Umman ubanki.. Ina magana kina ce min kai ɗin nan,wata rana sai na fasa maki baki.." Safwa tace "Allah ya baki haƙuri" Umma tace "ameen.. Sai ki wuce ki yi min wanke²n data haɗa" Safwa ta zaro ido tace "wanke² kuma? Umma na fa yi lalle" Umma tace "wallahi² sai kin yi min wanke² za ki bar gidan nan,idan ba haka ba Allah kaɗai zai raba ni da ke yau" tana kallon Muniba tace "je ki huta Maryama.. Allah yayi miki albarka,ya baki wanda za suyi miki" Muniba tace "ameen Umma" tana kallon Safwa da tai kicin² tace "muje nai miki ɗauraya" Safwa ta turo baki tace "ni gaskiya bazan iya wanke² lallena ya yi fading ba" Umma dake kunna gas ta juyo a fusace tace "Muniba yi tafiyarki sama cikin ƴan uwanki,wallahi² ita kaɗai za tayi wanke²n nan" Muniba ta gyaɗa kai tace "tou Umma" daga haka ta tafi,Safwa ta dunga kallon Umma daga inda take tsaye,ji take kamar za ta ɗora hannu aka ta kurma uban ihu,Umma data tirketa a kitchen ɗin tace "duk fa yanda za kiyi² amma wanke² sai kin yi min shi.. Ai ni ba baiwar ubanki bace da zan dunga girkawa ina baki kina ci daga kwance ki jefeni da kwano na wanke maki.." Safwa ta juya za ta fita daga kitchen ɗin bayan ta gama yanke shawarar yanda za tayi,Umma ta juya ta kalleta a fusace tace "Safwa dawo nan ina za kije?" Safwa ta turo baki tace "zan yi fa Umma" Umma tace "ok! Yanzu naji batu" daga haka Safwa ta bar gurin,sama ta tafi ta ɗauko handglobe sannan ta sauko,tana shiga kitchen tasa a hannunta ta fara wanke²n,Umma dake tsaye kanta ta taɓe baki,tunda dai za'ayi mata wanke²nta shi kenan ba ta da sauran damuwa.

*MUNIBA*

      Muniba na haurawa sama ta buɗe ƙofa da sallama,Khalidah na kallonta ta buga tagumi da hannu bibbiyu tace "sannu Sweetheart.. Kin je neman sunan naki kou?" Muniba na dariya ta nemi guri ta zauna tace "kai Yaa Khalidah,ɗan taimakawa Umma da nayi" Khalidah ta watsa mata wata uwar harara tace "dallah tafi can.. Sai ki tashi kije kiyi wanka,ai kin san za muje ku rakani make-up,amma dan wulaƙanci kika fita kika kama aiki kamar an sa ki" Muniba tace "toh! Bari nayi sauri" gudun aita mata faɗa yasa ta tashi ta fara cire kayanta,Baniynah ta taɓe baki tace "ai wallahi ko ni baki ji haushin data bani ba kamar zan rufeta da duka,kawai dan babu yanda zanyi da ita ne na ja bakina nayi shiru,ita ƴarta baki ga neman guri tayi ta zauna ba,sai ke agogo sarkin aiki,ki wani kama ki fita ki kama aiki kamar kece aka zo gidanku,da wannan son aikin naki me zai hana kice da Mami ta sallami duka househelp kawai sai ki dunga yi" Muniba da bata ji haushin maganganunsu ba ta fara dariya,Khalidah tace "c'mon wuce kiyi sauri ni dai" tana ci gaba da dariya ta wuce bathroom ɗin Umma,tana shiga ciki babu jimawa Bilal ya yi sallama,Khalidah suka amsa tace "shigo Bilal" yaron me hankali da nutsuwa kamar ba ɗan gidan ba,ya shigo ya ɗan durƙusa yace "Yaa Khalidah ina kwananku?" Khalidah tai masa murmushi tace "ka tashi lafiya?" Yace "lafiya lau" Baniynah na kallonsa da murmushi a fuskarta tace "surukina" a kunyace ya ajiye flask ɗin tea da Umma ta tafasa tace ya kai musu,Baniynah tace "auu! Baza ka kulani ba? Zan fasa baka ƴar tawa fa" a kunyace ya fita ɗakin kamar mace yana dariya,a karon farko Khalidah tayi dariya tunda suka zo gidan tace "Bilal zo mana" ya tsaya daga bakin ƙofa yace "ga ni" Khalidah tace "auu! Baza ka shigo ba?" Yace "ai kunyarta nake ji" Khalidah tace "ita Baniynar kake jin kunya?" Ya gyaɗa mata kai yana murmushi,ta buɗe manyan idanunta tace "toh shi kenan,jeka tunda ni baka jin kunyata" da sauri yace "a'a ina