*SAFWA*

      Kwana biyu kenan kusan kullum sai ta duba Damfo a WhatsApp,amma har sannan taga babu alamar ya ga message ɗinta,dole tasa ta yanke hukuncin kiransa,sai dai wayar nasa bai tafiya saboda tsohon number ɗinsa Baniynah ta turo mata,da yake da shi yake chat,a yanzu kam cike take da ɗokin ta san nawa ne kuɗin ɗinkinta ta biya ta huta,sauran kuma tayi uzurin gabanta tunda ta samu enough kuɗi. Kasancewar yau Monday tana school,kuma su Muniba ma ta san suna school ɗin,shi ya hana ta kiran Baniynah,amma duk dare yau idan ta koma gida za taje gidansu Muniba suyi maganar,duka kwanaki biyu na weekends basu haɗu ba,saboda bata dawo gida ba,ta shiga ranar Saturday gurinta,a tunaninta data ce mata za ta dawo ranar ta dawo ɗin,sai ta iske Khalidah kawai a gida,ita ta sanar mata Baniynah bata dawo ba tana can gidansu Muniba,shi yasa yau ta yanke hukuncin za taje gidansu. Daga school ko data gama lectures,sai data koma gida tai wanka ta shirya sannan ta sanar da Umma za taje gidan Commissioner,Umma tace "toh! Akan maganar ɗinkin naku ko?" Safwa tace "ehh! Amma ina ga za muje siyan takalmi da jaka daga can" Umma tace "toh! Shi kenan,nima kya duba min plat ɗan dai² haka,ki siyo min da ƴar jaka da zan yi fitar biki" Safwa dake kallon Umma tace "kai Umma gaskiya ki bari na gama nawa siyayyar,Allah yasa ma kuɗin su isheni nima,kike ba ni sautunki" Umma tace "toh shi kenan.. Ki sissiyo dai komai irin nasu,ko color ban yarda ku bambanta ba idan da hali" Safwa tace "ai dama nima bazan yarda suce ayi haka ba" Umma tace "sai kun dawo,maza ki tafi kada ku ɓata lokaci" Safwa tace "sai na dawo" Umma tace "Allah ya tsare" Safwa ta amsa da ameen. Daga gidansu babu nisa zuwa Commissioner road inda gidansu Muniba take,kasancewar duka cikin GRA ɗaya suke,amma duk da haka bata iya tafiya da ƙafa ba,sai data samu tricycle ta hau,tafiyar 5 minutes ya kawosu line,ta sauka tare da sallamar me napep sannan ta isa get ɗin gidan,ɗaya cikin police get keeper da suke zaune yana kallonta yace "Hjy! Gurin wa kika zo?" Safwa tai masa wani kallon ƙasƙanci tace "so kake kace baka gane ni ba?" Yace "sure" tace "toh gurin masu gidan nazo,daga gidan Eng. Ridwan nake" gyaɗa kansa Police ɗin yayi yace "ok! Ki jira a nan,sai an bada izinin ki shiga" Safwa ta kalleshi daga sama har ƙasa tace "ni ce zan jira a nan? Kamar yau na fara zuwa?" Yace "sure" Safwa ta dunga kallonsa ta kasa cewa komai,lokaci ɗaya ta ciro wayarta ta fara kiran Muniba,ring biyu wayar yayi ta ɗauka,Safwa da ranta ya gama ɓaci tace "hello!" Muniba tace "hey! Ya kike? Ya su Umma?" Safwa tace "ga ni get ɗinku get keeper ya hana ni shigowa" Muniba tace "a'ahh akan me zai hanaki shigowa? Bashi wayar" Safwa ta miƙa masa wayar tana aika masa kallon banza,ya karɓa yana kallonta ya kai wayar kunnensa,Muniba tace "hello! Ka barta ta shigo,she's my friend" yace "ok Hjy" daga haka ya miƙawa Safwa wayarta yace "za ki iya shiga" Safwa taja siririn tsaki ta wuce ta barshi a gurin,tana shiga compound sai ga Muniba ta fito,hango Safwa na shigowa yasa ta tsaya balcony har ta iso gurin,Muniba tace "sorry Babe! Basu taɓa ganin kin shigo a ƙafa bane,shi yasa suka tsayar dake" Safwa da ranta ke ɓace ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta gyaɗa kanta tace "maybe" Muniba tace "zo mu shiga.. Sannu da zuwa" Safwa tabi Muniba a baya zuwa ciki tana cewa "Mami fa?" Muniba tace "Mami bata dawo ba tana BUK,sai mu kawai a gidan" Safwa ta gyaɗa kanta,a parlour suka tarar da Baniynah kwance,ta ɗago ta kalli Safwa tai mata ɗan taƙaitaccen murmushi tace "hey Babe" Safwa tai mata murmushi also tace "how far? Ya skul?" Baniynah tace "fine.. Ya Umma da su Bilal?" Safwa tace "suna lafiya" ruwa da drink Muniba data tafi kitchen ta kawo mata,tana ɗan murmushi tace "sai kika ga mutuniyar shiru bata dawo ba" Safwa tace "wallahi shi yasa ai kika ganni na zo.. Dama akan maganar ɗinki ne da zuwanmu super market nazo naji ya ake ciki,na yiwa Damfo magana na ga he didn't respond" Baniynah tace "halan kin samu masu kauri?" Safwa tai wani murmushi tare da fari da idonta tace "ke dai ki bari kawai,na taka babban dami" Baniynah tace "Allah ƙawata?" Safwa tace "wallahi" Baniynah ta tashi zaune tace "anya bazan shiga jakarki ba kuwa Hjy ta?" Safwa tai dariya tace "shigo mana,ai baki da matsala" Baniynah tace "yeah! I see" Muniba dai na jinsu tana murmusawa,Safwa tace "yaushe za muje super market ɗin yanzu? Ya kamata asa date" Muniba tace "sai dai mu bari weekends,shi ne ranar da Mami take nan,and muma babu abunda muke yi" Safwa tace "alright! Allah ya kaimu" suka amsa da ameen,har Mami ta dawo daga aiki ta sameta,ba ita ta bar gidan ba sai dare,Mami tasa driver ya kaita gida.

WAZEER!Where stories live. Discover now