ji.. Amma ba kamar ita ba" Khalidah tace "a'a baka wani jin kunyata.. Amma shigo na tambayeka" da ƙyar ya shigo ɗakin ya tsaya bakin ƙofa,amma ya ƙi kallon Baniynah sai sinne kai yake,Baniynah sai dariya take tana tsokanarsa,Khalidah tace "wace ƴar tata za ta baka ne?" Baniynah tace "first daughter ɗin Sis Muniba mana" Khalidah ta fara dariya tace "tofa! Tun ba'a haɗu da uban ƴar ba,har an fara alƙawarin bada ita?" Baniynah tace "bari kiga ta fito daga bathroom,bazai iya kallonta ba sam.. Idan yana gidan nan fa muka shigo da ita guduwa yake,ai ko yanzuma dan bai san tana nan bane ya shigo" kafin ta gama magana yai wuff ya bar ɗakin,Khalidah na kiransa bai dawo ba,Baniynah ta dunga dariya har da ƙyaƙyatawa,Muniba na fitowa wanka ta kalli Baniynah tana girgiza kai tace "Allah ya shiryeki.." Baniynah tace "ameen" tana ɗaukan hijab tasa tace "bari naje na karɓo mana breakfast a gida" Khalidah tace "yawwa kiyi sauri don Allah,kinga dai fita za muyi yanzun nan" Baniynah tace "toh!" Bakin gado Muniba ta zauna ta fara shafa mai a lallausan farin fatar jikinta,tana gamawa Baniynah data fita karɓo musu abinci a gida ta shigo tana cewa "Sweet albishirinki" Muniba ta ɗago almond eyes ɗinta tana kallonta tace "goro fari tatas" Baniynah tace "Abba ya zo yanzun nan" Muniba na gyaɗa kai tai murmushi,Khalidah tace "sa kayanki muje mu gaisa,ina jin gurin ɗurin aure za su tafi suka biyo ta nan" Muniba ta gyaɗa kanta ta tashi da sauri,tsadadden lace silver grey color da suka fitar za su sa lokacin ɗaurin aure ta saka riga da skirt da suka karɓi jikinta,Baniynah ta ajiye warmer ɗin hannunta da sauri tace "taɓɓɓ ɗin nima bari nasa nawa muje" Khalidah tace "ba kun gaisa ba kike zumuɗin sake fita? Idan dukanmu muka fita kayanmu kuma fa?" Baniynah tace "ai na san baza ku dawo yanzu ba idan kuka fita" Khalidah ta maka mata wani kallo tace "shekara za muyi a can" Baniynah ta fara dariya,Muniba na gama shiryawa,Khalidah tace "Sweetheart ki ɗauko cards ɗin nan mu tafi da su kawai su bar hannunmu" Muniba tace "taɓɓɓ ɗin banda kin tuna min,ni har na manta da su" ta tafi ta buɗe wardrobe ɗin Umma ta ɗauko ledar katinan suka fita. Suna sauka downstairs suka tarar da Umma a parlour ta haɗa shayi,ga slice bread a gabanta tana ɗebarwa su Bilal,tana ganinsu ta tsaya kamar wanda akai pausing,a gurguje Khalidah suka gaisheta sukai waje,Umma na kallon Muniba data sauko a ƙarshe tace "har kun gama karin ne naga za ku fita?" Muniba tace "a'a yanzu zamu dawo,za muje dai gida ne mu kaiwa Mama saƙonta" Umma tace "aiho! Sai kun dawo to,a gaida Hjy Batoolu da Dr,na san ta shigo yanzu" Muniba tace "za su ji" tana shirin fita parlour Safwa ta fito kitchen tana cewa "ina zuwa Babe?" Muniba tace "Abba ne yazo,za muje mu gaisa kafin su fita,sai saƙon Mama da zan kai mata" Safwa tace "ok! Bari nayi wanka kafin ku dawo" Muniba tace "ok! Hurry up,yanzu za mu dawo" tana fita ta samu Khalidah tsaye ta kama waistband ɗinta,Muniba ta fara dariya tace "Yaa Khalidah please ba sai kin ce komai ba" Khalidah tace "wuce muje,idan kika bani haushi da wannan attitude ɗin naki,zan iya fusata na kai maki mangari" Muniba ta shagwaɓe fuska tace "i'm so sorry big Sis" Khalidah bata san lokacin da ta saki murmushi ba,tana girgiza kanta tace "let's go.." A ƙofar gida suka ga motocin Abba,Police ɗinsa da sojojin da basu san daga ina ba sun bazu a layi har da wasu ƙarin private security da akai hiring,dai² za su shiga cikin gida Abba suka fito shi da ƙaninsa da suke tafe suna magana,sai Yaa Khalifa da Yaa Mubasshir da suke biye da su sun ci manyan kaya brown colour ɗin tsadadden shadda,Abba kuma yadin Vicuna ne jikinsu fari tas,wanda kuɗinsa per yard ya kai aƙalla 1.3M,Muniba ta ƙarasa kusa da Abbanta dake mata murmushi yace "Autana!" Muniba ta shige jikinsa kamar ƴar yarinya tace "good morning Abba" Abba yace "morning! How are u?" Tace "i'm good" tana kallon Baffanta da suke gaisawa da su Khalidah,tace "Abba good morning" Dr Sulaiman Mijinyawa yace "morning Mamana,kun tashi lafiya,ya hidima?" Tace "lafiya lau alhmdllh" tana kallon Yayyunsu biyu maza tace "Yaa Mubasshir ina kwana?" Yace "lafiya lau Muniba,ya taro?" Tace "alhmdllh.. Yaa khalifa ina kwana?" Ya amsa yana kallon yanda ta maƙale jikin Abba kamar mage yace "cat iyayen son jiki" ta turo baki tace "Abba ka ganshi ko?" Abba yace "Khalifa ka shiga hankalinka fa da taɓa mana uwa" Dr Sulaiman yace "kai haka ake yi ne wai? A gabanmu ma sai ka mata tsiya babu kunya? Ka sani fa Mamarmu ce" Khalifa ya tura hularsa baya yana murmushi yace "Abba amma mu ai kakarmu ce" Dr Sulaiman yace "toh! Kuma idan akaga muna nan ai sai a dunga ɗaga ƙafa koh?" Khalifa yace "toh Abba an ɗaga" ya faɗa yana ɗaga ƙafarsa ɗaya,duka akai dariya har shi,Safwa ce ta fito cikin lace grey color da ya ɗan ciza ba kamar nasu Muniba ba,ta gaida su Abba suka amsa mata da kulawa har suna tambayar Baba tace "yana gida yanzu zai fito" tana kallon Muniba tace "yaushe za mu tafi?" Muniba tace "yanzun nan.. Yaa Khalidah mu shiga mu fito kou?" Khalidah tace "ehh muje" sukai sallama da su Abba,cikin gida dake cike da hayaniya da baƙi suka shiga,basu jima sosai² ba suna gaisawa da ƴan uwa,Muniba ta wuce upstairs ta kaiwa Mama cards,kafin ta sauko ta karɓo key ɗin motar Mami wacce suke tare da ƙanwarta Aunty Wahidah,tana saukowa suka fice gidan,sanda suka koma gidansu Safwa sukai breakfast,guraren 9am sannan suka bar GRA suka tafi gurin make-up,da yake Khalidah kawai za'a yiwa su biyu sunce baza suyi na ɗaurin aure ba sai an jima idan za'a tafi dinner,ana gamawa Khalidah Safwa tace ayi mata light,Baniynah ta buɗe baki zatai magana,Muniba ta hanata ta hanyar rufe mata baki da hannunta,ta dunga kallon Muniba dake girgiza mata kai kawai tayi shiru,ana gama mata suka fito suka wuce gida Muniba na driving. Ƙarfe 11am dai² aka ɗaura auren Khalidah Sulaiman Mijinyawa da angonta Dr. Muhammad Muhammad Kankarofi akan sadaki 500K,ɗaurin auren da ya samu halartar da yawa daga gwamnonin arewa,manyan ƴan siyasa da masu kuɗin dake cikin Kano da kewayenta,sojoji a gurin da suke tsaron tun daga bakin titi har cikin masallaci za ka ɗauka yaƙi ake shirin tafiya,haka sauran ɗamara ma babu kalar da babu a gurin nan saboda ɗaurin auren ya tara manyan mutane,daga masjid Umar bin Kattab ana gama ɗaurin aure ango ya kira amaryarsa dake tsakiyar ƙannenta yai mata albishir,kana jin muryarsa ka san yana cikin farin ciki,daga nan kuma duka Bristol palace hotel ƴan ɗaurin aure suka wuce akai reception,sai guraren 1pm sannan su Abba suka taho gida tare da makusantansu,sai ango da nasa tawagar shima da zai je gaisar da iyayen matarshi,convoy da akai zai baka mamaki kayi zaton gwamna aka rako,sanda suka iso shi da kansa ya kira matarshi suka fita,nan aka fara hotuna tun daga waje,Safwa da su Muniba duk suna wajen ana ta ɗaukar hoto da angwaye,yayyu maza da iyaye,zuwa abokan karatu. Safwa an samu abunda ake so,gaba ɗaya ji take babu kamarta a gurin,duk hoton da za'ayi indai na gungu ne ko za'ayi da su Muniba sai ta shiga,haka yanda take commanding photographers ɗin suna mata hoto da friends ɗinta da samarinta,za ka rantse da Allah itama jinin gidan Mijinyawa ce. Wazeer dake tsaye can nesa duk yana kallon abunda ke faruwa,ba kowa yake kallo ba illa Muniba dake liƙewa Abbanta,kana kallonsu ka san duk inda ya fito mahaifinta ne saboda tsananin kamar da take da shi,number Safwa da sai daren jiya yai saving ya shiga kira,so yake ya bar gurin da wuri,banda ya mata alƙawari ma da tun daga gurin ɗaurin auren ya ɓace,tana ɗauka tace "hello! Friend ban ganka ba fa.. Zan yi fushi da kai" Wazeer dake can nesa gaban masallacin dake line gidan yace "ni ai na ganki" tace "kana ina tou?" Yace "gani kusa da masjid" tace "wane masjid ɗin? Inda akai nikah?" Yace "um'um! Na line gidanku" waro idanunta tayi da mamaki,ita dai ta san duk hirar da suka yi bata sanar masa inda gidansu yake ba,ya akayi to ya sani? Sai kuma ta kallo gurin da yace mata tuna ai yana group ɗin *Yaran Tumbin Giwa*,ya ɗaga mata hannu daga inda yake,Safwa tai wani ƴar ƙara tace "awwnnn! I'm coming.." Daga haka ta kamo hannun Muniba tana cewa "Babe dan Allah zo ki rakani can mu gaisa" Muniba da duk take jinta a takure saboda kallon da wani abokin Muhammad da suka zo tare yake mata duk inda tayi,bata da wani zaɓi bayan na bin Safwa,da sauri tace "ok!" Suna barin gurin Muniba ta sauke wawan ajiyar zuciya tace "wash! Allah na gode maka,na kuɓuta daga kallon da mutumin can yake min,sai kace zai cinyeni da ido.." Safwa tace "waye ne?" Muniba tace "wancan abokin Yaa Mohan ɗin mana.." Safwa ta fara dariya tace "haba ƙawata,kika sani ko yana ciki ne?" Muniba ta zaro ido waje tace "taɓɓɓ ɗin ni ina zan iya da wannan mutumin me jarabar kallo.. Allah ya kiyaye" Safwa tace "ban gane Allah ya kiyaye ba? Wai me kike nufi ne? Ni fa ina kula dake sam ba kya kula samari,bama kya basu fuskar da za suzo miki da wani magana" Muniba tace "ke rabani da maza,ni yanzu karatu nake,ban isa fara tsaiwa da samari ba" Safwa tai dariya dai² lokacin suka kawo inda Wazeer yake,Muniba ta fara cewa "assalamu alaika" da sumammu kuma gajiyayyun idanunsa ya bita da wani irin kallon da tunda yake a rayuwarsa bai taɓa yiwa wata ƴa mace kwatankwacinsa ba,within few seconds ya gama karanceta tas,ya kuma ganeta itace dai wacce ranar a plaza tai masa sallama,yauma dai da mask ɗin a fuskarsa,har suka gaisa da Muniba,yai mata Allah ya sanya alkhairi tai masa godiya fuskarta cike da murmushin da ya gama narka jini da ɓargonsa,Safwa dai na tsaye tana masa kallon ƙurilla,duk da rabin fuskarsa a rufe yake amma sanda zuciyarta ya shiga bugawa past²,can ƙasan ranta ta furta "subhanallah! Allah ya yi halitta a nan gurin" ko sallama ta manta batai ba,Muniba ta kalli Safwa da duk ta ruɗe ta kasa magana ta taɓata,kamar wanda ta taso daga suma tai firgigit tace "sannu.. Da zuwa friend" ya lumshe kyawawan idanunsa ya buɗe akan Muniba,sai dai duk nacinka baka isa ka gane inda yake kallo ba kai tsaye,saboda yanda yayi ƙasa² da lashes ɗinsa ya sake shanye idanunsa,calmly ya furta "how are u? Ya taro?" Ya subhanallah,hausarsa kawai da kunnuwan Safwa suke sauraro sai da ya kusan sawa ta ƙarasa sumewa a tsaye...

           #Toh! Shi kuma wannan sarkin kallon na ina ne? Wannan shi ake kira an gudu ba'a tsira ba,Muniba na gudun kallo ta sake haɗuwa da wani sarkin kallon.. Ko me zai faru tsakaninsu 4 nan kuma? Amma nace ba gaskiya Wazeer ya shammaceni da ya zo bikin nan,saura ya kunyatani ana gayyatarsa dinner yace zai je kuma..😪


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Where stories live. Discover now